*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story* ❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰 🥰*
*Page 71*
.........Bikifa yayi biki,Amma *Zeey💞Abdool* Basu iya rawaba,sai dai dariya Dan Abdool da Zulaihat Baki yak'i rufuwa Dan murna,Dan sunga jama'a sosai a bikinsu,kowa sai murna yake,ga young G ma yagaji shida Ayyan Dan Suma sunsha rawa,gasu Hajiya Auta da Nana,Su Aunty hannafiya da Aunty farida ba'a magana,Dan kaman ba matan aure ba,rawa sukasha sosai,ga Deejah ai Saida Dr. Sameer yace Mata tabi a hankali......
*Nikoh nace Koh Dan little babyn shi,Kinga laifinshi mie Xuuby😍?*
Hajiya Kaka ma ta taka,can na hangota Dan tare sukazo da farida daga kano, Dinner Masha Allah,Dan taro yatashi lfy,kowa yakoma gida a koshe Kuma da gajiya,Dan anci ansha Kuma an cashe........
Gidan Deejah suka yada zango,Dan Dr. Sameer nee ya dawo dasu gidanshi,part guda Dr. Sameer yabasu Kuma tare dasu ya kwana da su Malan Ahmad,kwana sukayi suna Hira......
Hakama bangaran su Zulaihat,Hira sukayi sosai Amma banda Zulaihat,Dan hankalinta na Kan waya tana posting hotunan da aka musu,Dan Auta tab'a wayan ta dinga daukansu kafin Mai hoto ya turo nashi......
Nan take duniya ta dauka,bikin *Zeey💞Abdool*,Dan kowa sai yabawa suke,da Kuma masu tambaya 'daman ba Miji da Mata bane?' 'oh bashi ya haifi Young G ba?' tambaya dai iri iri kundai son gulman social media.......
*GOMBE*
Bilkisu ce take nunawa ummansu da sister's dinta hotunan dinner,murna suke sosai da cewa "Ummmmm dama munje wlhy,but Insha'allah *Cross of the sword* dinmu muma zai hadu sosai" "insha'allah Dan Yaya Umar ai yace zai hadu sosai,Dan su Malan Ahmad sungama shirya komai kafin su tafi KD"........
Haka suka kwana da murna,Dan burin yayan nasu yacika,Dan Abdool baida wani labari sai KYAKKYAWATA,Gashi Kuma Allah ya cika Mai burinshi.....
*Wow Congratulations Oga Abdool👍🏻👍🏻👍🏻,wannan Taya murnace daga Mai GOLDEN PEN🤩*
Washegari kuwa aka tashi da shirye shiryen tafiya Gombe ,Dan da sassafe suka Kama hanya,kuma Dr. Sameer nee ya shirya motocin zuwa,abun har kunya yafara ba Abdool,Dan yarasa dame zai sakawa Dr. Sameer......
Tafiya fa Alhamdulillah,Dan sun Isa lfy,sun Young G yafi kowa gajiya,Dan a motar su Abdool ya tafi,Dan tunda Abdool yazo Yana mak'ale dashi......
Sun sauka Gombe Around 6pm, Amma fa sunga tarba sosai,Dan Abinci ma Saida suka ture,kowa Saida ya yaba da irin tarban da aka musu,Dan sunada yawa sosai Dan Saida akayi motoci biyar......
Washegari kuwa akafara Shirin zuwa *Cross of the sword*,kwalliya sosai akama Zulaihat,Dan tsaf take cikin silver material yamata kyau sosai hakama Abdool ya shirya tsaf cikin ceremonial dress na Nigerian Air Force,ya Mai kyau sosai, dan tsaf ya fito *Abdulsamad Abdulaziz* dinshi,yayi masifar kyau sosai Dan Shirin banawasa bane........
An bar gida around 2pm,Dan kowa ya shirya tsaff,bikin *Cross of the sword* yafara,Dan yayin shigowar *Zeey💞Abdool* abun ya burge Ni sosai,Dan abun sai Wanda yagani,Dan *sword crossing* din ya burge ni sosai aradu.......
*Nima sai naji ina son in Auri soja😂😅🤩😜🤪 Koh Dan Nima amun Cross of the Sword ,Lolx*
Shagali akayi sosai,Dan Deejah ma ta tashe a bunta a Gombe, hakama Aunty rahela ba'a barta abaya ba,su Auta da Nana ba'a magana......
Bangaran Sisters da brothers din Abdool kuwa ba'a magana,Dan su bilkisu dasu Fatima an samu bikin Yaya,hakama Umar da Hamza can na hangosu suna daukan hoto da big bro nasu.....
Wow Masha Allah biki yatashi lfy,bayan sundawo ne suka tattara sai gidan *Zeey💞Abdool* Amma banda Zulaihat da Deejah ........
Masha Allah kawai,Dan gidan ya hadu sosai,Dan both the two parts din suyi kokari,Dan gidan haduwanshi sai Wanda yagani,turare su Aunty rahela suka dinga bankawa gidan kaman basusan zafin turaran ba,Nan da Nan gida yadauki kamshi sosai da sosai,Dan jiran su kawai suke su iso.......
A gidansu Abdool kuwa,abbanshi ya tarasu a bangaran shi,shida Zulaihat da uwar gidanshi hauwa'u da Abdool din ya musu nasiha Akan su zauna lfy,dukda ba'a gida Daya zasu zauna ba,Amma yakamata yaji tsoran Allah ya musu adalci a tsakanin su,nasiha Mai ratsa jiki sosai ya musu,hade da nuna musu lallai su rike Allah da Manzonsa,Dan shine tudun tsira.....
Bayan sun musu sallama, Dr. Sameer,Deejah,Malan Ahmad, Tubabbe da Suleiman suka raka *Zeey💞Abdool* zuwa gidansu,bayan sun Isa Malan Ahmad yamusu nasiha sosai tare da Jan jankalinsu Akan Aure bautane,Kuma duk abunda akace bautane sai anyi hakuri sosai,ya had'a da musu Addu'an zaman lfy,sannan suka musu sallama zasu wuce.........
Abdool nee yaga Aunty farida ta Goya Young G abaya, Dan yariga da yayi bacci
"Aunty farida ina Zaki da my boy?" "Zantafi dashine sai gobe sai akawo mukushi" "lah babu damuwa da kinbarshi anan ma" "kayi hakuri Oga Abdool kabari mutafi dashi,inyaso gobe sai a kawo mukushi" "kun tabbata Aunty rahela,karku gudu mundashi fa KADUNA?" "Ah haba mun Isa,ai Ya Imran sunce sun baka, hakama mummy,kaga koh Young G yazama naka" "aikoh Nagode," "toh Saida safe" k'asa yayi dakai ya k'asa amsawa,rakasu yayi har gate,har zai kulle gate din sai ya hango Ni,wani uban harara ya watsamin,Sim sim haka nazo na wuce.........✍🏼✍🏼.*Bee🐝 and Bro Umar Kunga Oga Abdool Koh?,karo nibiyu Kenan yana harara na koh?toh ku gaya Mai nifa Yar jarida ce, Ehe,(Nidai baruwana 😅🤩😂)*
By Tooraee 🥰🥰🥰
*(GOLDEN PEN)*
YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Ficción históricaLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su