ZeeyAbdool 42

1 1 0
                                    

*Zeey💞Abdool*
         *(2021)*









*True life story*






*Love story*❤️❤️







*By Tooraee 🥰🥰🥰*








Page 42







Shuru Zulaihat tayi tana kallon Mummy, Aunty Rahela ma tsura Mata ido tayi Dan taji Mai zatace......

Rungume Mummy tayi sannan tafara magana tana kuka
"Mummy wlhy inason in cire Abdool a Raina Amma bana tunanin haka zaiyuwu,Amma tunda kinason hakan Zan kokarta,Dan Mummy nayi ladaman rashin jin maganar ki,danaji magananki Mummy dabanshiga halin danake cikiba a yanzu,Daman kina fada mun Duk gaggan dayacika Zaki fashewa yakeyi,gashi kuwa wannan gangan yafashe,Dan Allah Mummy kiyafemun" sai kuka Shar......

"Haba Zulaihat kibar kukannan, Mummy ai ba Baki tamiki ba, a wancan lokacin Gaskiy take gayamiki Amma kin kiji"
"Hakane oya kiyi shuru kinji,komai yawuce kinji Zulaihat"
"Thank you Mummy"

B'angaran Abdool kuwa kukan zuci yakeyi,Dan yanzu yariga ya sadakar bashi ba Zeey💞Abdool...
Zulaihat kuwa jiki yayi sauki sosai Dan haryanzu Bata kunna wayantaba,Dan anma sallamesu Uncle G ma yakoma...

Jikin Zulaihat sai sauki yaketa karayi Amma a Zuciyarta batajin Dadi,Dan yanzu tanason tamanta da komai Amma Koh sunanta Aka kira Yana dawo Mata da komai *Zeey💞Abdool*,Dan a wannan karon tayi danasani canza sunanta,Gashi Kuma ta kunna wayanta Amma Koh flashing Abdool Bai Mata ba,wannan abun ya mugun d'aga Mata hankali,tunani tashiga tana zaune
*Ashe Abdool zai iya mantawa Dani?Daman nine nadamu dashi?Nima in hakane yakamata in shafe tari hinshi*
Hawayene yafara zubu Mata in tana tuna Abubuwan dasuka faru a baya "innalillahi wa'ina ilaihirraji'un Aunty Hannafiya kinyi gaskiya dakike gayamun indaina zak'ewa?ya Allah kashiga lamarina"

Abdool kuwa washegari ranan dayadawo nee suka tafi yakin BH,Dan abun Babu sauki,Kuma DAJI dasuka shiga Babu network,Kuma Koh Akwai network bashida Daman iya yin waya gaskiya Dan yaki suke Babu dare Babu Rana,lamarina abun ya sauya Dan Sun musu bazata wannan Karan,su Abdool sun saki jiki suna tafiya a DAJI,Ashe BH sun kwanta a Ciki DAJI sunyi flat Basu sani ba,kawai sai sukaji wutan bullet.
Habawa sai salati Shatima nee yarude Yana cewa "Oga Abdool Innalillahi wa'ina ilaihirraji'un mutanan sun mamayemu"
"Just go dwon Shat..."
Bai k'arasa magana ba kawai sai bullet a  kirjin Shatima,salati Shatima ya saki kawai,habawa suka budemai wuta Shikenan sai Gashi ya fado Jikin Tubabbe...
Wani k'ara Abdool yasaki tare da gujin kuka"shateeeeeeema pls pls pls na rokeka karka tafi kabarni" habawa Shatima yatafi, Tubabbe zai Mike Abdool ya janyoshi ya Fado jikinshi,kuka Abdool yasaki Yana rungume da shatima Yana kuka yana Kiran sunanshi,Amma Shatima yariga mu gidan gaskiya,Gashi Kuma wuta suke Kara bude musu, Tubabbe ma kukan yake Yana cewa....
"Ya zamu koma Babu Shati...."
Bai k'arasa ba kawai yaji Abdool yayi k'ara, bullet nee ya gugi bayan Abdool ya wuce, Abdool nee ya zuciya idonshi yayi ja,ya Miki yafara fafatawa harbi yake Yana kuka,Gashi sun biyosu,Gashi sun Kona musu motocin yakin su Guda Biyar,Gashi bazai iya daukan Shatima ba yayi nauyi,Gashi Kuma sun fisu yawa sun kusan cin musu,rasa yadda zaiyi yayi kawai ya Duka Yama Shatima Kiran Sallah a kunne daga Nan ya Dan haka Rami kadan yasa ganye da k'asa ya rufeshi,bayan yacire bindiga da sauran abunda yadace da in mutu ya rasu suke submiting.....

