*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story* ❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰🥰*
Page 46
Tana shiga taga an rufe Uncle G tundaga Kai har Toe dinshi,wanni irin Kara tasaki a take awurin tafadi tasuma........
Ihunta nee dasukaji yasa suka shigo da gudu a lokacinne Uncle G kuma kafanshi yafara motsi,Dr. Nee yashigo da wani Abu a hannunshi,ganinsu yayi a cike a dakin,shine yake tambayansu lfy,shine sukece Wannan ce tayi k'ara shine muka shigo,idon Dr. Dinne yakai Kan Uncle G da k'afanshi yake motsi.....
"Alhamdulillah yafarka,Daman wannan abun naje na dauko in buga a saitin kunnanshi Koh zai farka,shiyasa ma na lullubeshi Kar yayin bugawa ya farka yaganni a saman kanshi ya razana" "Masha Allah,Bari mufita da Wannan to" "ok Amma ku yayyafamata ruwa" "eh yanzu ma" fita da Zulaihat sukayi suka yayyafa Mata ruwa,tana farkawa tafara kuka tana magana.....
"Dan Allah karku cemun Uncle G yamutu" "Bai mutuba,sakamakon Karan da kikayi ma yasa yafarka" "Dan Allah,Yana Ina" "Yana Ciki Dr. Na duba shi" likitocine suka taru akanshi don dubashi sosai,komai normal yake Amma Bai bude Ido ba sai Hawaye,wanni Dr.ne yace "a barshi ya huta zai bude Ido da kanshi" "ok Sir" fita sukayi sukace mutun Daya kawai a keso yashiga wurinshi saboda ba'ason yafarka Babu wani awurin, Zulaihat ce tayi zubur tace "Zan zauna" "ok Zaki iya?" "Eh" "bazaki Kara Suma ba?" "Eh Dr." "Ok jeki to" shiga tayi ta zauna Akan robber chair ta tsura Mai Ido sai hawaye yakeyi,itama shuru tayi tashiga duniyar tunani......
Mummy ce Labarin motsawa Uncle G yasameta,tafi kowa Jin Dadi sosai Dan addu'a ta kenan Allah yasa yafarka, Zulaihat kuwa Taki motsawa awurin Gashi Uncle G yakai 2hrs yaki bude ido,kafanshi yafara motsawa sai Zulaihat tace "lah Uncle G katashi?" Maganar tane yadaki kunnanshi,A hankali yafara bude Ido Amma yakasa saboda idon sun Mai nauyi,sake damke idon yayi, Zulaihat nagani tace.....
"Uncle G Dan Allah katashi,karka mutu kabarni, Dan Allah na rokeka"
Idon yafara budewa Dan Yana son yaga wake magana,bude idon dazaiyi sai suka hada Ido biyu da Zulaihat na gefan gadon ta Duk'a tana Hawaye,tsuramata Ido yayi Yana mamaki me kesata kuka Kuma? Tashi tayi dagudu tafita taje takira Dr. Suka shigo a tare,dubashi sukayi sosai sukaga Babu komai saidai damuwa,Shikenan sai hankalinsu ya kwanta sukace Kar a dameshi da surutu.....Tunda Uncle G yafarka baiyi magana ba,sai kallon kowa yake Dan Daya bayan daya ake shiga wurinshi,Koda Mummy tazo idonshi nakanta murmushi kawai yamata sannan tafita suka wuce gida,Koda daddare baiyi magana ba sai murmushi,ya Musty nee yazo da wanzami da Alh. Baba da daddare akamai aski bawanda yasani saboda duk yayi Muni.......
Washegari Zulaihat a Asibiti ta wuni,Dan Babu skull tun safe tana tare dashi,babu abunda yake Mata sai murmushi, wuni tayi a Asibiti har yanma sannan Mummy tazo da Aunty Hannafiya suka wuce,Dan tare suka zauna dashi da Aunty Rahela da Amina,bayan kowa ya wuce saishi da Ya imran da daddare,yake cemai....
"Ya imran?"
"Na'am Uncle G,sannu Koh?"
"Yauwa"
"Akwai inda yake maka ciwone?"
"No nawarke,an birne My Dr. Koh?"
