*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story* ❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰🥰*
⚖️
*HAMDALA WRITER'S ASSOCIATION💪*
_*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_
https://www.facebook.com/111403834371046*✨✨{{H.W.A}}✨✨*
*Page 57*
......Zaune take a karkashin bishiya tana shakar iska Mai Dadi tareda ma young G Wasa,shiko Bawan Allah sai wangale Baki yake Yana dariya,Tun daga nesa ya hangota sai dayayi tsayuwar mintuna 10 Yana shawara da Zuciyarshi kafinnan yafara takawa zuwa wurinta,Koda ya Isa wurinta baiyi sallama ba dan duk a daburce yake,tsayawa yayi a kanta dan yarasa ta Ina zai fara, wani kamshin turarene da Ko a ina tajishi bazata taba manta Mai Shiba ya daki hancinta,shuru tayi tana nazarin turaran Amma sai ta kyaryata Zuciyarta akan amsar da tabata,jin kaman numfashin mutun a saman kanta yasa ta d'aga Kai dan taga waye? D'aga Kan dazatayi sai ihu,Dan saura kadan ta yarda young G badaban wannan mutumin ya cabe shiba.....
Mutuwar tsaye tayi tana mamaki aranta,duk ta daburce ta rude kamar wadda tayi gamo,shiko tsuramata Ido yayi Yana Kallonta,rasa mezai cemata yayi,sai ya Mik'a Mata young G ya juya yafara tafiya cikin natsuwa da Kamala,binshi tadingayi da Ido harya bace Mata,shiko tunda ya juya yafara tafiya Bai juyoba, murmushi kawai yake Dan koba komai yaganta,sai maimaitawa yake "Alhamdulillah",Itako kasa tashi tayi Dan tana cikin rudunani,tajima a zaune a wurin tana tunani sai Kuma ta tashi takama hanyar gida,Koda tadawo gida takasa sukuni,tarasa dawa zata tattauna wannan Zancen Dan wannan Zancen bazata iya tattaunashi da Aunty Hannafiya ba,Dan Aunty Hannafiya batada fahimta yanzu saita murda zance......
B'angaran wannan Bawan Allah kuwa Yana cikin farinciki da nishad'i Dan abunda ya Dade yake mararin son sake gani shine yasake gani a lokacin daya cire Tsammani, Zulaihat kuwa takasa sukuni Koh Abinci takasaci,sai tunani takeyi tarasa ya zatayi,gashi Kuma yamma tayi bare tace zata wurin Aunty Rahela,tana tsaka da tunani sai taji sallamar Deejah tashigo,takosa Deejah takaraso Amma Deejah tatsaya ma young G wasa a Palo,kasa hakuri tayi tafito tace Mata "Deejah kece?" "Eh wlhy nice,ya skull?" "Lfy Lau" "yanaganki wani iri" "lfy Lau,Amma inasan inganki pls" "Ok muje ciki toh" Dakinsu suka shiga ita da Deejah, Zulaihat hadda kulle kofa Dan Bata San kowa yaji,"menene Kuma na kulle kofa?" "Wlhy wani abune yafaru yau a skull Kuma banason y'angidan mu su sani" "meyafaru?" "Deejah gamo nayi" "gamo fah?" "Eh wlhy" "gamon me to" "wlhy Deejah Ina zaune a kasan bishiyannan danasaba Zama injiraki idan kinzo skull?" "Eh Ina ji" "Ina tsaka dama Young G wasa sainaji kaman mutun a saman kaina" sai kuma tayi shuru "ehen inajinki?" "kinsan d'aga kan dazanyi wanagani?" "A'ah sai kinfada" "Abdool nagani" ido Deejah tazaro tace "Abdool fa?" "Eh shi" "meyace Miki toh?" "Ai baimun maganaba,Kuma wannan yafi Abdool haske kadan,Kuma yadanyi kiba kadan,sai Kuma da Uniform din Airforce naganshi Amma overall ne irin na engineers dinnan dasuke sawa Navy Blue" "toh fa,Kuma kince baiyi Miki maganaba?" "Eh" "Kuma da uniform din Airforce?" "Eh" "To fa,aikwai alamar tambaya,Amma ba gamo kikayiba ki kwantar da hankalinki" "inba gamoba menen? Abdool fa Army nee shi,toh me yahada shi da Uniform din Airforce?" "Hakane kilan Mai Kama dashine" "Uhmmm shine har kamshin turaransu Daya?" "To shine bansani ba" bude kofan d'aki dasukaji nee yasa suka bar zancan suka koma wata Hira,suna tsaka da Hira sai sakon Abdool yashigo wayan Deejah kamar haka *Pls hau online muyi magana* murmushi Deejah tayi,Dan duk Labarin da Zulaihat tabata tana sane dashi,Dan itace ma ta tsarawa Abdool yadda zayi Kuma ta kawoshi skull din tanuna Mai inda take Zama intafito da lectures....
Deejah ce ta hau online suka Fara charting da Abdool....
*WhatsApp chart*
"Assalamualaikum""wa'alaikumuslam"
"Thank you dear,Naga kyakkawata ta K'ara kyau sosai" "Ayyah Babu damuwa,Amma tace baka Mata maganaba?" "Oh tabaki labarine?" "Eh wlhy duk ta rude wai tayi gamo" "lolx hakane Dan nima Naga rudewa a tattare da ita shiyasa ban Mata maganaba,Amma duk da haka naji Dadi sosai Allah ya biyaki da gidan aljanna" "Ameen amma haba saikace wani babban Abu" "Uhmm bazaki ganeba Deejah,yadda nakeson kyakkawata Ina ganin duk duniya Babu wani d'a namiji da zai iya matashi,Dan inasontane so nagaskiya Babu tantama,Koda ban Auri Rayhana ba,nasan banyi asara ba a fagen Soyayyah" "kadaina fadin haka insha'allah burina sai ya cika" "tayaya Deeja?" "Kaidai kacigaba da bani hadinkai insha'allah" "insha'allah toh Zan Baki Amma dakaman wuya?" "Bari nasauka tana mun magana" "Ok thank you bye" sauka tayi suka jigaba da maganan bayan fitan Aunty Hannafiya daga d'akin.......✍🏼✍🏼.*To fah kunji Deejah,Anya zata iya🤔🤔?*
By Tooraee 🥰🥰🥰
*(GOLDEN PEN)*
![](https://img.wattpad.com/cover/257143015-288-k141625.jpg)
YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Tiểu thuyết Lịch sửLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su