*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story* ❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰🥰*
Page 25
Sallama sukayi ta ajiye waya tana dogon nazari🤔............
*Yazatayi da Uncle G idan yazo KADUNA yasamu Zulaihat takoma Zeey💞Abdool?*🤔............
Shuru tayi tana tunani yadda Uncle G zaiji idan hakan ya bayyana,wayanta nee yadauki k'ara........
Dubawa tayi taga Zeey💞Abdool ce,Dan haka Zulaihat tamata Saving a wayanta....
"Assalamualaikum Aunty Rahela?"
"Wa'alaikumuslam Zeey💞Abdool"
"Ya kk,ya Ayyan?"
"Lfy Lau"
"Gobe zamuzo gidanki nida Aunty Farida"
"Dan Allah😳😁,kwana zakuyi?"
"Eh kwana biyu ma😁"
"Alhamdulillah,Allah ya kaimu"
"Ameen ameen"
Bayan sun Gama wayane taketa tunani,gaskiya in aka Hana Uncle G Zulaihat ba'amai adalci ba.....
Dan tun Zulaihat na karama yake Nuna Mata kulawa,kowama yasani Dan kullun a gidan mu yake wuni Dan gidansu Yana kallon gidan mu, Uncle G yanada kirki Dan duk abunda Zulaihat takeso Yana Mata,bama ita kadai ba dukkan mu,Dan yasha biya Mana Skull fees dukkan mu,Anya munma kanmu a dalci kuwa?🤔🙄....
Gashi Ahaji Baba bazema Zulaihat auren Dole ba,Dan yafi son mu Akan y'ay'anshi, Innalillahi wa'ina ilaihirraji'un,nashiga Uku Ni Rahela ya zanyi🙆🏻♀️🙆🏻♀️?kumafa nice Babba........
Nusawa tasakeyi cikin wani tunanin Koh zatasamu mafita🤔.....
Magana tafarayi a hankali ita kadai a d'aki......
"Uncle G baida wani makusa,yaya Imran maiyasa kadakatar dashi?,dayanzu Zulaihat batasan wani Abdool ba sai Uncle G, Uncle G yanada kirki sosai bawanda za'ama rashin mutunci bane,Dan shinema yafara siyan ma Zulaihat waya Kuma ya roki Mummy tabari tafara rike waya tun tana SS 1.........
Anya Amma Uncle G adalci kuwa? No no gaskiya.......
Koda Ayyan yadawo wanka tamai yayi bacci itama bacci dai daukanta yayi Dan tunani takeyi iri iri Dan Abban Ayyan baya gari......
*Washegari*
Dassafe Zeey💞Abdool da Aunty Farida suka shirya sai tafiya gida Aunty Rahela,Dan sunbar Hannafiya da cefanan komai......
Tare sukafita da Kaka,Dan Kaka zata koma Kano Saida suka sata a mota suda Mummy,sai Mummy ta juyo gida ita da Auta sai Su suka Kama hanya zuwa gidan Aunty Rahela.........
Suna Isa suka hau Hira kafin Aunty Rahela ta zubo musu Abinci,Dan Aunty Rahela akwai iya tarban Bako Dan zakaci abinci iri iri da abunsha Dan tasan sirrin tarban Bako, Dan itama tana Shirin tarban Abdool Dan har gidan Aunty Nafeesa ma za'a kaishi balle ma su Aunty Babba😁......
Bayan sungama cin abincinne Zulaihat tafara ma Aunty Rahela bayanin yadda sukayi da Uncle G.......
"Ni yanzu narasa yadda zanyi Aunty Rahela🤦🏻♀️?"
"Dole munemi mafita,Dan Kinga Kar Uncle G yazo Abdool nanan,Kuma bazamu iya Hana Uncle G zuwa gidanan ba?"
"Gaskiya,Dan wani lokacinma a gidan muma yake sauka"
"Toh fah😨?wai ya kuke da wannan Uncle G din haka?"