Shuru ya imran yayi Bai bashi amsa ba "Ina son zanje P/Harcourt banson a Uku banje na musu Gaisuwa ba" "wanne Uku Kuma Uncle G,ai Dr. Jibi zatayi arba'in" "arba'in fah?" "Eh Dan Kai kafi wata a Asibiti...." Nan take yakwashe Labarin abunda yafaru bayan yasuma da yadda yafarka da Zuwansu Alh. Baba da su Mummy Gaisuwa P/Harcourt.....
Shuru yayi yafara hawaye, "haba Uncle G wannan hawayan bafa shine mafitaba, addu'a shine kaji" "hakane insha'allah,Ina wayana?" "Gashi can" mikamai yayi ya amsa ya dannan number maman Dr.,bugu Daya ta dauka.....Mamaki yakamata dataji muryan Uncle G,"Alhamdulillah yarona ya farka,kayi hakuri kaji Koh,Allah Yana tare damai hakuri" "Nagode Mummy,Allah yajikan Dr. Zulaihat" "ameen ameen" "Insha'allah zanzo ayi addu'a 40 days Dani" "no kabari saika warke kaji,karka damu kayita Mata addu'a" "insha'allah Mummy Nagode" yana Gama wayan ya tsurawa screen din wayanshi Ido Dan hoton tane akai,Dan ita tasama da hannunta,Dan baze manata draman dasukayi ba a lokacin.....
*"Sweet wannan da take Akan screen Dinka ai yakamata ka cireta kasa nawa Koh?" "A'ah My Dr. Bloody nace fa?" "Bloody Kuma? Bakace mun sis Dinka bace?" "Eh hakane" "toh gaskiya a cireta koma wacece,dannine ma bloody Dinka tunda nine Zan Zama matarka" "toh Duk yadda kikace ai daidaine,Zaki iya canzawa" atake a wurin ta canza tundaga lokacin hoton Zeey💞Abdool yabar Kan screen dinshi*
Kallon hoton yayi yacigaba da tunaninta,Yana tuna moments din dasuke tare,wani yayi murmushi wani kuma sai yayi Hawaye,haka Uncle G yacigaba da Zama a Asibiti na tsawon sati Daya,kullun sai Zulaihat tazo wurinshi ta dubashi,har sudanyi Hira kadan kafin tawuce, Zulaihat tarasa meyasa take damuwa da Uncle G haka,Bata iya sukuni yanzu Babu Uncle G,Amma Zuciyarta Kuma tana wurin Abdool,Dan Koh Tashiga duniyar tausayin Uncle G sai Abdool dinta yafado Mata a Rai.....
Uncle G kuwa Yana Jin dadin yadda Zulaihat take kulawa dashi,Koh ba komai shima yasan yasamu wani bagare a rayuwarta, Uncle G yasaki jikinshi sosai da ita,Dan yanzu ma gobe za'a sallamesu Kuma sunce a kula da abunda yakeso Kar a Bari yashiga damuwa, Zulaihat ce tadauki alwashin insha'allah hakan baze faruba......
Washegari aka sallami Uncle G yakoma gida,tare sukaje hayi da Zulaihat sai yamma da Abban Ayyan zai wuce shine ya taho da ita,Dan Yana Asibiti aka sallamesu,Jikin Uncle G sai K'ara sauki yake Gashi Zulaihat sai K'ara shiga rayuwar Uncle G take Don a ganinta batason yakoma gidan jiya.....
Damuwa ta ragu a zuciyar Uncle G,Amma kullun cikimyima Dr. Addu'a yake Allah yajikanta,Dan yanzu Yana samun kyakkawar KULAWA a wurin Zulaihat,Gashi shikuma yasaki jiki sosai da ita,Dan shi Daman baya ganin laifin Zulaihat Koh kadan,Dan kullun Zulaihat saita Kira Uncle G da safe sannan ta kirashi da yamma sai Kuma idan zai kwanta Dan yasha magungunan shi saita Kira,wannan abun datake Mai Yana tuna Mai da Dr. Dinshi.......✍️✍️.
*Nikuma wannan abun da takeyi Yana tunanin mun da Abba na*
By Tooraee 🥰🥰🥰
*(GOLDEN PEN)*

YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Fiksi SejarahLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su