ZeeyAbdool page 54

0 1 0
                                    

⚖️
*HAMDALA WRITIN'S ASSOCIATION💪*
        _*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_
https://www.facebook.com/111403834371046

             *✨✨{{H.W.A}}✨✨*
     https://chat.whatsapp.com/IfZVNIt6C9S8PvTV10v3wZ*Zeey💞Abdool*
     *(2021)*

*True life story*

*Love story ❤️❤️*

*By Tooraee 🥰🥰🥰*

*Page 54*


"Daman Zulaihat Zaki  damu haka idan Uncle G  ya rasu?" Juyowa tayi a razane tana kallon Aunty Hannafiya,sannan tace "Wlhy inason Uncle G,Dan Allah kuce ya dawo,bazan iya rayuwa babu shi ba fah?" "Ayau Kuma? Ai baze dawo ba, addu'a kawai yake buk'ata a Halin yanzu,Dan nasan Nan gaba kadan zaki manta dashi" "kema abunda unlce G yagayamun shi kike kara fadamun,nashiga Uku,ku fahimceni Dan Allah" "me yataba fada Miki?" "Sanda nace yasama young G Sunan Abdool yace *bazesaba saboda yasan Nan gaba kadan Zan manta dashi*, shiyasa yasama yaronshi sunanshi Dan A dinga tunawa dashi" "ai gaskiya nee?" Rungume Aunty Hannafiya tayi tana kuka tana cewa "wlhy bahaka bane bazan taba mantawa da Uncle G ba,Kuma Ina sonshi sosai,yazama Kama jinin jikina Daman can Dan uwanane,bakiji Yana cemun bloody ba?" Tausayintane yakama Aunty Hannafiya sai ta rungume ta tana Bata hakuri,"lokacin Uncle G yayi Dole yatafi,muma muna sonshi sosai babu yadda muka iya,Allah dai ya raya Mana Young G" "ameen" tun daga ranan Aunty Hannafiya tadena gayama Zulaihat magana Dan taga ta saduda,duk tayi laushi Aunty Rahela kullin sai tazo,yaune akayi Addu'an bakwan Uncle G,rayuwa Kenan shikenan Uncle G babu,kowa sai tausayawa young G yake,sai magana ake kaman yasan zai mutu shiyasa yasama yaronshi sunanshi,Allah sarki, Allah ya rayashi......Ameen.

Zulaihat na zaune ita da Kaka a tsakar gida tanaba young G nono tana Hawaye,Kaka na Bata Baki,Dan tunda akayi rasuwar Kaka tazo daga Kano Bata koma ba haryanzu,wayan Zulaihat nee ya dauki K'ara Amma har wajan 5 missed calls Amma bataji kiranba,abun ya daurewa Kaka Kai cikin mamaki tace "Zulaihatu bakiji wayanki na ruri bane?" "Wayana Koh Kaka?" "Eh" "banji ba" "dauka to kiduba Koh waye?" "Ya tsinke Kaka koma waye zai sake Kira" Kaka Bata matsaba Dan a Halin yanzu tausayi take Bata abun a lallabane ba abun a kure bane, Zulaihat ce ta Mike rungume da Young G a kirjinta Tama manta da wanyan ta shige d'aki,Kaka ce ta dauki wayan ta ajiye kusa da ita,ita Koh Zulaihat tana shiga d'aki young G tasa agaba tana kallon shi tana hawaye tana tuna sanda takeda cikinshi, *sun fita strolling da daddare itada Uncle G tanada tsohon cikin Young G,sai tace Mai "Uncle G nagaji" "kin gaji?" "Eh nagaji wlhy" "aikoh bloody Baki isaba,ke kikace a fito so sai mun Ƙarasa" yanayi Yanamata  dariya,ita Koh budan bakinta sai tace "in da Mai kyauna ne baze ce mun hakaba,goyani zaiyi" da mamakinshi ya juyo yace "waye Kuma Mai kyaunki?" "Abdool Mana" shuru yayi baice komaiba saiya duk'a yace "toh hau muje" Ƙin hawa tayi Yana binta Yana Bata hakuri amma TaƘi wai tayi fushi,sai dataga yafara zubar da Hawaye tukunna ta hakura,bayan ta hakura sai yace Mata "bloody wata Rana Zaki yabeni ko bayan Raina na sani" tabe Baki tayi irin Ina abun yabon yake anan* kuka ta fashe dashi tace "Dan Allah Uncle G kayafe mun,Dan Allah na rokeka" sai kuka shaaaa......
Kakace ta shigo rike da waya Yana Ringing Amma ganin halin datake Ciki yasa batayi saurin Bata wayan ba,ta zauna  A bakin gado tace, "Zulaihatu yanzu so kike ciwon zuciya yakamaki?" Kai ta girgiza alamar a'ah,"toh kiyi hakuri kinji,baze dawoba addu'a yake buk'ata a Halin yanzu ba wannan kukan banzan ba" "toh Kaka" hawayanta ta share saita Mik'a Mata wayan "ana kiranki"Kaka nabata ta fita,ajiye wayan tayi tak'ara lulawa duniyar tunanin Uncle G.......,wannan tunanin Kuma murmushi yasata Dan wannan Good moment nee *Abinci sukeci ita dashi,Sai ta dinga dauke Naman tana cinyewa,shikuma Yana cin abincin,shuru yayi Yana zuba Mata ido,Saura biyu ta dau Daya tak'ara Kai Baki sai yace "bloody Amma akwai nawa a tukunya Koh?" Bata bashi amsa ba Saida ta cinye na bakinta, "no shikenan" tana kokarin daukar wani,zunbur ya rike hannunta Amma ta dauke Naman, kokarin Kai bakinta take Amma ya cafke hannun,zura hannunta yayi cikin bakinshi Saida ya tabbatar ya siɗe hannun tukunna, "lah Uncle G kaida zaka dauki nama shine ka lashe mun hannu?" "Ai Danma karkice mun maye da hadda hannun Zan cinye" "Kama Isa?" "Harnayi yawa" Nan ta biye Mai suka dinga shashanci aka manta da cin Abinci*, murmushi kawai takeyi Dan wannan tunanin yasata nishadi,sake rungume Young G tayi ta sake  Lulawa tunani....

Autace tashigo tace "Mom G ana kiranki a waya" firgit tadawo daga duniyar tunanin Uncle G zata dauki wayan saiya tsinke,"kawo young G ƙilan asake Kira" "Ok gashi" auta na fita da Young G a hannu sai aka sake kiranta,daukowa tayi tak'ara a kunnenta,Muryan Daya daki kunnanta nee yasa hannunta yafara rawa tasaki wayan a k'asa.....✍🏽✍🏽.

*Ko waye wannan🤔? Oho🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️*

*Kubiyoni sannu a hankali,zakuji waye but I need more comments😇😇😇, love you ol my fans🥰😘*

By Tooraee 🥰🥰🥰.

*(GOLDEN PEN)*

ZEEYABDOOLWhere stories live. Discover now