ZeeyAbdool page 66

0 2 0
                                    

*Zeey💞Abdool*
        *(2021)*

*True life story*

*Love story* ❤️❤️


Page 66

........ Network yaki barinsu su sake kasancewa da juna,gashi ya dauko Mata magana Mai anfani,gashi network yak'i,Koda suka koma normal call sai busy,Dan suna neman juna a tare,a take suka yanke shawaran hakura sai gobe Dan duk a tunaninsu network dinne.......

Abdool kuwa tashi yayi yafara nafiloli Dan sake godewa Allah,Dan yanada yakinin zai samu *Zeey💞Abdool*  akaro na biyu,Dan Koda sukayi waya da mamanshi ta nuna Mai babu matsala zata samu babanshi.........

Bangaran Zulaihat kuwa bacci ya kaurace Mata, tunani takeyi........

*🥺🤔wanni irin laifi nama Mai kyauna haka? Ya Allah kasa bawani babban laifi bane,Dan banason in rasa Abdool akaro na biyu*.......

Gajiya tayi da zulumi da tunani ta tashi ta dauro alwala tafara nafiloli Dan neman mafita tareda dama Uncle G Addu'a,Dan Zulaihat Bata mantawa wajen yima Uncle G addu'a kwata kwata........

Washegari da sassafe bayan ta idarda da sallah ta Kira Abdool, Abdool murmushi yayi Dan ganin kiranta,jira yayi Kiran ya katse kafinnan ya kirata back........

"Assalamualaikum" "Wa'alaikumuslam kyakkyawata" "Na'am" "kintashi lfy?" "Lfy lau" "banyarda ba?" "Bakai bane?" "Menayi toh?" "Mai kyauna?" "Na'am" "bakaine kace namaka laifi ba?" Murmushi yayi Mai sauti,Dan duk maganan datake Mai a halinzu cikin shagwabane da itama batasan tayi ba,Dan Daman Zulaihat akwai shagwaba,kuka ta sakin Mai hade da shagwaba,Ido ya zaro "Rayhana kuka Kuma?" "Bakaine kake mun dariya ba?" "Toh kiyi hakuri kinji?" "Toh nayi" "dawuri haka?" "Eh Mana,kana son in samu matsala da Zuciyata ne?" Ido ya zaro kafin yace "Akan me?" "Kasan Zuciyata Bata yarda kana kuskure ba balle kuma laifi,tayaya toh kakeson in karyatata akan abunda yake ba hakaba awurinta?" Shuru yayi Yana mamaki........ 

*Ashe laifine kawai Yama Zeey💞Abdool? Bawai soyayyar shi bace ta rushe? So  son da Zeey💞Abdool take Mai da bawai kuruciya bace?........* "Mai kyauna lfy?" Wannan maganan datayine yadawo dashi daga tunanin dayakeyi,gyaran murya yayi,ya naimi wuri ya zauna Dan duk maganan da sukayi dazun a tsaye yayishi,Saida ya natsu sosai,Dan harta fidda Rai zata kashe wayan sai taji muryanshi daga sama......

"Zulaihat?" Cikin rawan murya ta amsa "Na na 'am" Bai damu da hakan ba yacigaba da magana,cikin muryan babu wasa bare sassauci "Izunki nawa yanzu a Hadda?" Ido ta zaro Dan rabonta da hadda ta manta,saidai kullun da safe bayan tayi sallan asuba zatayi karatun Alkur'ani,Amma hadda ta ajiye tun randa ta yanke shawaran zata rayuwa da Uncle G..........."

Katseta yayi ta hanyar cewa "kin wasar Koh?" nanan ma shuru,Bai wani shiga mamaki ba Dan yasan hakanne ma,ga mamakinta sai taji yafara karatu ta hanyar farawa da basmala..............

Ido tazaro waje😨,Bata K'ara shiga mamaki ba Saida taji yace "cigaba Ina sauraran ki" cikin inda inda tafara itama da basmala,gamamakinta sai taji tana kawomai daidai,Dan Daman wurin takeyi muraja'a,haka yayita jamata cikin izu 5 din dayasan sun had'a,yadanji Dadi kadan Koh ba komai nabaya Bai Zube ba, "Amma yanzu Zulaihat Ashe Zaki iya sakaci da lahiranki Dan bakyatare Dani? Idan narasu nabarki da yarana bazaki iya jajircewa bakenan akan karatunsu ba? Zulaihat banji dadin abunda kikayi ba,Dan inada tabbacin  Marigayi bazai hanaki hadda ba a gidanshi,koshi kikace ya amsar Miki ai zai amsa" Jikin Zulaihat ne yayi sanyi,yanzu tagane kuskuren data tabka,Amma kunya da ladama ya hanata magana,wasu hawayene masu dumu suka zubo Mata...........

