*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story* ❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰🥰*
*Page 63*
.......Zulaihat na ganin Abu wasa wasa yazama gaske,Dan yazu takoma *ZeeyAbdool* a skull,ga Abdool ya dage sai musu new post yake,duk Friday in yazo,tun Bata yarda ayi da kyau harta koma biye Mai suna kashe zafafan hotuna,har yanzu yakai stage din anko suke duk Friday's Dan yin new post,duk duniya ta dauka da *ZeeyAbdool*,Dan dayawa daga cikin mutane sun dauka ma'auratane,Dan salon nasu Yana bada matuk'ar ma'ana,gakuma Young G sai sake shakuwa yake da Abdool,Dan yanzu Young G haryafa dabo,Dan yakusan 1 year,Dan fatama Abdool yake tafiyarshi yayi karfi kafin yacika 1 year ya hada Mai birthday.......
Zulaihat ce zaune akan gado tana kallon hotunan su da Abdool ke saki a duniya,su Auta nee suka shigo tare da Deeja da Nana,zura Mata ido sukayi Dan batama San sun shigo ba, Young G Kuma yabi Mummy biki Dan yau Saturday.......
Nana ce ta Dan ta bata sannan tace "ZeeyAbdool" dago idanuwanta tayi ta tsuramata su "Uhmmm salon Soyayyar ku tana burgeni" Ware idon tayi sannan tace "kamar ya Nana?" "Kamar yadda yake canza salo" "salo Kuma Auta?" "Eh Mana,dafa Soyayyar ku iya family ta tsaya,yanzu kuwa duk duniya ta dauka,kowa zancan Soyayyar ku yake,gashi kullun sai K'ara yawan fans kuke" Deejah ce takarbe da "Uhmmm Ni bama wannan ba,randa duniya zata San keda Abdool ba ma'aurata bane" "kamarya?"
"Lallai ma Zulaihat,toh bari kiji,duk wannan posted din da kukayi da Young G babu Wanda zaice ba family bane,Dan kowa gani yake Mata da mijine da dansu" "ya keyi dai zakice Ni bansashi bafa" "bakisashi bafa? Toh ai duniya batasan shi kadai yakeyi ba,Dan sunan page din *ZeeyAbdool* ba *Abdoolsamad* ba" "toh yazanyi?" "Mafita kike so?" "Eh" Deeja ce ta tsunguli Nana sai crab Nana tafara magana.........."In Baki shawara?" "Inaji Nana?" "Dan Allah kiba Uncle Abdool dama for d second time" "Dama Kuma?" "Yes Zulaihat" "hardake Deeja" "nima am in support" "no no Auta,Ni bazan iya ba" "ZeeyAbdool idan kikace no,ya Abdool zaiji?Kuma mekike son yagayawa duniya?cewa ke ba matarshi bace,Koh Young G ba danshi bane?" "Ni bance zan kyaryatashi ba" "toh idan bahaka bane menene?" "Deejah ki fahimce ni" "wace irin fahimta zan Miki Zulaihat, Zuciyarki na son Abdool,kawai kinason kyaryatata ne,Amma Koh a idonki ga sonshinan aciki ,Kuma Ina da tabbacin idan Kika Auri Abdool bazakiyi ladamaba" Ido ta zaro tace "Aure?" "Aure Mana,inba aure ba menene?so kike kuyita new post Amma babu promotion?" "Hakane Aunty Deejah,Dan Allah ZeeyAbdool ki duba lamarin Abdool pls and pls",suna Gamawa suka Kama hanyar fita,Dan ran Deeja yagama b'aci........
Tunda Su Nana suka fita Zulaihat keta nazarin maganganinsu,ta k'asa cin Abinci gashi sai tunani takeyi,Koda Mummy tadawo sannu dazuwa Tamata takoma ciki,Koda dare yayi kasa bacci tayi tana nazarin maganganin su,gashi Kuma Young G ya shaku da Abdool Dan kallon baba yake Mai a Halin yanzu..........
Wasa wasa yadda Zulaihat taga Rana haka taga dare,don a gaskiya tason Abdool Amma idan ta Auri Abdool Tama Uncle G adalci kuwa?,kanta ta girgiza tafara rusa kuwa tana sumbatu "wayyo mutuwa,ya Allah ka jikan Uncle G,narasa ka,nasan bazaka dawo ba" haka ta kwana kuka har asuba,idonta duk yayi luhuhu saboda kuka da bacci,bayan tayi sallah ne bacci ya dauketa,ba ita tashiba sai 1pm,Koda tafarka wanka tayi tafita zuwa wurin Deeja.......
Samunta tayi zaune a tsakar gida tana yankewa Nana kumba,Dakinsu Deeja tawuce direct, Deeja ce ta bita abaya Dan tasan akwai magana......
"Lfy Zulaihat naganki haka?" "Hmmmm zancan jiyannan ne" "eh Ina jinki?" "Gaskiya zancan Abdool abarshi,Dan idan na Auri Abdool banma Uncle G adalci ba,Kuma Uncle G yamun Baki,idan na Auri Abdool, Koh Sau d'ayane saina yabeshi" "Baki Kuma? A auren naki dashi kinmai wulak'anci ne?" "No" "and den what? Kedai kice bazaki Auri Abdool ba Amma baruwan bawan Allah Uncle G,Allah yajikanshi da Rahma,kekuma Allah yasa hakan shiyafi Miki alheri"Zulaihat ce tafita cikin fushi hakama Deejah Dan bawanda yabi takan kowa........
Abu kaman wasa yazama babba,Dan Deeja ta dauki fushi da Zulaihat,Dan Koh calls dinta ta daina dauka,Bata zuwa gidansu ba runta da Zulaihat,Koh haduwa basayi Dan yanzu ma Deeja tanayin internship dinta a 44 hospital batama da time,gashi kamu da Soyayyar wani hadaddan Dr. a 44 hospital ana cemai *Dr. Yaseer* soja ne shi,shi kadai mamarshi ta Haifa,gashi iyayanshi Mayan mutanene Dan mamanshi ma lecturer ce,abbanshi Kuma baban mutunne,Dan yanada Hannun jari Mai karfi a *Oando* Kuma fitaccan mutunne,gashi iyayanshi naji dashi sosai,itama Deeja suna sonta,Dan duk abunda Dr. Yaseer yakeso Suma iyayan suna so,duk wannan budirin Zulaihat batada labari,Dan yanzu sunkai 3 months basuga junaba,Dan sahun Zulaihat Uku gidansu Deeja Amma batanan,dan Deeja Bata dawowa da wuri saboda Dr yaseer ne yake dawo da ita.......
Abun duniya ya ishi Zulaihat,Dan Deeja ta kulle duk kofar dazasu hadu da ita,abun yana damunsu duka,Dan Deeja nason tabata labarin Dr yaseer Amma ta danne Dan cimma burinta, Zulaihat ce taje tasamu Mummy akan batunta da Deejah,Dan Mummy tayi magana tayi magana sunce babu komai,shiyasa tazuba musu Ido,dakin Mummy tashiga sukayi magana,banji Mai Mummy tace mataba Amma naji tana cema Mummy "toh Mummy Nagode,bari naje wurinta toh" "Ok saikin dawo"........ ✍🏼✍🏼.
*Toh Fans,kuna tunanin Zulaihat taba Mummy labarin fadan sune?in kuma tabata,wanne shawara kuke tunanin Mummy zata Bata,dan dai kunasan kudirin Deeja nayin gaba........🤣*
By Tooraee 🥰🥰🥰.
*(GOLDEN PEN)*
YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Ficțiune istoricăLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su