"Lah Dan uwan mune sosai,Baki sanshi ba?"
"Ta Ina zata sanshi Zeey💞Abdool?itafa dagin Mummy ce shikuma dangin Daddy ne,bazaki ce tsanshi ba,Kuma again Bata taba zuwa KADUNA ba sai wannan Karan"
"Eh Kuma hakane"
"Bari kiji Aunty Farida.........
Uncle G yaron Cousin din Daddy dinmu ne,da mahaifin Daddy da Mahaifin Alhaji Baba uwa Daya uba Daya suke,ai Kinga Alhaji Baba Koh?"
"Eh naganshi, bashine Wanda gidanshi ke kallon gidanku na hayi ba?"
"Yauwa yar gari shine,Toh Alhaji Baba shine baba a Family dinmu gaba Daya, shine first born a wurin babansu,babansu yarasu yabarsu su Uku,sai babansu Daddyn mu ya daukesu ya rikesu......
Daddyn mu shine babba a gidansu,dalilin hakanne suka shaku dajuna saboda zaman gida Daya dasukayi......
Tun suna kanana,daddyn mu baya iya yin Abu saiya shawarci Alhaji Baba,Hasalima shine yasashi yayi gida kusa danashi a Hayi,Dan Daddy baya kyaunar zaman Hayin Rigasa,Amma saboda Alhaji Baba ya hakura ya zauna.....
Wannan shakuwan dake tsakanin Daddy da Alhaji Baba yasa duk abunda Daddy yakeso Alhaji Baba ma yanasonshi,shine yatsaya tsayin daka yaranshi sukayi makaranta,shinema ya neman Uncle G NDA har yazama Naval Officer........
Uncle G duk Rabin rayuwar shi agidanmu yakeyinta,mun shaku dashi sosai,Dan duk Abunda mukeso yana mana bama Jin kunyar Tambayanshi saboda Shakuwan damukayi dashi,Yana da brothers dayawa Amma bama iya Tambayansu saboda bamu shaku dasu ba kamar Uncle G.......
Shakuwan da mukayi da Uncle G ne muka canza Mai suna yakoma Uncle G,da ya Garzali ake kiranshi kamar yadda Muke Kiran suran,irinsu Ya Imran, ya Musty dadai sauransu........
Amma saboda munshaku sosai Muke cemai Uncle G, Zulaihat ce Kuma tasamai Our pride Dan Uncle G akwai ilimi sosai,Dan duk Abunda sukasa a gaba shida Daddy insha'allah suna Samu.......
Kisan menene dalilin shakuwan Daddy da Uncle G?"
"A'ah Aunty Rahela saikin fada?"
"Daddy bayason Yaro Mara maida hankali a karatu Kuma bayason Yaro Mara gaskiya,Toh Uncle G yacika duk sharadin da Daddy yakeso,shiyasa Daddy yaso ya hadashi da Zulaihat dayaga yanasonta,Amma Uncle G yanuna a barsu su daidaita kansu"
"Innalillahi wa'ina ilaihirraji'un🙆🏻♀️😨😳, Uncle G yayi kuskure gaskiya"
"Sosai Amma hadda mu,Dan duk alamun da mutun yanason mutun Uncle G yanuna,furtawa nee kawai baiyiba"
Zulaihat ce tayi zuru zuru da ido😨,saboda itama tasan Bata kyautawa Uncle G ba.....
"Yanzu Aunty Rahela menene mafita🤔😨?"
"Nima dawannan abun nakwana,Dan Uncle G yakirani jiya"
"Nashiga Uku🙆🏻♀️,Ya Kamata a Hana Uncle G zuwa,Dan banason abunda zai batawa Abdool Dina Rai🥺"..........✍️✍️.
*Shin Kuna ganin Hana Uncle G zuwa shine solution?🤔🤔*
By Tooraee 🥰🥰🥰
*(GOLDEN PEN)*

YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Fiksi SejarahLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su