ZeeyAbdool 45

10 1 0
                                    

*Zeey💞Abdool*
         *(2021)*





*True life story*


*Love story* ❤️❤️



*By Tooraee 🥰🥰🥰*



Page 45



Zulaihat ce taketa tunanin maganan Mummy,dashi takwana dashi Kuma ta tashi,skull tashirya tatafi daganan tacewa  Mummy zataje gidan Aunty Rahela, murmushi Mummy tayi tasan mezai kaita,bayan Zulaihat tatashi daga makaranta saita biya Asibiti tacimma ana rade radin Wai Uncle G yafadi Akan aljanune za'a maidashi gida ayi na gargajiya, hankalin tane yatashi takira Mummy tagaya Mata, Mummy daga Office tazo tahana tace....

"Babu wani Aljanu insha'allah zai warke,mu Kara hakuri pls" shuru sukayi Dan sun rasa mezasuce Dan Daman su hajiyarsu nee da Yan uwanta,Alh. Baba Bai san da zancan ba,Daganan Zulaihat ta wuce gidan Aunty Rahela.....

"Aunty Rahela sai Kika ganni?" "Wlhy kuwa,batan hanya kikayi?" "No shawara nazo muyi" "uhmmm Nima ai na aza laifin Abdool nee yashafeni?" "A'ah" "toh tun Randa kuka bar gidana keda Abdool mukayi Dan Mani kin dawo?" "No bazaki Gane ba,pls kiban shawara" "Fadi matsalar ki".....

Labarin yadda sukayi da Mummy ta kwashe tagaya Mata,shuru Aunty Rahela tayi batace komaiba,sai ta kalli cikin idon Zulaihat Dan tanason karantar wani Abu before she start talking.....
"Zulaihat tashi kici Abinci,kafin kiwuce zamuyi magana" "ok to" kitchen tashiga tazubo Abinci Mai Rai dalafiya ta zauna taci ta koshi,kawai saitaji tausayin Uncle G yakamata.....

"Aunty Rahela yanzu haka Uncle G zai cigaba dazama dayunwa?" "Menene naki toh,ke da kikace bakyasonshi Kuma bazaki taba sonshi ba" "uhmmm nidai banasonshi Amma Ina tausayinshi sosai,Dan shima Yana tausayina Dan na tabbata da nice nake cikin wannan halin nasan Koh Abincin nan Dana ci bazai iyaci yadda naci ba" "ai bazaki hada ba,wannan ma kinyi kokari tunda har kin iya tunashi bayan dakika Gama cinyewa, Kuma ai Banda abunki Zulaihat ai abun a bayyane yake,shifa sonki yake kekuma tausayinshi kike Kinga d different is clear Koh Y'an Mata,da ace Abdool nee ai Koh Lipton bazaki iya shaba, Amma dayike Wanda kikafi SO ne ai Gashi kinciye plate" Aunty Rahela nagama magana tatashi tabata wuri,tadade a zaune a wurin tana mamakin Aunty Rahela saikuma tatashi tabita bedroom tace......

"Baki bani shawara ba?" "Shawara Kuma,so kike ince Miki ki SO Uncle G? Wanda Kuma a Halin yanzu zuciyar ki shi tafi tsana? No no Zulaihat kar muyi haka dake,Kita jira dai,kullun ana gafarasa Kuma kahonnan ba ganinshi za'ayi"

Abunda Aunty Rahela Tama Zulaihat Bai Mata Dadi ba,daurewa tayi tatashi tawuce gida,tana zuwa gida tafara Hawaye Auta ce tashigo tace
"kinfara nee?" "No Auta zauna kiji" Labari taba tiryan tiryan tun daga yadda sukayi da Mummy har zuwa Aunty Rahela,"toh fah kin tambayi Aunty Hannafiya?" "No ban tambayeta ba,Aunty Rahela tamun haka bare Aunty Hannafiya Mai b'aro b'aro" "ai yanzu b'aro B'aron ta nee abun so,Bari tashigo"sallamanta sukaji "yauwa gata" shigowa tayi Auta tabata Labari......

"Toh fah,nidai kunsan halina gaskiya Zan fada saidai aji haushi na" "eh fada munaji" "Zulaihat maganar gaskiya shine batun Abdool ki ajiyeshi a gefe kidauki zancan mahaifiyarki, Mummy so take ki Auri Uncle G Amma bazata iya Miki Dole ba,Dan tasan irin son dakikewa Abdool Zaki iya cewa Dole tamiki wata Rana" "toh fah yanzu ya zanyi?" "in gayamiki mezanyi in niceke?" "Eh" "Zan bi maganar mamana in Auri Uncle G,tunda Abdool shima yayi biyayyah ma iyayanshi ya Auri matarshi kema kima naki biyayyah" "yanzu mezancewa Abdool?" "Ce Mai zakiyi kema biyayyah zakiyi yanzu" "Amma na kyauta?" "Wannan nee bansani ba, Abdool Zaki tambaya amsa tunda shine malaminki,Amma in Zaki tambaye shi gawata kik'ara aciki" "fada inaji?" "Menene hukuncin mutumin dayake fifita son zuciya Akan gaskiya?" Dukkansu sun dauke wuta Dan Auta ma yanzu Zulaihat tafara Bata haushi dukda karancin shekarun ta,a wurin Aunty Hannafiya tatafi tabarsu suna nazarin tambayar ta......

