MAHWISH PAGE 1

141 8 0
                                    


*Assalamu alaikum mutanen kwarai mutanen arziki masu albarka, ina maku barka da Sallah, tare da jimanta mana tafiyar watan Ramadan mai albarka, ina roqon Allah da ya sa mu na daga cikin bayin shi da ya enta a cikin watan Ramadan*

*Masoya karanta novels d'ina da duk wani rubutu nawa ga sabo na kawo maku mai suna MAHWISH wato KYAKKYAWA KAMAR WATA, ina roqon ku kamar kullum ku dinga tara wa saboda in na yi gaba.....🤭😂*

*Labarin MAHWISH labari ne wanda tushen shi wato jigon shi zan gina shi a bisa labarai na gaskiya, wanda suka faru, na mutane mabanbanta,wanda na ke fatan na rubuta shi a matsayin labarin mutum d'aya*

*Masoya novels d'ina ina fatan za ku min uzuri, domin ba za ku dinga samun post kullum ba, amma inshaa Allahu duk sanda na samu dama zan yi maku posting, ina godiya sosai a bisa soyayyar ku ta tsakani da Allah, Allah ya bar mu tare da imani, ina son ku domin Allah, Allah ya so mu ya lullube mu da rahamar shi*

Page 1:

Kunnuwan ta toshe suke da earpiece ta na sauraran shahararren gidan redion nan da ke cikin garin Kano wato Freedom redio, inda aka saka waqar da ta sanya zuciyar ta narkewa tare da tsananin shiga shauki irin na cikakkun masoyan da duk wani motsi ke tuna masu da masoyan su.

A hankali ta bud'e idon ta, domin jikin ta na bata ana kallon ta, ido biyu suka yi da qaramar qanwar ta da ke bi mata wato Zulaihat, dariya sosai Zulaihat ta kece da ita, sannan ta ce,

"Yah Mahwish ki na matuqar bani dariya, yanzu da ki ka kwanta shame-shame ki na kallon sama ido rufe me ki ke tuna wa? Ko ki na hango ki ne tare da Ali Nuhu ku na waqa ne kema?"

Wata sabuwar dariyar Zulaihat ta sanya, sannan ta samu gefen kujerar da wadda aka kira da Mahwish ta zauna, tare da zuba mata idanun ta da ke dauke da tsantsar dariyar tsokana.

Cikin yauqin ta da juya kyakkyawan jikin ta, ta yunqura ta zauna ta na kallon Zulaihat,cikin muryar ta mai cike da amo mai sanya natsuwa da kwanciyar hankali ta ce,

"Hummm Zulaihat kenan, ke fa har yanzu yarinya ce, baki san mene ne so ba,da ace kin san mene ne so, da kin fahimci  halin da duk wani masoyi ke shiga in ya ji kida na tashi, ko da ba waqa to kai za ka sama masa waqar da kan ka, kuma...."

"Zulaihat ! Zulaiii !"

Kiran da mahaifiyar su Mahwish ke kwala wa Xulaihah ne ya sanya ta miqewa cikin sauri, da tura baki, ta  ce,

"Ke fa Hajiya ke kira, Abba ma na jiran ki tun dazu"

"Amma ai ba ki fad'an ba Zulaiiii zama ki ka yi ki na ta surutu,"

Cikin bata fuska ta kalli Mahwish, dan ta fi kowa sanin ba ta son a kira ta da Zulaii, amma ta ke tsokanar ta,fita daga d'akin na su ta yi ta nufi babban parlourn su, wanda ya ke kewaye da manyan kujeru, waje ne mai matuqar kyau kwarai, kuma madaidaici, zama ta yi a gefen qafar Hajiya ta ce,

"Gata nan zuwa, Hajiya dan Allah ki daina kira na da Zulai, ita Yah Mahwish kun sa mata suna mai dad'i ni kun sa min Xulaihah kuma ban tsira ba sai an sake b'ata min a dinga kira na da Zulaii?"

Dariya Mahaifin su Alhaji Farouq Bukar Mai Taya ya yi, sannan ya ce,

"Gaskiya bai kamata ba kam, Hajiyan su ya kamata ki dena b'ata wa autar ki suna"

Wani kallo mai cike da so da qauna, tare da harara irin ta masoya Hajiya ta wurga wa Alhaji Farouq, sannan ta ce,

"Amma dai alhakin saka sunan zulai ya rataya a wuyan ka ne, ni da aka bar ni na sanya sunan Mahwish ba gashi na saka mai dad'i ba,"

"To ya ishe ku, sunan Yaya ta ne dai, takwara na mata,a bar tsokanar Yayata , a dinga cika mata sunan ta daga yau"

"Amma dai Abba Yah Mahwish ce babba me ya sa ba ka saka mata Xulaihah ba sai ni?" In ji Xulaihah da ta bata rai, dan ita sam sam sunan bai mata ba.

MAHWISHOù les histoires vivent. Découvrez maintenant