"Kamar yanda ku ka sani suna na Sumayyah, iyaye na 'yan asalin Danbatta ne, an haife ni da sauran' yan uwa na duk a Danbatta, yanayin aikin mahaifi na ne ya sa muka koma Maiduguri da zama, a unguwar Gwanje, layin Dan Bauchi.Hajiya na san kin ji labari na wajen qawar ki, dan ita ma daya ce daga cikin irin mutanen da na takura wa na addaba lokacin ina qarama, zuwan mu Maidugiri be sauya ni da komai ba, se ma qara ta'azzara rashin ji na da ya yi, sakamakon haduwa da yara kama ta, Ummana bata taba cewa Allah wadai da hali na ba, a kullum fatan ta Allah ya shirya ni, ta sani watarana zan bar qiriniya ne, ta dauki duk abubuwan da nake a matsayin yarinta, yaro sai da kazar kazar.
"Watarana wani baffana yazo hutu, qani yake ga mahaifin mu, sai ya tarar ina nan da hali na na jan fada da tsokana, dama tun a Danbatta shi kadai ke iya duka na ya zauna lafiya, ya shigo ya ji Umma na na min fada akan wani rashin ji da na yi a makaranta, kawai Baffa ya zabura zai daken da tabarya, Umma na zaune ta na tankade, ta na ci gaba da min fada, yanda ya taso da qaramar tabarya zai daken nima haka na tashi na yi wajen Umma na a guje ina ihu, ita kuma ta na daga kai ta gan shi da tabarya a hannu ya yo kai na, ganin shi da tabaryar nan ya sa ta yunqura zata tashi dan kar ya illa ta ni, miqewar nan da za ta yi, ji ka ke kauuu ya buge mata kai da tabarya garin tuwo ya zube a qasa, nai tsalle na haure garin da Umman da Baffan nai waje abu na da gudu, kadan kenan daga cikin artabun da iyaye na suka sha akai na"
Ana cikin wannan yanayin aka yi wa yayu na mata biyu aure, na sha kuka sosai saboda bana so gidan mu ya ragu, na fi son shi a cike, ta yanda zan tsokali wannan na koma kan waccan, bayan haka ma, mun saba, ina son su, suna so na, duk kalar ta'adi da qiriniya da zan musu ba sa damuwa, su na shagwaba ni sosai, su na ririta ni, kamar ni ce auta, nan kuwa ina da qanne biyu mace da namiji.
A kwana a tashi na kai shekaru goma sha d'aya, ina zuwa makarantar boko da ta allo, aji na shida a primary, a allo kuwa na yi kusan izu tara, daga baya sai Baban mu ya maida ni Islamiyya da ke gaba kadan da layin mu.
Tun a wannan qananun shekarun na fara samun samari, kamar wata babbar mace, yara su zo, manya su zo, ba wadda suke so sai Sumayyah, Baba kuma ya na so na sauke alqur'ani ko da ban gama boko ba, dan a cewar shi boko ba a gama ta, amma karatun addini in yaro bai da shi, yayi aure, to wani yana dawwama ba ilimin addini, sai a samar da uwa mara ilimin addini a al'umma.
Saurayi na na farko wani babarbaren matashi ne, wanda ke zuwa unguwar mu sana'a, watarana na fito daga islamiyya, zani gida, ya ganni ya tsaida ni, suna na kawai ya tambaya da unguwar mu da layin mu, daga nan bai sake ce min komai ba, da dare sai gashi ya zo waje na, Umman mu har ta ce ba zan je ba, ta koma daki, na lallaba na dauki takalmi na da hijabi na da nai sallah da shi, nai wuf na fice, zuciya ta cike da murna, ko ba komai yanayin yanda qawaye na ke zuwa zance abun na ban sha'awa, duk da cewa su sun girme ni, sun isa zance, ni kuma na qagu in ga nima an fara bari na tsawa da wani, an dade ana zuwa waje na, amma su Baba na hana wa, da sunan ban girma ba, yanzu kuwa tunda na fara al'ada wata biyu da suka wuce, girji na ya fara tasa wa, Ummaa ta kan ce, na girma, dan haka ba me hana ni zuwa zance na.
Ina fita na hadu da wannan bawan Allah da ya tsaida ni a hanya da rana, ba tare da na gaishe shi ba na ce masa.
'Bawan Allah zance ka zo?'
Cikin mamaki ya kallen ya ce,
'Eh, na zo ne dan mu san juna, tun dazu da ido na ya sauka a kwayar idon ki na ji soyayyar ki ta kama zuciya ta, shine na zo in sanar da ke, ina son ki, ina fatan kema ki na so na?'
Wata iri yar dariyar murna na yi, na yi juyi, sannan na ce masa,
'Nima ina son ka,to yanzu mu yi xancen'
"Kan shi ya daure, shi be san me nake nufi ba, saboda ga dai zancen muna yi, ni kuma na amsa masa ina son shi ne kawai, ba dan na san ma mene ne so din ba, sannan a zato na shi zancen da ake ta yayata ana yi tsakanin saurayi da budurwa wani wasa ne, na yi shiri tsaf a kafta wasan, dan haka na sake ja baya, na gyara zaman hijabi na, na kalli kwan fitilar da ke haske mana fuska na bude baki zan magana, na ji an ja ni cikin gida an durma min dundu, ba kowa bane face Umma na, qara na saki, na ruga cikin gida a guje ina kuka, Ummaa na ta jima a waje kafin ta shigo, ba ta jima da shiga ba Baba ya dawo daga masallaci, nan ta labarta masa qudirin zuwan wannan bawan Allahn, Baba ya ce,"
![](https://img.wattpad.com/cover/292798077-288-k314670.jpg)
ŞİMDİ OKUDUĞUN
MAHWISH
RomantizmQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........