Suna sak'a da hakan saiga wani BH yakama Tubabbe Abdool nee ya juya ya karemai tanaji,yaja Tubabbe suka Fara gudu, Tubabbe nee ke waigawa Yana ihun sunan Shatima kaman zai koma  wurinshi Amma Babu Hali Dan saura kadan su cin musu,Suna cin gudunne sai ga a yarinsu Malan Ahmad sun hadu, haduwa sukayi suka musu fata fata Amma Duk dahaka abun Bai biya Abdool Shatima ba,bayan tashin hakalin ya lafa, Abdool yafara magana Ciki fushi da tashin hankali....

"Malan Ahmad Shatima yarasu,danasan Shatima zai rasu da nabarshi lokacin dayace zai tafi bazai iyaba tun muna deport"
"Yes natuna,Amma ai bazai taba sallakewa ajalinshi ba"
"Hakane Amma we r going to Miss Shatima, pls everyone here should pray for him,Shatima has gone"

*Allah sarki Shatima,Allah ya jikanka da Rahma,may ur soul continue resting in jannatul firdaus and da Duk sojojin NIGERIA gaba Daya (R.I.P)*

Uncle G zaune suke da Dr. Dinshi a wurin cin Abinci Suna Hira tana bashi Labari Yana Shan Dariya,Dan yanzu yafara son Dr. Sosai sosai,kulawa yake samu daga gurinta shima haka Yana iya kokarinshi,Dan tunda yakoma yakira Zeey💞Abdool so Daya yamata ya jiki Bai Kara ba,Dan yaji muryanta Alhamdulillah........

Mummy nee ta nemoma Zulaihat Admission midwifery dake Tudun Wanda a Asibiti dutse,Dadi Zeey💞Abdool Taji Dan koba komai zata samu sauki a cikin zuciyar ta....

Wasa wasa yau Watan su Abdool Daya a cikin DAJI inda Kuma ita Zeey💞Abdool tafara zuwa skull abunta ta Dan ta rage damuwa, Uncle G kuwa har sunfara maganan Aure da Dr. Zulaihat Dan tace Mai yakamata suyi Aure,yace toh tabari insha'allah zaizo suyi magana da iyayanshi duk abunda sukace zai gayamata....

Karatu ya kankama Dan yanzu Zeey💞Abdool Babu zancan soyayyah yanzu tama manta da a tunainta Abdool yarabu da ita har abada,itama  takoma rayuwar ta ita kadai Koh saurayi Taki yarda dashi,zaune take a tsakar gida tana kallon status kawai sataga hutana Uncle G yasa a status ya hadawa budurwanshi birthday Gashi tayi kyau sosai hadda zuwa Studio akayi Hotuna zafaffu,Babu abunda yabata mamaki sai dataga yasa *Dr. Zulaihat*, muryan Aunty Hannafiya taji daga d'aki tana magana tana fitowa...
"Zulaihat zokiga Lamari,abun Uncle G Babu sauki,Kinga wasu zafaffanfun Hotuna?"
"Nagani ba status ba?"
"Eh,Kinga yarinyar ta hadu"
"Babu laifi tayi kyau daidai nata"
"Aikuwa,Amma Uncle G yakashe kudi"
"Gaskiya kinsanshi ai da bautawa mutane,saidai in baka kusa dashi"
"Aikuwa,dayanzu ke aka hadawa wannan abun Arziki Amma Kika bararda Daman ki"
"Bawani menene abun dama anan?"
"Aikoh Akwai tunda bawan bawan"
Shuru Zeey💞Abdool tayi Dan tasan halin Aunty Hannafiyan batada kirki wani sa'in,kukanta Tasha tagodewa Allah sannan har tamike zata shiga d'aki saiga Kiran Abdool ya shigo....✍️✍️.




By Tooraee 🥰🥰🥰.





*(GOLDEN PEN)*

ZEEYABDOOLWhere stories live. Discover now