Auta ce tace "Zulaihat ki Kira Aunty Farida Mana muji nata shawaran?" "Eh kumafa hakane,Bari nakirata toh" wayanta ta dauko takira Aunty Farida bugu Daya tadauka......

"Assalamualaikum Aunty Farida"
"Wa'alaikumuslam Zeey💞Abdool"
Shuru tayi nadan wani lokaci sannan ta amsa dakyar "na'am" "Amma kaman ba kalau bakoh?" "Eh gaskiya shiyasa nakiraki,shawara nake nema" Labarin abunda yafaru tabata tudaga Kan Mummy, Aunty Rahela har Aunty Hannafiya yadda sukayi,shuru Aunty Farida tayi nadan wani lokaci sannan tace....

"A gaskiyan magana Nima nasoki da Abdool,Amma ga abunda Abdool yazo yayi Dan bazan boye Miki ba Abdool Bai kyauta mun ba,Amma baka gujewa kaddaranka ko Ina yake saikaje kasameshi,saboda haka Zulaihat bazan boye Miki ba, Mummy tanason ki Auri Uncle G nee,Amma batason tamiki Dole,amatsayin ki name tunani yakamata kiduba maganan Mummy dakuma halin da Uncle G yake Ciki,Dan yanzun Uncle G Yana cikin wani Hali da yake bukatan taimako na SO da KULAWA,kuma kiduba idan kika amince da maganan Mummy bakisan wanne irin farinciki Zaki sataba,Kuma nasani bazaki taba Shan wahala a wurin Uncle G,idan ma Baki amince da maganan Mummy ba, Abdool fa ba auranki zaiyi ba yanzu,Dan karki manta babanshi yace lallai  ya maida matarshi,Amma shawara ce Nima" "toh thank you, Nagode ki gaishedasu Munubiya" "zasuji" sallama sukayi tayi shuru tana nazari.....

*Yanzu kowa amsa Daya?Bari dai inje wurin Deejah*

Hijab dinta tadauka taje wurin Deejah,Ga mamakinta saitaga Deejah tabata amsa iri Daya Dana Aunty Hannafiya,Shuru tayi kawai batace komaiba,gida tatashi tadawo,Koda dare yayi juya maganar take a Zuciyarta,takasa bacci......

*Anya na kyautawa Mummy kuwa idan ba amince da shawaranta ba?Amma yazanyi da Abdool?*

Zubur kawai tayi tatashi taje dakin Mummy,tasamu Mummy a zaune Akan sallaya tagama sallah

"Mummy kin idar?" "Na idar?" "Mummy Daman wancan shawaranne" "eh inaji? Kin Yankee hukunci kenan?" "Eh Mummy" "toh gyamun" "Mummy na yarda da shawaranki Zan Auri Uncle G" "kin tabbata?" "Eh Mummy" "toh Masha Allah kin kyauta,Allah yasa hakan shiyafi Alheri" "ameen" kawai tace tatashi takoma dakinta,sai Kuma data koma tafara ladaman meyasa ta amince,mikewa tasakeyi tayi dakin Mummy,sai Kuma ta juyo kawai tafasa,kwanciya tayi Akan gado, haka takwana Babu Dadi Dan har kuka Saida tayi.....

Uncle G fa yau Jikin yafi na kowanne Rana tsanani,Dan yanzu numfashin shine yake bugawa sama sama,Dan saida akasa Mai oxygen,wani  Dr. aka Kira ya shiga shi kaidai ya sameshi a dakin,Dan an bukaci kowa yafita,tunda Dr. yashiga Bai fito ba sai around 2pm,Dan tun 10am ya shiga, Zulaihat nee tabiyo Asibiti daga school tasamu su ya imran a waje,Suna sak'a dazama saiga Dr. Yafito,magana suke Mai Amma yayi banza dasu,Kuma yafito Yana zufa, Zulaihat ce tashiga dakin da yafito da gudu Wanda Uncle G ke Ciki,tana shiga taga an rufe Uncle G tundaga Kai har Toe dinshi,wanni irin K'ara tasaki a take awurin tafadi tasuma........✍️✍️.

*Ni Kuma kamewa nayi*



By Tooraee 🥰🥰🥰.



*(GOLDEN PEN)*

ZEEYABDOOLWhere stories live. Discover now