*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story*❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰🥰*
Page 39
*Wannan page din nakune Zeey💞 Abdool,Dan Danku nake wannan Novel din, can't love you less❣️❣️❣️❣️❣️❣️*
Wannan shine abunda nake son sanar muku,and again yau ake Suna Daughter na data Haifa mu........"
Juyawar dazanyi kawai Dan Inga halin da Zeey💔Abdool ke ciki......
Ashe tunda Abdool yafara magana Zufa ke keto Mata,duk da akwai fan adakin Kuma ta saitinta yake,Duk tajike saboda zufa,idonta yayi ja sosai takasa gasgata wannan maganan.....
*Anya ba mafarki nakeyi ba😳?*
Hannunta tadauka ta murza idonta dan ta tabbatar anya ba bacci takeyi ba?,Amma habawa saitaga fa zahiri nee......
Zuciyarta nee yafara Mata zafi,batasan mezatace ba?shikoh Abdool Koh da yagama magana Bai iya dago idonshi ba,Dan jira yake yaji Mai Mummy zatace.....
Aunty Hannafiya Koh Ta Suma a zaune,Dan itama batayi expecting din wannan zancan ba.....
*Abdool nada aure Kuma da Yarinya😨😨😰,Kuma yau ake suna😳,tabdijam*
B'angaran Aunty Rahela kuwa,takasa motsawa Dan wannan Lamari ya lalace sosai.....
Aunty Nafeesa ce tace.....
"Toh Hajiya kinji abunda yace"
Mummy Daman tunda yafara maganan take murmushi,batace komai ba....
Abdool yayi shuru Yana jiran Mai Mummy zatace,ga mamakinshi sai yaji tace....
"Toh Nafeesa Ai Babu komai,ai Kama kyauta daka fada Allah ya zabamana abunda yafi Alheri🤲"
Suleiman Koh duk a tsure yake,sai zazzare ido yakeyi kamar wani Mara gaskiya👀......
*Allah sarki bawan Allah,kamayi kokari wlhy*
Abdool nee yayishuru baice komaiba dayaji abunda Mummy tafada, k'asa daga idonshi yayi,mikewa yayi cikin kasala da rashin karfi yatashi zaifita Daga Palon.....
Suleiman nee yarigashi fita,shikoh yayin dayazo fita baigani da kyau Dan yafara ganin bibbibiyu Dan idonshi ya cika da kwalla🥺,yazo fita takofa ya bige kafadanshi da kofan dakinsu Zeey💔Abdool....
Gashi kuma kofan na karfene irin Mai karfinnan,aikoh ya bugu sosai Dan Saida Zeey💔Abdool ta d'ago ta kalli bayanshi Amma shi Koh a jikinshi,Yana fita Aunty Rahela tabi bayansu Dan yau Zeey💔Abdool ba zancan rakiya....
Mummy nee tajuya ta kalleta taga halin datake ciki,Dan har Zulaihat ta kwance daurin da akamata,Dan jin daurin take a halinyanzu kaman an dauramata gida.....
Mummy nee da Aunty Nafeesa suka shiga d'aki Dan su tattauna,suna shiga Aunty Hannafiya tazo kusa da Zeey💔Abdool....
"Zeey💔Abdool kiyi hakuri kinji,haka Rayuwa take"
"Nifa banyarda Abdool yayi aure ba?"
"Baki yardaba gashi yafada da bakinshi"
"Uhmmm Wai hadda yarinya 😰?"
YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Historical FictionLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su