*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True Life Story*
*Love Story* ❤️❤️
*By Tooraee🥰🥰🥰*
*Page 59*
.......Binshi take da kallo dan ya dage yana lallashin Young G,dan gefe yayi ya barta a zauna,yanda yake abunne cikin natsuwa ya burgeta sai ta dauko wayanta tafara musu Video,abun yamata dadi,sai Murmushi take tace a hankali "Abdool komai naka mai kyaune" duk abunda takeyi baisani ba,dan yamaida hankalinshi sosai akan Young G,aiko Young G sai washe baki yakeyi yana dariya,haka Abdool yadinga mai har yafara yi kaman zaiyi bacci,Zuwa yayi yace tagoyashi,Zulaihat ido tazaro tace "ban dauko mai zanin goyoba" Murmushi kawai yayi yasashi akafad'a yana dan jijjigashi,duk abunda suke wata mata nagefe tana kallonsu,kwalla tashare tace "da miji nane saidai ya hauni da masifa,amma kalla murmushi kawai yayi yamata Uzuri" dan duk a tunaninta Mata da miji ne.....
*Uhmmm hakane fawoo,Ya Allah kabamu mazaje masu fahimta,Masu ma matansu Uzuri, Masu Aure Ya Allah kara basu kwanciyan hankali da fahimtar juna a tsakanin su🙏🙏*
Fita sukayi taga ya tsare keke napep,ga mamakinta taji ya kira sunan wurin cin abinci,ba musu tashiga dan tasan wurin,suna zuwa yasa aka kawo musu abinci daman yasan best food dinta,kasa sakin jiki tayi taci,shiko cin abunshi yake a natse kuma ga Young G a kafadanshi bai saukeshiba,shiko sai bacci yake abunshi,Zulaihat ce tace "kawoshi kahuta" "Nace miki nagajine?" Kai ta daga alamar a'ah,yana gama ci yatashi yabarta a wurin dayaga kaman tana jin kunya,yana fita tasaki jiki taci abunta dan daman kunya takeji,Tana gamawa fitowa tayi tasameshi a waje,Keke ya tsare mata yace tashiga ciki sannan yama mai keke kwatance yabiya kudin,sai ya mika mata Young G,juyawa yayi yafara tafiya,tunda kekesu yafara tafiya take waigenshi amma yak'i juyowa,tafiyanshi yake abunshi batare da ya waigo ba,bashi ya waigiba saida yasan sunyi nisa sosai sannan ya juyo,idonshi yayija sosai,tunani yake anya *Zulaihat zata karbeshi karo nabiyu?,shin zata kara yarda dazancanshi kamarda?* Hawayene ya zubo mai,samun wuri yayi ya zauna saida yaci kukanshi ma'ishi sannan yatashi yafara tafiya.....
Bangaran Zulaihat kuwa takosa ta isa gida ta kira Deeja,haka koh akayi tana zuwa gida ta ijiye Young G tunda haryanzu yana bacci ta ajiye jakanta tace musu "Ina zuwa" fita tayi direct gidansu Deeja,tana Zuwa Nana tagani tana karatu babu kowa a gidan "Nana" "lah *Zeey💞Abdool*" Murmushi tayi,dan ta dakatar dakowa akan wannan sunan amma takasa tsayarwa Nana,dan karamar yarinyace bazata iya mata bayani yadda zata fahimta kuma batareda ta tsani Abdool ba,shiyasa tabarta ahaka,dan koda ta auri Uncle G Nana batasoba,kuma tace bazata daina kiranta da ZeeyAbdool ba,koh agaban Uncle G haka take kiransa,"Wurin Aunty Deeja kikazo ko?" "Eh tana ciki ne" "no sunfita barka nan baya" "Oh bama nisa sukayiba kenan?" "Eh suna around" "yauwa my Nana y'an boko" kunyane yakamata tace "Uhmmm ni bansanma nafadaba" "karki damu kinji,inason mutun mai