*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love Story* ❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰🥰*
⚖️
*HAMDALA WRITER'S ASSOCIATION💪*
_*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_
https://www.facebook.com/111403834371046*✨✨{{H.W.A}}✨✨*
*Page 56*
....Bayan
Gama idarta Deeja ta siyo Mata form din HND na midwifery Kuma cikin ikon Allah tasamu Admission,wani Abu dabaku saniba tunda Abdool ya Kira yayi gaisuwa bai sake Kira ba itama Bata damuba,shiko duk abunda yake Yana sane don Yana samun information a wurin auta da Deeja Dan yasamu number Deeja nee a wurin Auta,har date din data fita daga takaba yasa acikin diary dinshi,Dan Daman Diary dinshi nanusamman nee,abongon Diary din an rubuta *Zeey💞Abdool* da salo Mai kyau,aciki Kuma ya rubuta date din dasuka Fara waya,date din dayafara zuwa Kaduna wurinta,date din dayafara sata zubda hawaye a dalilinshi,sai Kuma date din Daya fidda ran auran Zulaihat wato date din auranta da Uncle G,dan koh da ana gobe bikinta Bai fidda Rai ba, Sai Kuma date din data bar gidan mijinta wato ranan da Uncle G yarasu,sai date din idarta,duk suna cikin wannan dairy din, Deeja nabashi kwarin guwa sosai akan yadawo akaro nabiyu Amma yak'i,Bai San ta inda zai Fara ba Bai San yaya zaiyiba,Dan Abdool yanada zurfafa tunani akan Abu kafin ya aiwatar,duk wannan wainar da ake toyawa tsakanin Deeja da Auta da Abdool Zulaihat Bata saniba,Dan a Halin yanzu tafara zuwa lectures tare da Young G,Dan Mummy ma tayi tayi tana dinga barmatashi suna zuwa Office Dan tasamu tayi karatu da kyau Amma Tak'i,Dan tace young G shine Last hope dinta,bazata iya wasa dashi bakuma....Zulaihat ta wayi gari kawai da farinciki da nishadi jinta take sawai,bayi tashiga Tai wanka sannan tafito tasa kayanta cikin natsuwa Dan Uniform suke sawa,fitowa Palo tayi ta amshi Young G a hannun Aunty Hannafiya tagama Mai shiri tsaf,Dan Koda sukadawo KADUNA daga P/Harcourt Aunty Hannafiya kemai wanka,Dan har yafara Gane Aunty Hannafiya Dan sukanyi wasa sosai da ita,Dan idan Zulaihat zata makaranta kanta kwai take shiryawa saita fito ta amsheshi,tana amsarshi taga yadda tashirya Matashi yamata kyau sosai,daukanshi tayi tana murmushi tana tafiya tana mamakin Aunty Hannafiya *Mai hali a murde,itadai baruwanta indai gaskiya tazo zata fada, baruwanta da halin dakake ciki,ko yazakaji dadi ko sabanin haka,ita dai baruwanta da Mai zai faru? No itadai tafada,kafama dashi* dariya tayi tace "Aunty Umma duniya" rungume Young G tayi tana murmushi,itama tarasa Meke sata farinciki,kamshin turaran da Aunty Umma kesawa Young G Yana Mata Dadi sosai da sosai,Koda ta Isa makaranta mikashi tayi wurin Mai raino tashiga class,yaune Zulaihat tafara fahimtar Abu sosai a makaranta tunda tadawo HND,Dan Koda can kadan kadan take ganewa sai intazo gida ta duba,Amma yau dabanne ta fahimta sosai da sosai Dan a ganinta babu bita yau intaje gida,Koda suka fito daga lectures ita kadai taje ta dauko yaronta Dan Daman Bata da k'awa dasuka wani shaku sai Deeja Kuma bama ajinsu D'aya ba,Dan Deeja na zangon karshe,Zama tayi k'ark'ashin bishiya tana shakar iska Mai Dad'i tareda ma young G Wasa,shiko Bawan Allah sai wangale Baki yake Yana dariya,suba nishad'i.....
Tun daga nesa ya hangota, kwarjinin data Mai nee yasa yafi mintuna 10 Yana shawara da Zuciyarshi kafinnan yafara takawa zuwa wurinta,Koda ya Isa wurinta baiyi sallama ba dan duk a daburce yake yarasa ma meyasa ya iso wurinta,tsayawa yayi akanta dan yarasa ta Ina zai fara, wani kamshin turarene da Ko inana tajishi bazata taba manta mai Shiba ya daki hancinta,shuru tayi tana nazarin turaran Amma sai ta kyarta Zuciyarta akan amsar da tabata,jin kaman numfashin mutunne a samankanta yasa ta d'aga K'ai dan taga waye? Daga Kan dazatayi sai ihu,Dan saura kadan ta yarda young G badaban wannan mutumin yacabe Shiba.......✍🏼✍🏼.
*Aganin ku waye wannan😨🤷🏼♀️?*
By Tooraee 🥰🥰 🥰
*(GOLDEN PEN)*

YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Historische RomaneLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su