ZeeyAbdool 69

5 2 0
                                    

*Zeey💞Abdool*
         *(2021)*

*True life story*

*Love story❤️❤️*

*By Tooraee 🥰🥰 🥰*

*Page 69*

Murna da shirye shiryen tarban a halin Abdool zuwa KADUNA ya cigaba,Dan yau saura kwana d'aya su taso, zasu taso ranan Alhamis zasu sauka a Unguwar sarki,sai washegari ran juma'at zasuje neman auran *Zeey💞Abdool*........

Zulaihat takasa zaune takasa tsaye,Dan cike take da murna,gashi Aunty Rahela tazo domin shirye shirye,Dan aiki ya ma Zulaihat yawa.....

"Aunty rahela,wlhy ina missing din Aunty Umma,Dan datananan  da yanzufa duk girke girken Nan da zamuyi gobe ita zatayi,saidai naji da shirya kaina"  "Allah sarki Ummana,ance tacika masifa Ashe tanada Rana?" "Tana dashi Mana,ai koh karema yanada Rana bare Hannafiya,matsalar ta d'aya masifa kawai" "ai gashi batanan saikuyi abunku koh?" "Eh haka zamuyi,Dan ma Deejah tana Mana farfesu a gidanta,Kinga ai ta ragemana" "eh Masha Allah, Amma dai ana kewar y'ata" "sosai ma Mummy".......

*Lolx Mom Anwar kinji ana kewar Aunty hannafiya koh,Amma da ace ta cika masifa🤣😂*

Shirye shiryen ya cigaba da gudana har washegari, su Abdool suka taso, Abdool fa yaga Abu Dan minti minti Zeey💞Abdool saita kirashi,dayike Yana gaba basu cika sanin sanda yake answer calls dinba,Kuma dayike abbanshi baya cikin Yan zuwa neman auren.......

Alhamdulillah,tafiya tayi Albarka,Dan Abdool sun sauka lfy a Unguwar sarki Around 5pm,Dr. Sameer nee ya kaimusu Abinci har masaukin su,Kuma ya zauna ya musu sannu da zuwa har suka tab'a Hira,daga Nan yatashi yamusu sallama Saida safe Dan har 9:00PM yayi.......

B'angaran Zeey💞Abdool kuwa,aikoh kaman yau take sallah,Dan murna wurinta babu k'akkautawa,Dan gani take kaman daurin aure suka Zo,gashi basuyi wani waya sosai da Abdool ba,Dan yagaji sosai bangajiya kawai tamai sukayi sallama,itama bacci ne yasaceta bawai Dan tanaji ba........

Washegari

Da sassafe Zulaihat da Aunty rahela suka tashi Dan hada breakfast,Dan Deejah batajin Dadi sosai,dakyar ma ta iya dafa musu farfesun,Amma taso ta musu breakfast din dakanta,suna gamawa saiga Dr. Sameer yazo daukan Breakfast.....

Bangaran su Abdool kuwa mamakine yakama iyayan nasa,Amma bandashi da yasan yafi haka agunsu Mummy,Kari Mai Rai da lfy sukayi,Dan duk abunda bahaushe Dan arewa yake buk'ata yayin Karin kumallo ,su Aunty rahela sun tanada musu a breakfast dinsu Dan harda Masa (waina).....

*Uhmmmmm nikam sai hararan Abdool nake Dan yaki yasanmun😒😒,kodai baison ina kallonshi bane? bari na K'ara kura Mai idon toh,koh zai ganni😂😁😆*

Bayan sun Gama breakfast tare da Dr. Sameer Dan baffannin Abdool sunce Dole sai sun k'arya tare,haka ya cire kunya suka karya tare,suka danyi Hira sai sukayi wanka suka shirya sai hayin rigasa Dan zuwa neman auren *Zeey💞Abdool*.....

Hayin rigasa

Alh. Baba yashirya tsaf domin tarban ahalin Abdool,Dan anyi musu tarba sosai,su gwaggo Baki har kunne Dan abunnema yasamu,kowa sai murna yake ana jiransu Abdool su iso,Dan a musu lunch din dazasu ci,Dan yanzu ana neman 11am da safe.....

Abdool nee da Zulaihat suke WhatsApp chart a yayin dasuke hanyar zuwa hayin rigasa.....

'Mai kyauna yanzu kuna Inna?' 'Rayhana mun kusa isa' 'Masha Allah, Allah ya kaiku lfy?' 'Ameen kyakkyawata, Mrs Abdool bari mun iso,zuwa anjima zumiyi magana' 'ok Allah yafito daku lfy' 'Ameen Oum Rayhana and Rayhan'......

Sauka yayi,yasa wayan a aljihu yafita Dan ganin yaya musty da Yaya imran a kofar gida suna jiran saukowan su,sauka sukayi yayin da su Yaya musty suka tarbesu cikin girmamawa da mutunci tare da shigar dasu cikin gida,da isar dasu sashin Alh. Baba......