swag" "koh *ZeeyAbdool* ? ai kema kinada Swag" "Toh fa? Nikuma?" "Eh mana,hakama Mai kyauki,yanada swag shima,yana birgeni Sosai" "Koh?" "Eh mana,Kodai kina son Abdool ne My Nana?" "A'ah,bana sonshi" "kinason kice mun bazaki iya auranshi ba kenan?" "No, bazan aureshi ba" Shuru Zulaihat tayi batace komaiba,dan tasan Nana da surutu karta baro mata tambayar dabazata iya amsawaba,tana saka da wannan tunanin sai taji tace kaman daga sama "ZeeyAbdool?" "Na'am Nana?" "Kinsan wa nakeso ya aura?" "No sai kinfada?" "kyakkyawarshi" "wacece kuma kyakkyawarshi?" "Keh mana" Juyowa tayi tamaida hankalinta sosai akan Nana tace "Nana ai bazan iya auran Abdool ba saboda inada aure" "Cab,toh ba Uncle G yarasuba?" "Eh yarasu" "Toh ai malaminmu yace mana idan mijin mutun yarasu zai iya sake yin wani auran kuma idan sun rabu ma haka" Sallamarsu Deeja ne ya tsayar musu da maganan su "Ah harkun dawo?" "Eh wlhy,sannunku da dawowa" "Yauwa,ina Maigida ba cefane?" "Yana gida yana bacci" "ayyah ya alluran? Baidai yi kuka bako?" "Yayi amma dai an lalla...." Sai kuma ta tuna,"Uhmmm na lallasheshi sai yafara bacci" "Ayyah bawan Allah,Allah yatasheshi lfy" "Ameen" Deeja taganota amma saita basar,daki Deeja tayi sai Zulaihat tatashi tabita,"Deeja wurinki nazo" "Toh fa,gani" "Deeja yauma nasake ganin wani abun mamaki" "Toh fa,gamon kikasake yi?" "No ba gamo bane" Nan takwashe labarin abunda yafaru tabata babu ragi babu kari "Toh fa,Abdool fa kika ce?" "Eh shi" "kin tabbatar?" "Eh wlhy" "kodai maikama dashine?" "Ke wlhy shine,harfa ta'aziya yamun bana gaya miki ba?" "Eh hakane,amma ni bangama yadda ba" "karya kenan nake miki" "no ba kyarya kike munba,amma kinsan mezai faru?" "No saikin fada" "Zaki nadan biye mai kadan koh dan gaisawa kunayi kingane" "A'ah Deeja,gaisawa kum? Ni ban shirya wani soyayya bafa kuma" "ni nace miki kiyi soyayya ne yanzu?" "A'ah,ai bangane mekike nufi bane" "toh ai saiki bari in mutu kafin ki birnenni" "Toh gayamun yadda zanyi" "Yauwa Tawan,zakina biyemai ne saboda mugane Abdool dinne ko bashi bane,ai ke kinsan Abdool ko?" "Sosai ma" "ko Novel zaki iya rubutawa akan Halin Abdool" "Eh sosai ma" "Yauwa ahaka zamu gane Abdool ne koba Abdool ba,infa baka iya kama barawo ba sai barawo yakamaka" "Hakane kumafa,Tunda gashi a Kaduna kuma first ganinshi danayi da kayan Airforce ne ajikinshi" "Toh kingani" "kodai yakiraki da Kyakkwatane?" "A'ah da Mom G yakirani" "Toh kinga akwai aiki agabanmu,we have to be more careful" "yes wooo" "So don't Forget in yazo karki mai wulakanci,yadda zamu kamashi" "Insha'allah" "Dan banyarda Abdool bane" "Hakane gaskiya" "Bari nazo natafi gida kar Young G yafarka" "Ok toh muje in rakaki" "Toh muje" Fita sukayi atare, rajata har gida Tayi Suka cigaba da huransu......✍🏼✍🏼.
*Xuuby kinji Deeja koh? Wai Zulaihat zatama wayau,Anya kuwa Deeja?😄😅😂*
By Tooraee🥰🥰🥰.
*(GOLDEN PEN)*
YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Narrativa StoricaLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su