*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story*❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰🥰*
*Page 62*
...... Mik'a Mai tayi Babu musu,gyarasu Nana tayi,itadai sai bin Nana take da kallo na ganin ikon Allah,yadda ta jerasu sunyi kyau sosai,habawa duk y'an uwa dasuka dawo daga daurin aure kowa yazo da waya sai cire musu portrait akeyi,Auta ce tafito tareda Mai hoto tana neman Nana a musu hoto, saita samu ana musu hotuna,Nana tace "yauwa Malan Dan musu da camera kaji" Aiko batareda B'ata lokaciba yafara cire musu hotuna masu kyau,kowa sai Albarka yake sawa,Dan wasuma sun aza Mata da mijine ga d'ansu,Dan Zulaihat tayi kyau sosai wasu Basu gane taba,Nana ce ta bude jakanta tayi rubutu taba Mai hoto,sannan tace "pls idan zakayi editing nasu kasamun abunda narubuta a Jikin hotonsu" "badamuwa angama ranki shidade" Abdool ko sai murmushi yakeyi itako Zulaihat duk ta rude tashiga mamaki,tarasa meke Mata dad'i,barmai Young G tayi ta sulale takoma gida,neman Deeja tafarayi Dan tabata labari,Amma bataga Deeja ba,fita tazo sakeyi domin neman Deeja suka sake cin karo,ba yadda ta iya tsayawa sukayi Dan taga alamun yanason yamata magana "naga text dinki,kince kinason Zaki P/Harcourt Koh?" Kai tadaga alamar "eh" "Madallah,yanada kyau,Dan yakamata" "ok" kawai tace tafara tafiya,maryanshi taji daga sama yana cewa"idan Young G yadawo kiduba aljihun wandonshi akwai sak'o" "toh" Shima kaman Dole takama kanta, neighbor tashiga tafara Hawaye tana magana,"wai meke damuna nee?nakasa cewa mutuminnan yarabu Dani,nashiga Uku yazanyi ni Zulaihat?" Kaman daga sama taji muryan Deeja tana cewa "kinada yadda zakayi",dagudu taje ta rungume Deeja tace "gayamun Dan Allah" "sai kin daina kuka tukunna" cikin hanzari ta share hawayanta sannan tace "gayamun pls" "yauwa,kinsan me?" Kai tad'ga alamar a'a *Daman Zaki sake bashi dama ne" Ido tazaro tace "again?" "Yes" "no no no" "ok,shikenan Amma kayi tunani" sai tajata suka koma gida Dan had'a kayanta na tafiya, Deeja ce tazab'ama Young G Kaya sannan tace "kema zabi naki",haka Koh akayi suka shirya tsaf Dan Kai amarya P/Harcourt.....
Bayan angama Shan shagali kowa yagaji ana zaune da daddare ana Hira,sai Deeja ta dauko Young G zata Mai wanka,cire Mai Kaya tafarayi saitaji kaman Abu a aljihun wandonshi a dunkule,"menene Kuma wannan?" Hannu tasa Dan taga menene? Kudine tazaro a aljihunshi,da small note,budewa Deeja tayi Dan taga menene aka rubuta, rubutune kaman haka *pls manage dis* irga kudin Deeja tayi,duk abunda Deeja keyi Zulaihat na Kallonta,sai datagama kirgawa 20k nee,"kuttt Amma Abdool yayi gaganci,shine yasa kudi Mai yawa a aljihun Young G?" "No yagaya mun fa"
"Shine Baki cire ba?" "Namanta" "lallai Allah yaso rabone,Dan yadda Young G yasha daukannan yau" "Uhmmmm" "ai Daman haka kike" fira suka cigaba dayi sama sama har bacci ya kwashesu, washegari da sassafe suka Kama hanyar P/Harcourt Kai Aunty Hannafiya gidan Oga Zayyad, Alhamdulillah tafiya tayi Dadi Kuma sun Isa lfy,Amma Young G sai kuka yake Dan ya gaji,wanka akamai sai yafara bacci,call din Abdool nee yashigo wayanta Dan tun a hanya suke wayama Yanajin suna Ina, d'agawa tayi tafada Mai sun sauka lfy "Masha Allah,sannunku da kokari,Ina my boi?" "Yanzu yafara bacci" "ayyah yagaji Koh?" "Wlhy Dan saidama akamai wanka tukunna" "ayyah Allah yatasheshi lfy" "ameen mungode" murmushi yayi sannan yace "Saida safe Koh?" "Eh Allah yatashemu lfy",suna Gama waya da Abdool aka kawo musu Abinci Mai rai da lfy dan a gidansu Zayyad suka sauka,Dan za'ayi sword crossing washegari, Abinci sukaci sosai hadda amarya,Dan itama yunwa takeji sunci sunsha Dan hadda farfesun Naman rago aka kawo masu banda pepper chicken din da akayishi domin su hadashi da fried rice,ga sakwara da miyan agushi dayaji ganda da busheshshen kifi,sunfa kwashi girki Amma ko sumin Bismillah,sun barni da *GOLDEN PEN* a hannu........Washegari da sassafe Zulaihat ta hau online,tafara kallon status din mutane dan taga hotunan biki,status din Auta ta bud'e taci karo da hotonsu itada Abdool da Young G Kuma an rubuta *Zeey💞Abdool* ajiki,Bata Gama shiga mamaki ba,sai dataga wani Wanda Young G na dariya