*ZeeyAbdool* 49

3 1 0
                                    

*Zeey💞Abdool*
       *(2021)*

*True Life Story*

*Love story*

*By Tooraee🥰🥰🥰*

⚖️
*HAMDALA WRITIN'S ASSOCIATION💪*
        _*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_
https://www.facebook.com/111403834371046

             *✨✨{{H.W.A}}✨✨*
     https://chat.whatsapp.com/IfZVNIt6C9S8PvTV10v3wZ

*Page 49*


"Bloody Bari naje na dawo koh?" "Toh saika dawo" murmushi yasakin Mata  Saida fararan hakoranshi suka bayyana,itama batasan sanda tamayar Mai ba Dan Uncle G is very funny.....

Fita yayi Yana murmushi jin Dadi,Dan Uncle Yana cikin wani yanayin da bazai musaltuba Dan Dadi,Dan gani yake yafi kowa ayau dinnan,Magana sukayi sosai da Oga Zayyad Akan yadda zai taimaki iyayan late Dr. Zulaihat,Dan itace take rike gidansu,so yadau Alkawarin zai dinga Basu wani Abu aduk karshen month,bayan sungama sukayi sallama yakoma gida,Koda yakoma gida shiyasake yin girki Dan ya iya Kuma Bai dameshi ba,Sukaci suka koshi da yan ciye ciyen dayazo dashi,bayan sungama Daman dare yayi baccin sun sukasha abunsu.....

B'angaran Abdool kuwa tunda aka daura auran Zulaihat yaji ajikinshi Babu yadda ya iya sai hakuri,wani katon agogo yasa akamai da hoton Zulaihat ajiki ya ajiye Akan idan yasamu Mai zuwa KADUNA ya kaimata,sai Duk sanda aka samu Mai zuwa P/Harcourt a Kai Mata, Abdool makaranta yakoma danshi yanzu Babu wani zancan Soyayyah agabanshi,karatu yasa agaba Dan yasamu pass din karatu.....

Zaman Zulaihat da Uncle G Babu yabo Babu fallasa,Dan tana Mai biyayyah Babu laifi,Dan batamai wulak'anci sosai,saidai wani Abu datakeyi yake damunshi a duk sanda ta tuna da Abdool sai taci kuka kaman ranta zai fita,wannan abun Yana daga Mai hankali sosai,Kuma in tayi kuka saita kwana zazzabi,yarasa yadda zaiyi da Zulaihat Kuma shima yasan Abdool take tuna a duk sanda tayi kuka,yaune abun ya isheshi Dan ba'ayin sati sai tayi.....

"Bloody Abdool Koh?"
"Ido tazaro,tana mamakin ya akayi ya gane"Murmushi yayi sannan yace "bloody kiyi hakuri kinji,da Abdool zai aureki wlhy bazan taba auranki ba,Dan Ina matuk'ar daraja farincikin ki Akan nawa,Amma kina da tabbacin idan narabu dake Abdool zai aureki?" Ido tazaro tace "a'ah Uncle,wlhy ba Abdool nake tunawa ba,ina son kawai inje gida nee kawai" "kin tabbata?" "Eh" "toh na Miki Alkawari idan cikinki ya Isa haihuwa a gida Zaki haihu,yamiki?" "Eh yamun" "kin tabbata?" "Eh" "to kiyimun Alkawarin bazaki K'ara kuka ba" "eh insha'allah" karfin Hali tayi tafa jikinshi tana murmushi,Dan taga Uncle G ranshi ya baci sosai Dan Bata kaunar taga yayi fushi,Dan Bai iya fushi ba,Dan bak'aramin Abu bane ke batamai Rai.....

Dayaga tana dariya shima Murmushi yayi yabiye Mata Suna Hira abunsu Mai Dadi,tun daga ranan Zulaihat Bata kuka agaban Uncle G,Dan batason taga Yana fushi Dan shima kokari yake yaga yasata cikin farinciki......

Wasa wasa Zulaihat takusan Haihuwa Dan cikinta ya tsufa sosai,tazama wata katuwa da ita Dan Uncle G ma tsokanta yake Yana cemata Mai Ciki,yanzu damuwar Zulaihat kadanne akan Abdool,Dan Uncle G is trying sosai wajan sata farinciki,Jirgi suka biyo yakawota KADUNA Dan ta haihu shikuma yakoma Dan weekend ne ba wani dadewa zaiyi ba, Zulaihat ce tadawo gida haihuwa sai Dariya ake Mata,Dan Duk kayanta sun mata kadan sai Uncle G yasai Mata dogayan riguna masu kyau wanda zata iya shiga jama'a dasu,Kuma yabata kudi dayawa Dan in tana son wani Abu,Kuma Yama Aunty Rahela transfer din kudin kayan haihuwan Baby Dana fitan sunan Mai jego......

Kwanan Zulaihat Goma da zuwa tafara na kuda,Tasha wahala sosai Amma ba'a gayawa Uncle G ba,Saida takwana biyu tana nakuda kafin Nan ta haifi yaronta dogo San talele kaman Uncle G Suna Kama sosai,Aunty Rahela ce tafara kiranshi tamai albishir habawa sai murna,sai dayayi sujadar godiya ga Allah,yayi murna sosai,Shida Oga Zayyad suka nemi pass Dan zuwa ganin Babyn su,cikin sa'a suka samu,Saiga su sunzo Babu wanda yasani, Zulaihat Tasha mamaki sosai,Yana zuwa a gida yasame su,Yana ganin Zulaihat ya rungumeta Dan murna,ya dauki babynshi Yana juyashi Yana kallonshi,kwallan murna nee yazubo ma Uncle G.....
"Allah yamaka Albarka yarona" saikuma ya rungumeshi kaman ance za'a kwace Mai,dakyar Aunty Hannafiya tazo yabata,Saida sukaci suka koshi kuwa sannan suka shiga d'aki Shida Zulaihat....

"Uncle"
"Na'am Babyn Uncle" "Daman inason kasawa Yaronnan sunan Abdool........✍️✍️"


*Toh fah,babbar Magana,fans in kune Uncle G,wanne amsa zaku Bata?*


By Tooraee 🥰🥰🥰.


*(GOLDEN PEN)*

ZEEYABDOOLWhere stories live. Discover now