MAHWISH PAGE 12

48 2 0
                                    


Ta na tuqa tuwo, ta na tunanin abubuwan da za ta sanar da sabon bokan da ta samo, lallai dole ne Mahwish ta gane kuren ta, akan dukkan abubuwan da ta aikata.

Ta dauki lokaci mai tsaho kafin ta gama raba abinci ta yi wanka, dakin yaran gidan mata ta leqa ,ta kira d'aya daga cikin yaran ta, ta aike ta siyo Tiara za ta had'a wa Baban su.

Ta na bata kud'in ta koma ta d'ebi garwashi ta saka turaren wuta a d'akin ta da ya sha gyara, ta saka kayan bacci masu kyau,ta ɗora zani akai, ta na ta ci gaba da kai kawon ta, duk abin nan da take fuskar ta ba walwala sam sam.

A tunani na zan ga wani had'add'e kuma d'an gaye a matsayin mijin Zaituna, kawai na ga wani mutum kamar wanda aka tono daga rami, kayan shi duk datti, qafar shi ma haka, sai wari yake kamar ya yi sati be wanka ba.

Ya na sallama matan shi suka fito su na gaishe shi, gani ya yi bai ga uwar gidan shi ba ya ce,

"Ke Haule ina Balkisa? Ko jikin ne dai?"

"Malam yau ai Yaya wunin daki ta yi, jikin ya matsa, ko ruwa bata samu ta sha ba"

"Subhanallahi, bari na duba ta, amma ku na nan ku kasa bata abinci ta ci?"

"Malam an bata, ba dai ta iya ci ne,"

"Ashha, bari na duba jikin nata"

Cire takalmin shi mai datti ya yi a bakin qofar shiga d'akin uwar gidan nashi, ya yi sallama ya shiga, yaran ta manya guda hud'u su na jikin gadon da take, su na hidima da ita, su na ganin mahaifin su suka fita, zama ya yi, a gefen gadon ya na duba jikin matar tashi.

Can waje kuma Zaituna tun da taga an shiga da manyan ledojin kayan miya ta san mijin su ya dawo? To gidan uban wa ya tsaya? Yau dai girkin ta ne ba na kowa ba.

Yara ta miqawa ledar kayan miyan su ware masu kyau, da wanda ba su da kyau, ta koma ciki ta zauna ta na cika ta na batsewa.

Ya kai kusan minti goma kafin ya fita daga d'akin uwar gidan nashi ya wuce bayi, dan wannan na d'aya daga aikin Zaituna kai masa ruwan wanka da kayan da zai sauya, a cewar ta ba zai je ya gama kokawa da kwandunan kayan miya ba ya dawo ya shigar mata daki da datti.

Ya na gama wanka ya sauya kayan shi, ya miqa wa wani yaron shi kayan da ya cire, ya ce ya wanke, ko da ya shiga d'akin Zaituna ta cika ta yi fammmm.

Sallama ya yi, ba ta ko amsa ba ta fara sauke masa kwandon masifa,

"Daga ina ka ke? Ko dake ba sai ka bani amsa ba, Nuhu ka tsaya ka bud'e kunnen ka da kyau ka saurare ni, ka san sarai banda qaddarar haihuwa ba abinda zai sa ni auren ka ko? Ka sani sarai ni ba sa'ar auren ka bace ko? Ranar girkin su ko kallo baka ishen ba, dan me to ran girki na sai ka bi d'akin su ba za ka zo waje na ba direct? Kowacce munafuka da ta ji ka dawo ta hau fitowa,wai su masu miji"

Cike da ladabi kamar wani d'anta, yake bata hakuri,

"Kin ga da ke Balkisa ba lafiya, shi ne na leqa ta an ce yau ko ruwa bata sha ba"

"Munafurci ne, da safe ba na gan ta ba, ta na ba wa Isifu kudin siyan koko? Uban wa ya sha mata kokon? "

"Auuu haka neee? Kaiii mata sai a bar ku, had'a baki kenan suka yi har yaran suka ce bata sha ko da ruwa ba, ai kuwa za su ga iya shege gobe ko leqa ta ba zan ba, zan wuce kasuwa"

"Ahhh toh, mata sun maida ka wani sususu baka gane komai"

"A yi hakuri sarauniyar mata, a bani abinci na ci,"

Zanin ta ta kunce ta ajiye, ya bi ta da kallo a tare su ka sa dariya,abinci ta ajiye masa, ya ci ya qoshi.

Da safe ya shirya zai fita, ta bi ta maqale shi, ko kunyar idon yara bata ji, ta na ta zuba masa soyayya, d'aya daga cikin yaran uwar gidan shi ta zo a guje ta na kuka, ta ce,

MAHWISHHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin