ZeeyAbdool page 53

0 1 0
                                    

*Zeey💞Abdool*

💫
*Great Writer's Association*✍🏻

*_Motto great writing is remembering details. Most people want to forget. Don't forget things that were painful and or embarrassing or silly.turn them into the story that tells truth.💪_*
https://m.facebook.com/Great-Writers-Association-101245632167814/

           *📚(G.W.A)✏️*

        

*True life story*

*Love story*

*By Tooraee 🥰🥰🥰*

*Alhamdulillah,Zan Mika godiya ga Allah Daya nuna Mana farkon Ramadan da karshensa lfy,dafatan kunyi sallah lfy?Allah yasa hakan Ameen🙏🏼🙏🏼🙏🏼,Barka da Sallah to ol my fans❤️💚🤍*

*Page 53*

......"Gaskiya abun tausayi nee" Zooming dinshi Zulaihat tayi tanacewa "Yadda suka daukeshi ma tayaya Y'an uwanshi sugane......" Bata k'arasa magana ba kawai saita saki wayan a k'asa,ta saki wani k'ara tare da ihu...

"Nashiga Ukuna,kiduba mun pls Aunty Umma kice mun karyane abunda idona yake gane mun" wayan Aunty Umma ta Duka ta dauka ta duba me Zulaihat
Tagani?,salati Aunty Hannafiya tayi tace "Innalillahi wa'ina ilaihirraji'un,Mun shiga Uku Zulaihat,Mu kira Gida muji pls" kuka Zulaihat takeyi Dan a lokacin ma batajin abunda Aunty Hannafiya ke fada,wayanta Aunty Hannafiya ta dauka ta Kira ya imran,Amma Yana ganin call dinta yaki dauka,Dan baisan mezai Gaya mataba,Saida tamai missed call 10 Amma yak'i ya dauka,dabara nee yazo Mata sai takira Oga Zayyad ta fita,itama Aunty Hannafiya kuka take Amma ta daure,Dan yanzu Zulaihat ma a Halin yanzu Bata iya ganin gabanta,tashi tayi Jiri na dibarta tabi bayan Aunty Umma,kafin ta k'arasa inda take taji tane cewa"Uncle G aka kashe a hanyar Abuja" luuuuu Zulaihat tafadi dataji wannan Zancen, K'aran faduwar ta Taji,juyawar dazatayi kawai sataga Zulaihat ce,"innalillahi wa'ina ilaihirraji'un,nashiga Uku Zulaihat" kashe wayan tayi tazo ta d'agata sannan ta yayyafamata ruwa Amma Tak'i tashi, Aunty Hannafiya tashiga tashin hakali,ga tashin hakalin da suke ciki ga Zulaihat a sume,Oga Zayyad nee yazo cikin hanzari ga Kuma tashin hankali a idonshi ya taimaka aka kaita Asibiti, Aunty Hannafiya ce goye da young Gee Wanda Koh 3 months baiyi ba, tausayinshi yakamata saita fashe dakuka,"yanzu mugayan mutananan sun maida mun kai maraya?Ya Allah kasa Bai mutu ba?" Oga Zayyad nee yazo Aunty Hannafiya ke tambayarshi ya akayi aka kasheshi?"According to report din dayazo Mana,Wai yataho da motanshi daga Gida,Dan daga Nan P/Harcourt angaya Mai Zai K'ara komawa Abuja Nan da 3weeks, shiyasa ya taho da motanshi Akan Zai barta a Abuja kinsan Abuja,inbaka da mota zirga zirga sai a hankali,shine yana cikin tafiya yasa inner wear din sojoji a jikinshi,ya hadu da Kidnappers Suna tsaidashi yaki tsayawa shine suka budemai wuta inagaya Miki" Duk wannan Labarin da Oga Zayyad ke badashi Zulaihat naji Dan tafarka Amma takasa magana,hawayene yake zubo Mata,Kuka takeyi kaman ranta zai fita, Aunty Hannafiya ce tace "Uncle G dama katsaya wlhy" "bayadda muka iya Aunty Umma,sai hakuri lokacine yayi" "hakane Gaskiya,yanzu ance Gobe by 10:00am za'ayi jana'izarshi a Kaduna insha'allah,so Gobe akwai Jirgin da zamuje Jana'izarshi da sojoji daganan so da sassafe zamu tafi insha'allah" "hadda mu?" "Hadda ku insha'allah,Allah ya jikan Oga Garzali" "ameen"

Zulaihat da Aunty Hannafiya kwana sukayi Suna kuka,Dan a Asibiti suka kwana washegari da sassafe Suka Kama hanyar Zuwa KADUNA,batare da Bata wani lokaciba suka Isa Dan flight sukabi,Suna Isa garin kaduna a Gidan Alh. Baba suka sauka gida acike makil kowa sai kuka yake Yana tausayin Zulaihat da Dan nata,kowa jiran shigowarsu yake Dan anriga anmai wanka Daman su ake jira,Hajiyar Uncle G kuwa bawanda yagaya Mata Dan ba'asan halin dazata shigaba, Zulaihat nashiga Gidan ita da Aunty Hannafiya,Young G na hannun Aunty Hannafiya, Zulaihat ce taje da gudu ta rungume Mummy tana kuka,"Mummy Wai dagaske Uncle G an kasheshi?" Mummy kasa Bata amsa tayi sakamakon kukan Daya kufcemata, rungume Juna sukayi sunata kuka,dakyar aka dagata akace taje taga gawanshi kafin atafi dashi,tana shiga Koh tsoro batajiba ta kwanta a Jikin gawarshi tana sumbatu tana jijjigashi "Uncle G katashi,wlhy inasonka,wlhy nafisonka Akan Abdool,Dan Allah katashi innuna maka irin son danake maka,I love you Uncle G" Aunty Raliya ce ta dagota suka fita da ita ita da Aunty Rahela,Dan sunga tana neman zaucewa,Suna fita da Zulaihat aka dauko gawan Uncle G za'a wuce dashi makoncinshi, Zulaihat naganin za'a tafi dashi ta Fadi luuuuuu akasa sai sumaaa....

Dagudu mutane sukayi kanta Suna yayyafamata ruwa dakyar ta tashi Amma takasa magana sai hawaye kawai takeyi tana sake sake a Zuciyarta,hakuri aketa Bata anamata sannu Amma duk ba jinsu takeba Dan a yanzu muryan Uncle G kawai takeda bukatan ji.....

Aunty Umma ce da gwaggo take Bata Labarin yadda abun yafaru,"gwaggo ba'a motan haya yakoma ba?" "A'ah damotanshi ya koma,Dan yace Nanda sati 3 zai dawo yacigaba da abunda yakawoshi,zaikai wannan report dinne den saiya dawo,shine yace zai tafida motarshi ya ajiye a Abuja wurin wani abokinshi Dan yace zirga zirga a Abuja bakada abun hawa Babu Dadi,badason Alh. Baba yatafi da motan ba,Amma dayakawo wannan uzurin nashi sai yadda yabarshi yatafi" "hakama Oga Zayyad yagamun,eh baigamana yadda yafaru ba?" "Eh yadda Labari yazo,cewa akayi Yana tsaka da tafiya nee a cikin mota kidnappers suka tsaidashi Amma yaki tsayawa,suka budemai wuta,harbi biyar a jikinshi,biyu a Ciki Daya a Kai sai biyu a kirji,sai Kuma motar duk sun bubbulata da bullets babu kyan gani" "nashiga Uku gwaggo,haka sukama Uncle G? Ya Allah, Uncle G Meyasa baka tsayaba? Meyasa ka gudu? Da katsaya da kudi kawai zasu nema,Wlhy muna sonka sosai" sai tafashe da kuka,tana rungume da Young G, young G dai sai Ware Ido yake yana kalle kalle,Bai san meke faruwa ba.....

*Allah sarki rayuwa,mutuwa kenan,babu ruwanta , in lokaci yayi Dole katafi,Ya Allah kasa mutafi a sa'a ameen*

Mutuwar Uncle G ya girgiza kuwa a family dinnan harda iyayan mariganya Dr. Zulaihat,sunyi kuka sosai Dan bak'aramin taimako yake musu ba,Dan Uncle G mutunne Mai shiga Rai,bashida abokin fada kowa nasane,baya fushi kullun fuskanshi cikin fara'a yake,Yara da manya sai kuka suke Dan anyi babban Rashi, Zulaihat kuwa zazzabi nee yakamata Mai karfi Dan tun dataga an dawo daga birne Uncle G ta cire Rai dashi,tashiga ciwo da kewarshi,salati kawai takeyi a Zuciyarta Dan Bata ma San Meke Mata dad'i ba, Mummy ce ta dauketa suka koma gida Dan yamma tayi,Koda suka koma gida haka ake zuwa musu Gaisuwa Amma Zulaihat ba uhmmm ba ummummm Dan Bata da aiki yanzu sai zubar da Hawaye,daga ta kalli young G sai kuka,babu abunda yake d'aga Mata hankali in tatuna maganan Uncle G *karki damu my bloody,kwana nawane Zan tafi in barki da Abdool dinki?* Habawa sai kuka tana sunbatu "Wlhy na fisonka akan Abdool,kadawo gareni zakaga irin son danake maka,ai nagaya maka in kadawo Zan nuna maka kauna,yakamun haka Uncle G?" sai kuka, Aunty Hannafiya ce take kallonta tana mamaki,wanni lokacin tabata tausayi wani lokacin ta Bata haushi "Daman Zulaihat Zaki damu haka idan Uncle G yarasu?" Juyowa tayi a razane tana kallon Aunty Hannafiya....✍🏽✍🏽.

*Toh fah,kunji maganar Aunty Hannafiya,Anya da gaskiya take fada kuwa?*

By Tooraee 🥰🥰🥰.

*(GOLDEN PEN)*

ZEEYABDOOLWhere stories live. Discover now