Mahwish na tsaka da shan wahala Sa'eed ya dawo, ganin halin da take ciki ne ya yi matuqar karya zuciyar shi, ya rasa me zai yi, kawai sai ya rungume ta ya hau kuka, mijin d'aya daga cikin maqotan su ne ya dawo, da sauri matar shi ta fita ta kira shi, ya na zuwa ya ga halin da Mahwish take ciki, sai jikin shi ya yi sanyi.
Sai qoqarin kwacewa take daga hannun Sa'eed, ta na sake cizgar gashin kan ta, jini na ta zuba, addu'a suka had'u su na mata gaba d'ayan su.
Cikin ikon Allah kuwa nan da nan ta fara samun sauqi, bacci mai dad'i ya dauke ta.
Godiya Sa'eed ya dinga musu, su ka nuna ai ba komai, yi wa kai ne, bayan sun tafi ne, ta na baccin ya samu ruwa da towel ya gyara mata jikin ta, jinin ma ya rage zuba, ya na goge wa ya na kuka, dan kuwa duk ta ji wa kan ta ciwo, ta sa farce duk ta yagi jikin ta, kamar wadda ta yi fad'a da wata dabbar mai farce.
Wannan wace iriyar masifa ce kuma ta riske su?
Washegari da safe da zazzaɓi mai zafi ta tashi, kan ta na yi mata matuqar ciwo, ya so su je asibiti, amma ta nace akan ba komai, ya tafi kawai wajen kasuwancin shi, ya na da ganawa da wasu baqin mutanen Ciro, akan kasuwancin shi, ji yake kamar ba zai je ba, zai iya rasa miliyoyin kud'i amma ba zai iya rasa ta ba, gani yake da ya fita, za ta sake shiga halin da ta shiga jiyan, da kyar Mahwish ta samu ta bashi baki ya tafi.
Ya na tafiya kuwa ta rufe gidan, amma bata sa key ba, Sa'eed ya ce kar ta kulle duka, ta na dawo wa ta kwanta dan yin bacci, a gajiye take jin kan ta, kamar ta yi wani aiki mai yawa,ta na d'ora kan ta a pillow ciwon ya taso mata.
Wata iriyar jijjiga ta fara yi, ta na kama kujerar da take kai, saboda gani take gidan na juya mata, sai ta ga kamar za ta fad'i qasa, ko ina na jikin ta rawa yake, saboda tsamin da ya yi a jiya, ga wata sabuwar wahalar na cin ta.
Kuka take so ta yi, ta kasa, dan wani abun ya fi gaban kuka, Mahwish qoqari ta fara yi, dan ta tashi, ta nemi taimako, amma inaaa bata samu wannan damar ba, haka ta dinga cizgar gashin kan ta, ta na faduwa qasa kamar wadda ake buga wa da qasa.
Wani irin qarfi ta ke ji na shigar ta, da gudu ta nufi qofar d'akin, kamar wadda aka sanya, haka ta sa hannu ta dauke ta, ta wurgar a gefe, ta fita parlour, ba abinda take illa sake fama tsohon ciwon da ta yi wa kan ta jiyan, duk ta sake karce jikin ta.
Abun fa ya yi tsanani, ya wuce tunanin mai tunani, ta na cikin wannan halin shan wahalar ne, maqociyar ta ta sallama, ta shiga, dauke da abincin karya wa, shi ya sa Sa'eed ya ce kar ta rufe qofa, ko da wani abu zai faru, za a zo a taimaka mata, ai kuwa ta na shiga ta ga halin da Mahwish ke ciki, hannu na rawa ta ajiye abincin, ta fita d gudu, ta kira maqociyar su, nan fa suka taru, su na ta mata addu'a, mijin d'ayar ne ya kira Sa'eed a waya, ya sanar da shi halin da Mahwish ke ciki, a gaggauce ya sallami mutanen da suke tare, ya musu bayanin matar shi ba lafiya, sun tausaya masa matuqa, dan su suna girmama matan su, su na basu babban matsayi a rayuwar su matuqa, Sa'eed bai damu da mutanen da ke bin shi da kallo ba, ya na keta gudu kamar wanda aka biyo, haka ya fita, ya samu mota, sai gida.
Kafin ya je Mahwish ta yi laushi matuqa, gaba d'aya jikin ta ya yi jawur, saboda ciwukan da ta ji wa kan ta.
Daukan ta ya yi a hannu, ya ce musu zai kai ta asibiti, da sauri maqocin nasu ya riqe shi ya ce,
"Amma dai asibitin mahaukata ya kamata ka kai ta, mu je zan raka ka, na san waje, dan in na bar ka wahala za ka sha, ka shiga ka dauko mata takaddun ta, na shaidar zama anan,ina naka suke?"
Nuna masa aljihun shi ya yi, alamar su na ciki, ba ya so ya ce komai, zuciyar shi ta yi rauni sosai da sosai,
Sa'eed da fari, sai ya ji kamar an fad'a masa baqar magana,da aka ce ya kai ta asibitin mahaukata, Mahwish d'in tashi za a kai asibitin mahaukatan? Tunani ya yi da kyau kafin ya dauko mata takardar ta, ya tabbata can d'in ne mafita,ya na zuwa gaban ta ya duqa ya dauke ta suka isa mota, shiru ya yi, kafin daga baya ya ce,
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........