MAHWISH PART 2 PAGE PAGE 13

50 5 0
                                        

*MAHWISH PART 2*


WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Sa'eed na can na sallah, Sumayyah ta fito daga toilet bayan ta gama kukan ta ta wanke ido ta goge fuskar ta da qaramin farin towel din da ke cikin toilet d'in, ta na sa kai parlour'n ta ji ana buga qofar sashen nata, Mahwish ta fita dan ganin ko wa ne ne,mamakin ganin mutanen ne ya kama Mahwish, kallon agogon da ke tsintsiyar hannun ta ta yi ta ga qarfe 11:27am, cike da mamaki ta musu sannu da zuwa, tare da yi musu izinin shiga parlour'n.

Ihsan na ganin su ta miqe tsaye tare da dafe qirjin ta, nan da nan idanun ta suka cika da kwalla, jiki ba kwari ta durqusa ta gaishe su, amsawa suka yi kamar ba abinda ya faru, Hajiya mama kuwa a ran ta fadi take,

'Ahaf, ai na san za ku zo da qafafun ku bada hakuri, ai ni Adama ban haifi wulaqantacciya ba, sai dai yara na su aje namiji su ce ba sa so amma ba dai...'

A d'an firgice  Hajiya Mama ta ce,

"Iyyee na'am? Ki ka ce?"

Mahwish ce ta ce wa Hajiya Mama"Cewa na yi ana ta gaishe ki"

Juya wa ta yi wajen baqin ta na washe baki tare da gyara zama ta ce,

"Ku yi hakuri, ban ji ba, ina can na lula wata duniyar, kun zo lafiya? Ya mutanen gidan? To madallah, ya shirye shirye? Ai muna nan ana ta faman shirye shirye komai ya kusan kammaluwa,"

Murmushi wata dattijuwa ta yi sannan ta ce,

"Da farko dai ni suna na Hajiya Baito, ni ce Goggon Munkaila, na zo tare da Innar shi ga ta can qanwar mahaifiyar shi, da kuma qanne na biyu, wannan kuma na san kun san su, qannen shi ne mata biyu, Hajiya shirun ku ya nuna mana cewa tabbas abinda 'yar ki ta je ta yi a gidan d'an uwa na da sa hannun ki, da yawun ki, tunda ba wani babba da ya je ya bada hakuri, ko aka tattauna akan maganar, dan haka maganar aure ta tashi, mun zo mu tafi da lefe da kudin aure da muka kawo, Allah ya sa hakan shi ne ya fi alkhairi, domin kuwa tun a ranar Uwar yaro ta so mu zo mu karbi kaya, ni na hana, na ce ta yuwu abinda yarinyar can ta je ta yi baki sani ba, a jira, amma in ba ku yi ko da waya bane kun yi bayani, to zamu yo tattaki, to gamu mun zo, dan Allah ina so a yi abu cikin ilimi da fahimta ba tare da an rugurguza zumuncin da aka so hada wa ba"

Wani irin kuka Ihsan ta rusa, sannan ta fita waje da gudu, 'yan uwan Munkaila kuwa binta kawai suka yi da kallo, su na jiran a fito masu da kaya su yi gaba sun aro mota na can a waje za a kwashe kayan, daga nan gidan gidan yar uwar shi da mahaifiyar shi ta so ya aura tun fari suka nufa. Hajiya Baito ce ta dauke idanun ta daga kallon inda Ihsan ta bi a guje, ta numfasa ta ce,

"To Allah ya kyauta, dan Allah a hanzarta a miqo mana kayan mu na da wajen zuwa"

Cike da fushi da jin haushin su Zaituna ta fita, ta nufi sashen hajiya mama, jan akwatunan guda biyu ta yi ta dire a gaban su, cikin fushi ta ce,

"Gashi nan marasa imani da tausayi kawai, ku dibi halin da yarinyar nan take ciki amma ku ke maganar kayan ku, to wadannan wahalallun kayan? Wace sutura ce Ihsan bata saka ba? Ko tsinannun mayunkan naku? Ko shegen turaren ku me arha? A tashi a tashi a yi waje, shan sanyin ACn ya isa haka, ku yi waje na ce, "

Murmushi dattijuwa Baito ta yi, sannan ta ce,

" Tabbas na gani Habi, maganar ku gaskiya ne,mun so mu dauko wa kanmu wahala, gidan da babu tarbiyya ai ba gidan aure bane,"

Sa'eed ne ya fito yana tasbihi, ya kalli matan da ke tsaye suna shirin fita da akwatuna, ya dakatar da su, cike da mamaki ya ce,

" Me yake faruwa anan ne? "

A hasale Zaituna ta ce,

" Ka ga rabu da su, su tafi, talakawan banza, shi matsiyaci ko a tandun mai ka tsoma shi in ya fito qamas za ka gan shi, ba za mu hada zuri'a da wadannan mutanen ba ku je Allah ya hada kowa da rabon shi"

MAHWISHWhere stories live. Discover now