MAHWISH PAGE 3

76 6 0
                                    


Hira suke ta yi da Salim a parlour sun ci abinci sun bar wajen kaca kaca su na ta shan hira, Xulaihah na ta dariyar jokes din da yake basu, wayar Mahwish da ke caji ce ta hau ruri, cikin zargi Salim ya ke bin ta da kallo, ita kuwa fuska a daure ta miqe, dan ta san ba zai wuce mayen nata ba.

Ta na duba wa kuwa ta ga shi ne, bata fuska ta sake yi, sannan ta latse kiran ta yi zaman ta, da ido Salim ke nuna mata alamar ta dau wayar kar ta damu.

Xulaihah kuwa na gefe bata san me suke yi ba, d'aga kafad'a Mahwish ta yi, alamar kiran ya riga ya katse, Xulaihah ce ta ce,

"A gaskiya ban taba zaton Yah Mahwish za ki yi sanyi da wuri haka ba, kin yi bala'in burge ni matuqa, kuma in Allah ya yarda za ki ga da kyau a rayuwar ki, kai kuma Yah Salim Allah ya baka mace ta gari,wadda ta fi Yah Mahwish"

Yaqe suke ta yi daga Salim din har Mahwish, a tare suka amsa mata da

"Ameen"

Qasan zuciyar Mahwish kamar garwashin wuta haka take jin ran ta, Wannan wace irin rayuwa ce, ka na soyayya ba ka da hali da ikon nuna wa? Saeed kuwa ba zai ga da kyau ba Indai ya dage sai auren nan ya tabbata, yanda zuciyar ta take a quntace sai ta shi tafi ta ta quntata.

Mintina uku tsakanin kiran da akai na farko, wani kiran ya sake shiga, sai da ta jima ta na ringing sannan ta amsa, sallamar shi kawai ta amsa, ta yi shiru, miqewa ta yi ta shiga dakin su, mayafi ta yafa ta fita, tsaye ta gan shi jingine da motar shi, tabbas Saeed ya had'u, matuqar had'uwa, amma ita ganin shi take kamar wata halitta daban mai tsananin muni.

Tsaye ta yi a gefen shi ta juyar da kan ta gefe, sannan ta tura d'anlwalin ta gaba, gashin ta da ta dunqule waje d'aya ya zauna dass a dogon wuyan ta, hannayen ta duka biyu zube a qugun ta.

Murmushi ya yi, dan kuwa shi duk yanda za ta yi kyau take qara yi masa, kallon farin wata ya yi, ya ga yanda yake haska kyakkyawar fuskar ta, sakamakon d'auke wutar lantarki da akai, bude baki ya yi ya ce,

"Mahwish ba gaisuwa?"

"Ba a min wanan tarbiyyar ba, sai ka jira sai na koyo sai in maka"

"Allah ya baki hakuri amarya ta, ki na lafiya?"

"Asibiti ka gani akai na da ka ke tambayar lafiya ta? Wai ni Saeed dan Allah me ya sa ba ka da zuciya ne? Anya kuwa akwai zuciya a cikin wanan qirjin naka? Saeed ina mai baka shawara ka gaggauta janye wannan auren tun kafin a daura shi, ina tausaya wa rayuwar ka in ka dage sai ka aure ni, domin kuwa zaka daura aure ne da tashin hankali, da masifa da bala'i, wataqila ma da ajalin ka"

"Subhanallahi, dan Allah Mahwish ki dena irin wannan kalaman, domin basu dace da 'yar mutunci kamar ki ba, wadda ta fito daga gidan mutunci gidan manya, dan Allah Mahwish ki kalle ni, kuma ki saurare ni, ki sani duk abinda Allah ya hukunta zai faru sai ya faru, ba mu da tsumi ba mu da dabara, in Allah ya nufa ba zan aure ki ba sai ki ga Kafin auren wani abu ya gilma ban aure ki ba, amma....."

"Allah ya sa mutuwar ka ko mutuwa ta ce za ta gilma a tsakanin wannan qaddararren aure da ake so a qulla a tsakanin mu, Saeed na maka kuka, na maka magiya, na maka bori, na maka wa'azi, ba abinda ban maka ba, dan ka gane yanda na ke qin ka, na ke tsanar ka a rai na, amma ka rufe idon ka,ka toshe zuciyar ka, da kunnuwan ka, to kuwa ba za ka ga da kyau ba Saeed duk randa ka yi gangacin aure na, banza mara zuciya, wanda kare maqasqanci ya cinye wa zuciya, mtswww"

Qoqarin barin wajen take yi Salim ya fita, fuskar nan kamar hadari, ta na ganin shi kuwa ta nufe shi ba tare da bata lokaci ba ta fad'a jikin shi, ta fashe da kuka, kyakkyawar runguma ya mata a jikin shi, cike da tsananin begen ta ya ke shafa bayan ta da sigar lallashi, wani irin abu ne mai duhu ya lullube idanun Saeed, kunnuwan shi suka dauki wata qara, baya ji sosai, jiri na diban shi ya dafa motar shi, hasbunallahu wa ni'imal wakeel kawai yake maimaita wa, matar da zai aura nan da sati ce a jikin wani qaton a gaban shi ya na shafa ta, qirjin ta a na wani gardin, jikin ta na manne da na wani qaton, tunda ya ke da ita ko yatsan ta bai tab'a tab'awa ba, amma Salim ke riqe da ita a haka.

MAHWISHWhere stories live. Discover now