*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story*
*By Tooraee 🥰🥰🥰*
⚖️
*HAMDALA WRITER'S ASSOCIATION💪*
_*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_
https://www.facebook.com/111403834371046*✨✨{{H.W.A}}✨✨*
*Page 55*
.......Auta na fita da Young G a hannu sai aka sake kira,daukawa tayi tak'ara a kunnenta,Muryan Daya d'aki kunnanta nee yasa hannunta yafara rawa tasaki wayan a k'asa......
"Innalillahi wa'ina ilaihirraji'un" abunda ta dinga maimaitawa kenan,shiko Bawan Allah Daya Kira sai magana yake Amma baiji an bashi amsaba,haka baisa ya kashe wayan ba, Aunty Rahela ce tashigo zuwanta kenan tashigo dakinta tace "lafiyanki kiketa salati haka?" Waya ta nuna Mata,kallon direction din hannunta tayi sai taga wayan,duk'awa tayi ta dauka,haryanzu Bai kashe wayanba yanajin duk abunda suke fada,Kara wayan tayi a kunne sai tafara magana.....
"Assalamualaikum" "Wa'alaikumuslam Aunty Rahela Ina wuni?" "Lah Abdool?" "Na'am, Ya Karin hakurin mu?" "Alhamdulillah" "Allah ya jikanshi da Rahma" "Ameen,Ameen mungode" "Ina my boy Young G?" "Yanan lfy" "Mash Allah,kima Mummy Gaisuwa da Aunty Hannafiya,kigaishe da Auta" "zasuji insha'allah,kama Zulaihat Gaisuwa?" "Eh namata Nagode Aunty Rahela,kigaishe mun da Ayyan" "zaiji insha'allah" kashe wayan yayi Yana maida numfashi,harzai lula duniyar tunani sai Kuma ya tuna Alkawarin dayama kanshi sai yatashi Yana murmushi rike da takaddun karatunshi.....
Zulaihat ce ta rungume Aunty Rahela tace "kardai kice mun Abdool nee?" "Eh shine,bakun gaisa ba?" "No banmai maganaba" "Amma yacemun kungaisa" "no a'ah" "barito nakirashi kaman ta'aziya zai Miki ai?" "Eh Amma pls don't call him" "ok shikenan" Zama sukayi tana Mata Hira tana jinta kadan kadan Amma hakalinta ba'a Labarin datake Bata yakeba tashiga duniyar tunanin Uncle G, Aunty Hannafiya ce tashigo, take Aunty Rahela tabata Labari,"Ayyah Bawan Allah,toh waya gayamai?" "Ina tunanin Aunty Farida Dan suna waya" "shine Kuma zata bashi number ta,batasan tana takaba bane?" "Kefa dadina dake Baki iya cin riban zanceba,saiki Bari inmutu kafin ki birneni,shin wayace Miki ma sunyi magana,nifa Yama Gaisuwa Koh tambayarta baiyi ba,yamace a gaisheki" "toh Ina amsawa,Dasai ince Kiran meyayi?" "Kedai Kika sani wlhy" duk wannan cabtan dasukeyi Zulaihat batasani ba,Dan tana tuna Uncle G dintane Sanda sukayi waya dashi Yana tareda Hajiyarshi dataso suyi video call Amma hakan Bai yuwuba,hawayene ya zubo Mata sai kuka, Aunty Hannafiya ce ta tabe Baki tace "Toh fah wannan managan dana fadane ya Bata Miki Rai? Toh Allah yabaki hakuri *Zeey💞Abdool*" duk maganan datayi batajitaba Amma taji zancanta na karshe,Ido Zulaihat tazurawa Aunty Hannafiya tanaso tagano metake nufi acikin idonta Amma takasa ganewa, Aunty Rahela ce tarufe Aunty Umma dafad'a "kefa matsalata dake kenan bakida kirki Koh kadan,yanzu a wannan halin datake cikine kike Gaya Mata wannan maganan?" "Ai gaskiya nafada" "kirike gaskiyarki ba'aso" fita Aunty Hannafiya tayi tana maganganu, Zulaihat kuwa binta take da ido tana mamakin Hali irin na Aunty Hannafiya, Aunty Rahela ce taita Bata hakuri har Kaka tashigo suka cigaba da Hira,Amma Banda Zulaihat tana Nan tana sana'ar......*Waiwaye*