Abdool ma na dariya ita Kuma ta juya Dan taga mekesa Young G dariya haka,karaf suka hada Ido da Abdool,kafin ta janye idonta an dauki shot din,wannan hoton yayi mugun kyau sosai,haka kawai taji hoton Ya burgeta,haka ta dinga bude status din family and friends wannan hoton nee a status din kowa,ga kuma rubutun *Zeey💞Abdool* ajiki,shuru tayi tana mamaki,"ba shashka wannan aikin Abdool nee" fita tayi daga WhatsApp tashiga I.G,Dan ta kalli pictures da video din biki a page din Oga Zayyad,Tayi typing din Z kenan sai taga *Zeey💞Abdool* a jerin pages din Z din datayi typing,habawa budewa tayi Dan taga suwaye wannan,ga mamakinta sai taga hotunantane Wanda aka daukesu ita da Abdool a skull babu iyaka,Dan duk batasan ana daukan wa innan hotunan ba,Bata Gama shiga mamaki ba sai dataga Viewer's over thousand's of people,ga followers bazama ta iya fada ba,shuru tayi batace komaiba,hoton tasake budewa tabbas sai taga sunyi kyau sosai,saving tayi a gallery dinta sannan tace "Deeja?" "Na'am" "kin taba ganin wani page a I.G Mai irin wannan sunan" wayanta ta nuna Mata "Oh *Zeey💞Abdool* ?" "Eh" "nagani Mana har Ina following dinku" "following dinmu fa?" "Ehen,Baku kuka bude ba?" "wlhy bansan dashi ba,nazo zanshiga page din Oga Zayyad nee sai nagani" "oh,Aiko na aza kina san dashi,Dan hotunankune ai keda Abdool,wasu Kuma da Young G Koh?" "Eh duk bansan sanda aka daukesu ba,gakuma wannan hoton bikin ansa *Zeey💞Abdool* a Jiki" karba Deeja tayi dagudu kaman bataga hoton ba "lah,wow Kinga yadda kukayi kyau kowa?" "ai nagani a pages din mutane a I. G" "Koh Aunty Hannafiya?" "Eh Mana,koh Aunty Rahela ma tasa a page dinta" "toh fah?" Nan Zulaihat tasake lulawa I.G Dan taga abun mamaki,aikoh kowa yasa a page dinshi duk Wanda tasani yasa,har y'an skull dinsu datake binsu a I.G,shuru tayi tana nazarin,daga baya Kuma sai tayi murmushi tafurta wani kalma a hankali kaman bazatayi ba "Thank you ol" ga mamakinta taji Deeja tace "no karkidamu,basai kinyi godiya ba" harara ta zabgama Deeja sannan tace "ke wanne irin kunne gareki haka?ban San gulma" "kamarya? Godiya fa kikamana" dariya Aunty Rahela tayi Dan tagano Zulaihat tanason Abdool Amma batason nunawa duniya.....
*Shin gaskiya nee sis Maryam?*
B'angaran Abdool kuwa kwance yake ya tsurawa hoton Ido,ga yawan viewer's dasuke dashi akan hoton,nishadi yashiga Dan bak'aramin farinciki yakejiba , Deeja ce ta tura Mai da sako kaman haka *zuwa anjima Zan tura maka hotunan swords crossing* reply yamata *Ok besty,godiya nake* haka Koh akayi,bayan angama swords crossing,sunsha kyau gashi sunsha hotuna masu zafi,Dan sun bugu sosai da sosai, Deeja ce taturamai sannan tace *kasa a page dinnan pls* batare da Bata lokaciba ya Dora Akan page din, Shima yaga like dayawa,ga comments sosai da sosai, Zulaihat ma tayi liking Dan hotunan sunyi kyau sosai Dan tarigada ta sare da lamarin Abdool......
Kwanan su Zulaihat biyar a P/Harcourt suka dawo,sunbar Aunty Hannafiya acan,ayyah rayuwa kenan Aunty Hannafiya an zama matan aure, Zulaihat bataga komaiba Saida takoma skull,kowa yakoma kiranta da *Zeey💞Abdool* sakamakon wannan picture din,gashi Babu halin tace batason sunan,Dan duk y'an class dinsu sunsanta Abdool Dan duk Friday's tare suke wuni,Daman sunada tambaya a baknsu saiga wannan picture din ya Basu amsa,watace ce tace "Mom Young G,ai wannan mutumin da ke zuwa wurinki duk Friday's ai Daddyn Young G nee Koh?" Shuru tayi batace komaiba,Dan wannan tambayar Batada amsarshi,k'awar waccance tace "kema da neman magana kike,bikaga page dinsu bane a I.G?" "Nagani fawo,shiyasa nake magana" "ai basai kin bakanki wahala ba,dinga binsu kawai zakisha kallo,yauwa Mom Young G,Daman sunan Daddy Young G Abdool?" "Uhmmmm" abunda ta iya cewa kenan,ta tashi tace musu "zanje masallaci" "ok sai kindawo".....
Zulaihat fa tana ganin Abu wasa wasa yazama gaske,Dan yazu takoma *Zeey💞Abdool* a skull,ga Abdool ya dage sai musu new post yake,duk Friday in yazo,tun Bata yarda ayi da kyau hartakoma biye Mai suna kashe zafafan hotuna,har yanzu yakai stage din anko suke duk Friday's Dan yin new post......✍🏼✍🏼.
*Toh fah Fans,wannan page din nakune❤️❤️*
By Tooraee 🥰🥰🥰.
*(GOLDEN PEN)*