Bayan Gama charts dinsu *Zeey💞Abdool* tsalle ta hauyi tare da rawa,Dan taji dadin sunan da Abdool yakirata wato *Oum Rayhana and Rayhan*.....

Bayan shigansu Abdool b'angaran Alh. Baba,aka musu tarba sosai da Abubuwan ciye ciye da na sha,sunga tarba sosai tareda bama junasun girmamawa da mutunci da Uncle's dinsu Zulaihat ma duk sunanan,Dan bayan Alh. Baba yasa an Mai binciken Abdool a gombe ya sanar musu da suzo zancen auren Zulaihat ya taso.......

Bayan gaishe gashe da bangajiyan hanya da sukama junansu ne,tareda Y'an Hira da baza'a rasa ba na gabatar da Kai akan kowa yasan matsayin kowa a wurin yaran nasu biyu,shine Alh. Baba yafara magana kamar haka..........

"Ni sunana Ahmad Abdullahi,Ni wane ga Ibrahim Abdullahi Kuma nine babban wansu gabad'aya,Kuma Dan uwana mahaifin wannan yarinyar ya daukeni tamkar mahaifin nashi,duk abunda yakeso yayi sai ya nemi shawarana kafin yayishi,Kuma Koda yanada Rai nine madaurin auren su Zulaihat,inason in rokeku wani alfarma guda D'aya,tunda su yaranan ba yara bane Kuma bawai auren farko bane,gashi Kuma daga gari Mai nisa kuke,Akan ace ak'ara taso daku kuzo daurin aure akaro na biyu,y not bayan munyi sallar juma'at a daura kawai a masallaci"

Aikoh kaman jira suke baffannin Abdool suka had'a Baki,Dan sun tattauna haka da mahaifin Abdool a gombe Amma yace su bari sai iyayan Zulaihat sun buk'aci hakan......

"Masha Allah,ai hakan yayi Allah ya kaimu bayan sallah juma'at lfy ai sai a daura,Allah yabasu zaman lfy" "Ameen Ameen mun gode sosai da wannan fahimtar"

Abdool kuwa sai murna,Dan yakasa boye murnanshi,dan Shima yaso hakan Amma baiga fuskan tunkaransu da wannan zancan ba,yaso yakira Zulaihat yagaya Mata Amma yayi tunanin koh an sanar Mata.....

Alh. Baba nee yakira Mummy yamata bayanin,Dan daga baya sai suyi duk shagalin da suka ga zasuyi, "hakan ma yayi,Allah yabasu zaman lfy, Masha Allah" "Nagode Hajiya Allah yasaka da alheri" "Ameen Ameen"....

Duk wannan budirin da a keyi Zulaihat batasani ba,Dan ko bayan Alh. Baba yagaya ma Mummy Amma Bata gaya Mata ba Dan so take sai an daura
Tukuna......

Haka koh akayi Dan bayan an sakko sallan juma'at aka daura auren *Zulaihat Ibrahim Abdullahi da Abdoolsamad Abdulaziz* bisa sadakin naira dubu dari,Wanda dubun jama'a suka shaida,Dan Yan buk'aci mutane su tsaya bayan an idar da sallah juma'at..........

Mummy ce ta Kira Zulaihat da Aunty rahela tana sanar musu,Dan Yaya imran ya Kira ya sanar Mata an daura......

Ana Gama daurin aure Dr. Sameer da Abdool suka kamo hanya zuwa D'an Mani.......

Zulaihat tarasa ma mezata ce,fararan hakoranta kawai kake gani a waje,tarasa mema zatace, Aunty rahela ce kawai take cewa "Masha Allah,Abu yayi kyau,Amma Abdool din yasani?" Zulaihat ce ta juya tana kallonta Dan itama wannan tambayance a cikin Zuciyarta,fitowa parlour tayi da sauri Dan ta kirashi......

Still tayi a tsaye Dan ganinshi datayi a parlour tare da Dr. Sameer,Dan Deejah ma na hanya,Dan Dr. na gaya Mata an daura auren *Zeey💞Abdool*  taji ta warke Dan burinta ya cika.....

Zulaihat ce ta kurawa Abdool Ido Dan gani take kamar mafarki wa yannan Abubuwan ke faruwa, Abdool koh hawayan murna ke zubowa daga idanuwanshi,sufi minti 10 ahaka,Dan itama hawayan takeyi, Abdool nee ya Juya ya kalli gabass yayi sujjada, Zulaihat naganin haka tabi bayanshi.......✍🏼✍🏼.

*Nima dai inbi bayansu Koh my Xuuby🤩🤩🤩*

By Tooraee 🥰🥰🥰

*(GOLDEN PEN)*

ZEEYABDOOLWhere stories live. Discover now