Tunda Abdool yaji Labarin ansawa Zulaihat Rana ya sadaukar da auren kyakkawar shi,ya ajiyeso a gefe,ya koma rayuwar shi kadai, yakuma kudarci niyar komawa skull Dan yanada burin Zama Officer Amma Airforce,yamaida hankali Kan karatu Dan daman akwai Brain,yamanta dawani tunani Amma Soyayyar kyakkyawarshi tanan acikin Zuciyarshi,yanaba daughter shi kulawa yadda yakamata Dan yanzu baby ilham tagirma takai shekara D'aya darabi,Kuma bisa ga biyayyar iyayanshi ya maida matarshi Amma basa guri Daya yabarta a Gombe, Abdool Bai taba kawowa zai sake samun Zulaihat akaro nabiyu ba,Dan yayi saranda yabarma Uncle G ita,Koda yaji Labarin mutuwar Uncle G,yatausaya mata Dan har kuka Saida yayi danshi bawai so na aure kadai yakema Zulaihat ba har son yaga tana cikin rayuwa maikyau koda ace bada Shiba,yashiga Damuwa sosai,Dan washegarin rasuwar yagani a social media sai yakira Aunty Farida Dan ya tabbatar,shine take bashi Labari yadda abun yafaru Dan taso ma tahadasu awaya Amma yak'i saidai ya roketa ta turamai da number ta,yakai tsawon kwana bakwai Yana Danna wa zaikirata Amma saiya fasa,arana Koh babu adadi,sai ranan yafito daga class sungama yin wani exams Mai zafi,Su ashirin nee sukayi exams din, an zubar da goma an dauki goma Kuma shine first position, *karkumanta Abdool mahaddacin al-kur'anine,Kuma Koda yake soja Bai saki addininshi ba da tarbiyan shi,yanadaga cikin abunda Zulaihat yasa take sonshi Kuma take yarda da duk abunda yace Bata tantama* wannan sakamakon Daya ganine yabashi karfin gwiwar kiranta,shine yaketa kirantannan Bata dauka ba,har Saida Kaka takawo Mata wayar d'aki......
Tundaga ranan Abdool Bai sake Kiran Zulaihat ba,Amma Yana waya da auta har chart sukeyi ta Facebook,Yana sata Tana turamai hoton Young G Dan yadauki son duniya ya daurawa yaran biyu da ilham da Young G,sonsu yake sosai Dan duk jininshi yake daukansu,Wasa wasa Uncle G har yayi 40days,yaune Kaka zata koma Kano, Zulaihat tai kuka sosai Dan zatayi missing dinta Dan Kaka na debe Mata kewa,kakace taba Mummy shawara akan idan tagama takaban ta koma makaranta tunda Daman a diploma ta tsaya sai ta cigaba, Mummy tayi Na'am da hakan Dan hakanne ma a Zuciyarta....
Zulaihat na Kara watsakewa Dan Mummy tajata ajiki tana Mata maganganu nakwantar da hankali, hakama Deeja tunda akayi rasuwar ma tare suke kwana Dan intadawo daga skull gidansu take zuwa sukwana,Dan Koda suka Gama diploma ita tacigaba,akwana atashi babu wuya yau Zulaihat take Gama takaban ta,Deeja ce ta matsa Mata tasa sabon Kaya dakyar tasa Dan tace bazata Saba,ga Young G sai Zama kato yake abunshi shi baima son meke faruwa ba,bayan
Gama idarta Deeja ta siyo Mata form din HND na midwifery Kuma cikin ikon Allah tasamu,wani Abu dabaku sani ba tunda Abdool yakira Gaisuwa Bai sake Kira ba itama Bata damuba.......✍🏼✍🏼.*Uhmmm komai dalili? Oho🤷🏼♀️*
By Tooraee 🥰🥰🥰.
*(GOLDEN PEN)*

YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Fiksi SejarahLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su