ZeeyAbdool page 61

0 1 0
                                    

*Zeey💞Abdool*
       *(2021)*

*True life story*

*Love story* ❤️❤️

*By Tooraee 🥰🥰🥰*


*Page 61*

......Abdool Yana kofar gida a tsaye saiga Aunty Hannafiya ta dawo daga unguwa,d'aga Kan dazatayi Saita ganshi, k'ara bude idonta tayi Dan taga waye? "Tabbas Abdool nee,Toh meyakawo shi? Kuma Mai yazo yi?,Kan tarufe Baki sai taji Ayyan na ihu....... "Oyoyo Uncle Abdool, Oyoyo Uncle Abdool" waigawan dazatayi Saitaga Aunty Rahela na kokarin saukowa daga keke,Baki tasaki galala Dan tashiga mamaki,takowa yayi tareda da Ayyan Wanda yake rungume dashi,"Aunty Rahela Ina wuni" "lfy Lau,Kaine a garin not?" Hannu yasa a aljihu yaciro kudi zai biya "ah haba kabarshi Pls,ga kudi Nan Zan biya" murmushi yayi yamik'a ma Mai keke kudi sannan yace "Malan mungode Koh?" "Nikeda godiya yallabai" Murmushi kawai yamai,Mai keke yatafi Yana fara'a, Aunty Rahela ce tace "mun gode ko" Aunty Hannafiya na tsaya tayi jungum tana kallon ikon Allah,yadda taga Aunty Rahela na fara'a "y'anya batasan da zuwanshi ba? To dai bari naga ikon Allah" Aunty Hannafiya Bata shiga mamaki ba Saida taga Deeja tafito da fara'a,"lah Aunty Rahela kune?" "Wlhy mune my Deeja" "sannu da zuwa" "yauwa,ehmmm Deeja pls gayawa Mummy Abdool na waje sai mushigo kinji" "ai nazo shigo dashine" "ah toh badamuwa, Bismillah mushiga Koh" Abdool nee yaketa murmushi Dan tunda yazk yake kallon Aunty Hannafiya data dade a tsaye Bata karaso sun gaisaba,Magana yafara a hankali a natse kaman ba soja ba,"Ayyan jeka Kama Aunty Hannafiya Oyoyo Mana" waigawa sukayi gabad'aya,Deeja ce tace "Lah Aunty Umma harkin dawo?" Fuskewa tayi tace "Lah Abdool nee a Kaduna" "nine Aunty Hannafiya,sannu dadawo" "yauwa sannu" Deeja ta lura da mood din Aunty Umma,Amma ta basar Dan ita yanzu takusan Gama aikinta insha'allah,yadda take gani.....

Mummy tayi farincikin dadewarsu Basu shigo ba,Dan tashi tayi ta kunna turare dake burner ta,Dan Mummy akwai son kamshi sosai,kafin sushigo Palon, kamshin turaran harya iskesu a gate, Abdool lumshe Ido yayi,Dan yayi na'am da kamshin,duk abunda yakeyi Aunty Rahela na ankare dashi, dukkansu suka shiga d'akin a tare Amma Banda Abdool,ya tsaya nesa da Palo Yana jiran ammai izini,wannan abun dayayi yak'ara burge Aunty Rahela sosai Dan tana masifar son mutun Mai natsuwa da hankali sosai, Aunty Rahela ce tace "Ayyan cema Uncle Abdool ya shigo" Sallama yayi yayin shigowa,Zama yayi a k'asa akan carpet dake shinfide a Palon, Mummy ce tace "ya zaka zauna a k'asa ga kujera" murmushi yayi sannan yace "Na gode,Ina wuni Mummy" "lfy Lau,Ya hanya?" "Alhamdulillah" shuru sukayi na Dan wani lokaci sai Kuma yace "Mummy ya hakurin mu na Uncle G" "Alhamdulillah" "Allah ya jikanshi da Rahma,yakuma rayamana young G Kyakkawar rayuwa" "Ameen,mun gode sosai,Allah yabar zumunci" "Ameen" "Deeja tace kadawo Kaduna ko?" "Eh mummy nazo karatune" "Eh haka tace mun,wai taganka nee a 44 hospital shine kake Bata labari ai, kadade anane?" "Eh Mummy na kwana biyu,Dan na kusan 1year anan" "1 year fa Abdool?,shine bakazo kagaya Mana ba,ko kakira Ni ko Umma ko Deeja kagaya Mata,Aida ko visiting zamuna kawo maka ai,karatu bawasa bane" murmushi yayi,sai yaji Mummy tak'ara shiga ranshi,"ayi hakuri Mummy hakan baze sake faruwaba" "Tom Nagode,Ina fatan hakan" "nikeda godiya sosai" "karatun shekara nawane?" "3years" "saura 2years kenan?" "Eh insha'allah" "Dan Allah inason kamun wani alfarma,duk sanda kakeda time ka Kira Auta ko Deeja kazo Koh dinner kanayi damu" "insha'allah Nagode sosai Allah yak'ara lfy da tsawon kwana" "Ameen" bedroom Mummy tashiga ta turo Auta ta kawo Mai Abinci da ruwa,haka ko akayi Auta na zuwa suka gaisa,ta dinga Mai tamabayoyi kaman batasan da zancan Yana KADUNA tuntuni ba, Deeja ce tafito suka gaisa itama sama sama kaman ba ita tashirya komai ba,Abinci aka kawo Mai Tuwon alkama da miyan kubewa d'anya Wanda yaji busheshshen kifi da Naman rago,sai tacaccan ruwan abarbar Wanda ba'asa Mai komai aciki ba,Zama yayi abunshi suna Hira da Auta da Ayyan ga Young G ya makale Mai, yak'i rabuwa dashi,Dan tunda yashigo yasa Ayyan ya dauko Mai shi.....

*Mom Anwar Anya Young G bazai tonaba kuwa😂🤣?*

B'angaran Zulaihat kuwa tana d'aki takasa kunne duk abunda ake tanaji,duk saitaji Dadi Daman tasan Mummy bazata wulak'anta Shiba,ita Aunty Hannafiya takeji saikuma taga Bata cemata komaiba Koda tashigo canza Kaya....

ZEEYABDOOLWhere stories live. Discover now