MAHWISH PART 2 PAGE PAGE 17

29 4 4
                                    


'Kullum in ki ka aike ni wajen shi a kasuwa, ko ya dawo baki nan, ko ki na dakin ki, se ya dinga tambaya ta, wai in baya nan waye yake zuwa gidan nan ki na kwana da shi? Sai na ce masa ba kowa, se ya ce qarya nake in fada masa gaskiya akwai wanda yake zuwa da daddare ki na kwana da shi? Umma na me yake nufi ni ban gane ba'

"Wani irin baqin ciki na ji ya tokare min wuya, ashe Grema zargi na yake shi yasa nake jin tafiya cikin dare kamar an hauro, shi ke zuwa kenan ya ga ko na kawo wani gidan, ban san ido na ya cika da kwalla ba sai da na ji Modu ya taba ni ya na sake tambaya ta me hakan ke nufi"

'Kar ka wani damu kan ka, Modu na, wasa yake m....'

"Kafin in qarasa yaron ya katse ni a tsorace, ya na zaro ido ya ce,"

'Ah ah Umma na! Ba wasa yake min ba, ya ce ze kashe ni da wuqa in ban fad'a masa gaskiya ba, in ki ka aike ni wajen shi har duka na yake kuma ya ce kar in fad'a maki, kar in yi kuka, in ba haka ba se ya qara min'

" Anan fa zuciya ta ta hasala, na kai makura wajen bacin rai da ace Grema zai shiga gidan a wannan lokacin da ko ni ko shi, zuciyar fulanin asali ta motsa min a wannan lokacin, in zargi na yake me yasa yake ci gaba da zama da ni? Ya bar wa yan iskan ni mana, bari ya xo gidan, kamar ya san me ya aikata be zo ba a ranar, sai washegari, da yamma, ashe wai tafiya ya yi ta kasuwancin shanun shi, domin kuwa shima cikin ikon Allah tunda mukai aure kiwon shi ya yalwatu, kullum kuma kudi shigo masa suke, duk abinda ya taba na Sana'a ko kiwo sai Allah ya sanya wa abun albarka,banbancin su da Bukar shi ya na bani na kashewa, baya baqin ciki dan ya ban,"

" Ko da ya zo na so na tambaye shi, sai na yi shiru kar ya je ya daki yaro a banza, dan na kula ba shi da imani ko tausayi akan Modu, ni kuma yaron nan shi nake gani in ji dad'i tunda ban da na kai na, sannan ya na taimaka min ya na deben kewa, in Grema baya nan kuwa ya na ragen jin tsoro a gidan, ni banga abinda yaron nan ya tare wa Grema ba, yaro mai kazar kazar me hankali irin Modu"

'Tunanin me ki ke ne ko baki so na dawo bane?'

'Ina zan so ka dawo tunda zaka hana kwarata na masu hauro min katanga da dare su na leqe na zuwa,'

"Ina fadar haka sai ya yi shiru be ce komai ba, ya tabbatar na gano shi ke zuwa cikin dare ya na leqe na,dan haka sai na ce"

'In ba kwaratan yanzu da rashin rabo ba, ace ga mace dandatsetsiya kamata me makon su tada ni a yi abinda za ai, se su tsaya labe, da hange daga nesa'

"Buta ya dauka ya zaga, daga ranar be sake zuwa da daddare ba, sai ya sauya, ya fara zuwa min a duk lokacin da ya ga dama, kawai sai ya fado, da alama so yake in ina kawo wani gidan ya kama mu,"

"Wata rana na dawo daga unguwa kenan, se na zauna a bakin qofa, ban jima da zama ba sai gashi ya shiga, kawai sai ya hau ni da masifa,"

'Wannan wanne irin iskanci ne zaki zo ki zauna a bakin qofa duk wanda ya wuce ya na hango ki?'

'Iskanci ne irin na matan gida da ya fi na matan waje, haba Grema, wai meke damun ka ne kwana biyu? Yanzun nan fa na zauna, na manta ban saka dangur ba (dutse) shine xaka zo kana min fada har kana kira min iskanci?'

'An kira maki iskancin, ke daga yau in na sake zuwa na ga qofar gidan nan bude Allah ya isa ban yafe maki ba'

"Raina ya yi bala'in baci, akan rufe qofa zai ja min Allah ya isa?"

'Akan rufe qofa zaka ja min Allah ya isa? Wai kai wanne irin jahili ne? Ka fa fara kai ni maqura Grema, me yake damun ka ne, ka san ma' anar Allah ya isa ma kuwa? Idan kuma ta bi ni na samu wata matsalar a rayuwa fa? Daga yau sai yau kar ka kuskura ka sake ja min Allah ya isa, idan kai jahili ne baka san ma'anar ta ba ni na sani mtss'

"Ranar ya sha mamaki, na fita masa a giya sosai, na masa masifa son rai na, dan haka ya na kammala abinda zai ya ce,"

'Jahili zai fita'

MAHWISHDove le storie prendono vita. Scoprilo ora