*Zeey💞Abdool*
*(2021)*True life story*
*Love story*❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰🥰*
⚖️
*HAMDALA WRITIN'S ASSOCIATION💪*
_*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_
https://www.facebook.com/111403834371046*✨✨{{H.W.A}}✨✨*
*____________________**Page 47*
Shakuwa ce tashiga tsakanin Uncle G da Zulaihat,Amma fa Zulaihat na yin hakan nee saboda farincikin Mummy,Amma haryanzu Bata wani jinshi a Zuciyarta, Uncle G nee ya warke yasamu sauki sosai Dan Oga Zayyad yazo zasu koma P/Harcourt,Alh. Baba nee yace baze komaba sai ansa bikinshi da Zulaihat.....
"Ah Alh. Abari dai mukara shakuwa" "Oh kama samu tafara sonka salan sai wani yazo tak'ara canza Suna Koh?" "Hahaha,duk to yadda kukayi" haka Koh akayi akasa bikin Zulaihat da Uncle G 2 months,Dan saboda ma karatu tane da tuni anyi an wuce wurin tunda tuwona maina nee......
Tunda aka sanarwa Zulaihat ansa bikinta da Uncle G ta tsani kanta,Anya Tama Abdool adalci kuwa idan tayi Aure tabarshi? Me zaisa ma ta auri Uncle G?,no yakamata tacema Uncle G itafa ba sonshi take ba,tausayinshi take kawai....
Abunda Zulaihat batasani Duk maganan zucin datake Aunty Hannafiya Duk tajita,Mamakine yakama Aunty Hannafiya ta taba Zulaihat sannan tace "toh wlhy karma ki fito da Wannan zancan,Dan wlhy Mummy tariga ta buga Kati Dan lokaci ma yakure Miki,zancan Abdool ki Gaya Mai zakiyi Aure fakat" "ta yayata Zan iya Gaya Mai?" "Invitation card Zaki tura Mai ta WhatsApp" "sai ince Mai meye?" "Kar kice komai zai Gane" haka Koh akayi invitation ta turamai,Amma baya online, Zulaihat ta Dade a online taga Koh zai hau Amma Shuru,harma ta manta da zancan,Dan Abdool Saida ya kwana biyu kafin ya hau,dansun shiga DAJI.....
Yana zaune Akan sallaya yagama sallah ya dauki wayanshi ya kunna Data, message din Zulaihat nee yashigo Yana ganin sako daga gareta yayi saurin budewa,Yana budewa yaga invitation card nee,Saida Abdool ya karanta invitation card din abayyane yafi sau goma,Dan gani yake kaman a mafarki,idonshi nee yayi ja,sai hawaye Sha............
Saida yaci kuka yakoshi sannan yadauki waya yakirata, Zulaihat na zaune tana tunaninta datasaba Dan Yan gidansu nee keh murnan biki Banda ita,wayanta ne yadauki K'ara Koh dubawa batayi ba tasan Abdool nee,gaban tane yafadi dummmm,Saida yamata 5 missed calls sannan ta dauka tayi shuruuu...
"Assalamualaikum"shima shuru takasa cewa komai,magana yafara cikin muryan kuka da tausayi....
"To the light of my life that guide my way till eternity,to the brightness of my heart that shines through me. i try my best even when some said i wouldn't succeed, i might have get wat i want but u r alwayz wat i need, i feel soo tired but i can't sleep, m just stuck in reverse, my tears remain streaming down my face,i luv u sooo much n now it goes to waste, now i loose d one true luv i can never replace,Hmmmm could never be worse?your luv to me was the best medicine that was pure, i love you RAIHEEEERNA n i will never put anybody else above you, cuz their s no 1 in dis world dat can let know how much u really means 2 me, i m deeply in luv with u 2 it go, but those who never try will never know, i jst hope that d light dat guide my way n ignite my life will fix me one day......"
Yana Gama mafada ya kashe wayan Dan tunda yafara maganan take kuka shima kukan yake sosai kaman zai rasu,bazai iya jure kukanta ba shiyasa yakashe wayan, Aunty Rahela ce tazo har tazauna Zulaihat batasani ba Dan tsabagen kukan datakeyi...."Zulaihat waya mutu kike rusa Kuka haka?" "Abdool" "nashiga Uku meyasa mu Abdool din?" "Aunty Rahela nagaya Mai zanyi Aure,yanata kuka" "subhanallah,wayace kigaya Mai?" "Aunty Umma Dan tace gwamma ingaya Mai da Akan yaji a waje" "kumafa hakane,kiyi shuru kinji Allah Yana tare dashi,Kar ciwo yakamaki pls" lallashinta Aunty Rahela ta dungayi har ta hakura,Koda dare yayi Tama Abdool 3 missed calls Bai dagaba,ta damu hankalinta ya tashi Amma bazata iya nunawa ba saboda Mummy.......✍️✍️.
By Tooraee 🥰🥰🥰
*(GOLDEN PEN)*