ZeeyAbdool 41

1 1 0
                                    

*Zeey💞Abdool*
        *(2021)*





*True life story*




*Love story* ❤️❤️







*By Tooraee 🥰🥰🥰*






Page 41







Zulaihat ce tazubo dawani hawaye Mai zafi daga idanunta...

Aunty Rahela ce tashigo tace..
"Subhanallah Zulaihat"

sai a lokacin Uncle G ya lurada Ashe tafarka,Dr Uncle G yafita Kira shine Aunty Rahela ta dagata....
"Sannu Koh?"
Kai tad'aga alamar Eh

"Kiyi hakuri Zulaihat,Amma Dan Allah kima Abdool uzuri baya Gaya Miki wannan maganan bane Dan ya ruguza miki Rayuwa,no yayi nee Dan neman  mafita,Ni nasani a duk inda Abdool yake yanzu nasan baya ciki farinciki"

Magana tafarayi a hankali"Aunty Rahela Abdool Shima baida lfy,Dan Dana kirashi Dazun wai yasuma wasu mutanene suka daga wayan"

"Innalillahi wa'ina ilaihirraji'un, Zulaihat ku yayyafawa zuciyar ku ruwan sayinfa,komai yayi farko zaiyi karshi,Kuma Ina Suleiman?"

"Nima bansani ba,Allah dai yasa Yana cikin koshin lfy?"
"Ameen"

Uncle G nee yashigo tareda Dr. Dr. Nee yadubata yace....
"Jikin Da sauki,Amma haryanzu da damuwa akanta"

Uncle G nee yakuramata Ido Yana Mata kallon
*Kece Kika ja*

Ita Kuma tana Mai kallon tambaya....
*Soyayyah Ashe tanada zafi?*

Kallon amsa yakuma Mata...
*Tamkar rijiya take acikinta Akwai zurfi,ciki nafada Ina bukartar taimako*

Dr. Nee yafita yabasu wuri, Uncle G binshi yayi abaya...
"Zulaihat kinji abunda Uncle G yaji Koh?"

"Wlhy naji,kilama alhakin shine yakamani"

"Shiyasa nakece Miki kibi komai a sannu Amma kinkiji"

"Aunty Rahela *SO NEE*"

"Nasan sone Amma ai hankali baya gushewa yayin yinsa Koh?"

"Eh Amma Ina tausayin kaina yadda Zan Fara rayuwa a matsayin Zulaihat ba Zeey💞Abdool ba"

Shuru Aunty Rahela tayi,tafara tunani  a zuciyar
*Da can ai Zulaihat kike?,aike Kika koma Zeey💞Abdool,Kuma in kinso Zaki iya komawa Zulaihat abunku*

Amma saitace Mata "lokacine kinji karki damu"

"Ok Amma dakaman wuya"

"Uhmmm,kidai yinta addu'a,Amma Zulaihat in tambayeki Mana?"
"Ina ji?"
"Kinji wayan da Uncle G yagamayi dazu?"
"Eh naji"
"Kodai shine yasa Naga kina Hawaye?"
"Cab,nifa Abdool Dina nake tunani,Wlhy bazan boye Miki ba,banjin son Uncle G Koh Daya azuciyana bare Kuma inyi kishinsa"
"Koh? Amma dai Kya tausaya Mai Koh Dan yadda yake nuna damuwanshi akanki"
"Eh gaskiya Yana kokari Babu laifi Kam,Amma nifa inason Abdool har yanzu"

"Amma dai wannan maganan kibarshi anan indai kinaso kushirya da Mummy,Dan Mummy fushi take dake"
"Eh nama hakura,Dan nasanma bazan taba samun Abdool ba,Amma kisani Abdool yariga yayi tsiro a zuciyata Wanda Ina tunanin Babu Wanda zai iya mayeshi"

Muryan Uncle G sukaji kaman daga sama yace....

"Haka dai kike gani,Amma insha'allah za'asamu Kuma kobayan ranshi zakiyi kewarshi Kuma kice dama yananan ki nuna Mai soyayyah da kauna but  by den is too late to cry baby girl"

Yana Gama fada yace "Saida safe Dan zanje in dauko Mummy in kawota Nan Dan bazan Kara shigowa ba,sai gobe insha'allah"

"Ah Mummy bazata Zo ba,danna nace Mata Zan kwana saboda Abban Ayyan baya gari,so Tama tura Auta taje ta dauko Ayyan a hannun Yan gidan mu"

ZEEYABDOOLWhere stories live. Discover now