Sallama ake ta doka wa, Hajiya Mama na zaune ta na sid'e hannu, daga Ihsan har Tasneem ba mai hankalin amsawa, cikin b'acin rai Hajiya Mama ta ce,"Kaiiii wannan ba dan da alheri ya nufe mu ba,da na lailaya masa ashar na wurga masa tukuicin cika min kunne da ya yi, shin ku gumakan banza ba wadda ta iya amsa sallama balle ta duba ta ga d'an anacen da ke mana sallama kamar ya bada ajiyar uwarshi an qi maida masa ita?"
Da sauri Ihsan ta leqa tare da amsa sallamar a daqile, dan koma waye ya na neman kawo masu tsaiko akan abinda za su je yi, su na had'a ido da masu sallamar ta yo baya a guje ta na kuka, tare da fad'in,
"Ni ba zan koma ba, Allah ba zan je ko ina ba, gwanda ma ku tafi"
"Ke! ke da wa? Ni dai na san kaf kafatanin dangin mu ba mu da aljana 'yar tsamiya, balle in ce biyo ki ta yi har gida ta maida ke cikin d'angin su na aljanu, ke da wa?"
"Hajiya Mama ba wannan baban su Bilal d'in bane, ya wani kama ya zo da mutanen unguwar mu,har da malam liman"
"Tooo abun kuma aikin gayya ya zama? Mu je na ji ta ya liman d'in zai sa rawanin shi ya lauye ki ya mayar wa busasshen"
Miqe wa ta yi ta muttsuke hannun ta, ta goga kamar me shafar mai, sannan ta gyara daurin zani da d'an kwalin ta ta leqa, gaishe gaishe suka yi a tsakanin su, a yanda ta fita fuska ba walwala ba fara'a sai ta samu kan ta da sake fuska, saboda girman mutanen wajen.
Mai unguwa, da liman, sai mahaifin mijin Ihsan d'in da aminin sa, sai shi mijin Ihsan d'in da ya rakub'e daga gefe, ya na leqen cikin gidan na su Ihsan din ko zai gan ta.
Liman da mai unguwa sun jima su na Fafatawa da Hajiya Mama, sam ta qi amincewa da komawar Ihsan gidan Baban su Bilal, har sai in ya amince zai fasa qara aure.
Ana haka Sa'eed ya dawo, bayan gaishe-gaishe, aka sake kora masa bayanin abinda ke faruwa, sai ya kada baki ya ce,
"Mu dai 'yar uwar mu ba zata zauna da kishiya ba,"
Hajiya Mama ta washe baki ta kad'a kai kamar a qasar kudu, sannan ta ce,
"Uhumm, dan ku ji ku sani, 'yata ta fi qarfin zama da kishiya"
Sa'eed da ya ga ya samu Hajiya Mama na bin bayan maganar shi sai ya ce,
"Amma in ya dage sai ya qara aure, sai dai fa a raba gida, kowa da gidan ta, kuma dole ne mu ma a yi wa qanwar mu kayan fad'ar kishiya, dan wata ba za ta zo ta fi ta d'aura sabon zani ba, kuma dole ne a bata kud'in ɗinkin, kuma dole ne yaran ta biyu a musu sabbin kaya dan su ma su san uban su zai qara aure"
Hajiya Mama kan ta ya kulle, amma dai duk ta amince indai har 'yar ta za ta koma sai an cika wad'annan sharudd'an, da ido Sa'eed ya ke nuna musu su amince, nan da nan kuwa mijin Ihsan ya ce ya amince duk zai yi hakan,
"To abu na gaba a yau muke so da ta koma ka damqa mata kudin dinkunan tun kan a sai kayan, dan mu tabbatar da gaske ka ke"
"Na amince"
"Hajiya Mama magana ta kuwa ta yi miki?"
Cike da dariyar jin dadin hukuncin da Sa'eed ya yanke ta ce,
"Kwarai kuwa, kai dai Allah ya maka albarka, a cika sharad'i ta koma, a karya sharad'i d'aya ta dawo gida"
"Bama wannan maganar Hajiya Mama, yanzu ina ganin a shiga a taho wa da yaro matar shi su wuce gida, duk abinda aka shard'anta ni mai unguwa zan sa ido na tabbatar komai ya tabbata"
Hajiya Mama ba b'ata lokaci ta shiga dan fito da Ihsan, ta na shiga Sa'eed ya ce Mijin Ihsan ya bashi acc No d'in shi, nan da nan kuwa ya bashi, ya tura masa kudin da zai wa Ihsan duk hidimar da ya lissafa, sannan ya kafa mahaifin shi da sauran mutanen shaida, in ya kuskura ya wa qanwar shi ba daidai ba, da kan shi zai dauki mataki.
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........