Yana Jin zafin kukan datakeyi Amma bayanda zaiyi,Dole yanuna Mata kuskurenta Koh Dan gaba, "Azkar fa anayi?" Cikin shashshekar kuka tace "Eh" "Ok Bismillah" haka ta dinka Karan tomai azkar kala kala tana fassaramai su dakuma inda ya dace ayisu,hadda Wanda Bai koyamata bama duk ta karanto Mai,wani sanyi yaji sosai a aransa,kobakomai ta wanke kanta "madallah da kyakkyawata,Allah yami Albarka" shuru tayi Bata amsa ba, "Fushi kikeyi Dani?" Cikin sanyi tace "a'ah Rayhan" "Toh bakice ameen ba?" "Ai banyi Abu gwaninta ba,Da har na cancanci wannan Addu'ar" "Kinyi *Zeey💞Abdool* ,Kar kidamu kinji? Zamu cigaba daga inda muka tsaya, Kuma azkar dinnan dakika kawo,duk kin wanke laifinki a wurin"

Murmushi tayi Mai sauti,Dan Zulaihat nananda da hanlinta na in har akace Mata *Zeey💞Abdool*  sai taji farinciki,ko dama datake cewa bataso fada kawai takeyi amma Yana Mata Dad'i acikin Zuciyarta...........

Wani Abu da Zulaihat Bata sani ba,tunda suka Fara waya Mummy tazo daukan Young G Dan tamai wanka,Amma dataji tana waya saita tsaya a bakin kofa tajin abunda Zulaihat ke fad'a,Dan daga amsar da Zulaihat keba Abdool ta fahimci zancen su, Murmushi girma Mummy tayi takoma dakinta,tana Mai farinciki dawowan Abdool rayuwar Zulaihat,Dan Bata fahimci Abdool nada anfani a rayuwar Zulaihat ba Saida suka rabu,Dan bini bini Zulaihat na cikin karatun Alkur'ani a da,in kuma batayi da Baki zata kuna wayanta tanaji,Kuma ga Abubuwan addini sosai da Zulaihat take koyawa auta idan Abdool ya koya Mata,Amma tunda suka rabu da Abdool shikenan saidai karatun asuba da akeyi kullun da safe
Agidan Dan wannan wajibine.......

Mummy Daman tana son Abdool,Amma batason yadda Zulaihat take sadaukar da komai akanshi, "Amma a wannan karon Zulaihat,nabaki goyan baya dari bisa dari" kaman daga sama taji fati tace "dagaske Mummy?" "Eh autana" "Alhamdulillah Mummy Daman ke mukeji wlhy,shiyasama bamu daukaka abunba" Mummy ce ta harari fati kafin tace "aikoh Baku daukaka ba tunda gashi har kunyi celebrating 1m followers a IG" dariya fati tafashe dashi kafi tace "lah Mummy Daman kinsan page  din *Zeey💞Abdool* a IG?" "A'ah ke kadai ki Kika sani,ni jeki dauko mun GARZALI in Mai wanka muje gidansu Deejah aiki"  fuska Fati ta B'ata Dan ta tsani ana cema Young G GARZALI, "nije ki dauko munshi,basunan shi bane?" "Eh sunanshi,Amma Young G yafi dad'i" "ai saiki canza mai" fita fati tayi tana magana..........

B'angaran Zulaihat da Abdool kuwa sun Gama waya har ta hau online tafara musu wasu new posting.......

Abdool kuwa Yana Gama waya Kiran Mamanshi yashigo wayanshi,kiranta yayi suka gaisa tare damai Albishir, "Goro Ummana" "Babanku fa ya yarda" tsalle yayi ya zauna, "Dan Allah?" "Toh da Ina wasa dakaine?" "No Ummana,kawai nashiga mamaki ne?" "Koh nima haka,ban kawo zai yarda ba,Amma ga mamakina sai yace ya yarda,Koh Dan biyayyan dakamai a tashin farko,bazai tab'a mantawa da biyayyar da kamai ba,Kuma Yana matukar alfahari dakai a matsayin babban danshi" Murmushi Mai sauti Abdool yayi baice komaiba,"Toh Ina tayaka murna zaka Auri Mai kyauka" "lah hadda ke Ummana?" "Ai yakamata naso abunda yarona yakeso tunda Bai sabawa addini ba" "Nagode Ummana da irin kyaunar dakike nunami........" Bai karasa magana ba tace "shiiiiiiiii,yanzu tsakinana dakai ai babu godiya,Allah dai yasa ayi damu" "Ameen Ummanmu" Murmushi tayi suka cigaba da Hira,Dan idan ta Hira da Abdool kamar karsu ajiye waya haka takeji,yanzuma matsamai take yaushe zai dauwo,yasanar Mata next week insha'allah,ana Gama bikin Deejah..........✍🏽✍🏽.

*Toh fah fans😍💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 bikin Bestyn Zeey💞Abdool yazo,Amma bama gayyanta fans din Zeey💔 Gali 😆😀🥴*

By Tooraee 🥰🥰🥰

*(GOLDEN PEN)*

ZEEYABDOOLWhere stories live. Discover now