*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story*❤️❤️
*By Tooraee*🥰🥰🥰
Page 4
*My pride Allah ya karamiki lfy da tsawon kwana,wannan page din nakine my An💝neem........ I love u Momma❣️❣️❣️.*
"Eh na tuna,Amma Baki gayamun ida kuka hadu ba?"
"Wlhy Aunty Nafeesa ce tahada mu"
"Dan Allah,Dan uwanta ne?"
"A'ah a Facebook yaga tasa hotona Wanda Nayi da kayan India Nan dakika kasa ganeni?"
"Eh na tuna"
"Shine a Profile pic dinta a Facebook,shine ya dameta Dan Allah tahada mu,shine ta hadamu"
"Daman tasanshi ne?"
"A'ah just friend dinta nee na Facebook,Kuma sun Saba gaskiya"
"Ayyah kinji abun Allah,Allah ya tabbatar ta Alheri"
"Ameen"
Aikoh Nan take tasaki jikinta a makaranta,har tasamu tayi karatu dan kafin break time batama San me ake koyawar ba,lokacin break nee suka tattauna da Deeja.......
Abufa wasa wasa yau 2 weeks kenan da tafiyar su Abdool,Dan ba Zulaihat kadai ba hatta Mummy dabata damu dashi bama tadan damu,saboda taji a News ana neman sojoji dasuka fita Operation Guda 20........
Dabara Tama Zulaihat.......
"Zulaihat?"
"Na'am Mummy"
"Menene cikakken sunan Abdool?"
" *Abdoolsamad Abdulaziz* "
"Masha Allah,Aikoh baya cikin sojojin da ake nema,Dan banji sunanshi ba"
Aunty Umma ne ta kalli Mummy🙄, Mummy ce ta Harare ta😏......
"Mummy dagaske?"
"Eh Zulaihat ki kwantar da hankalinki kinji?"
"Insha'allah"
Tashi tayi tana murmushi☺️,bayan tabar wurinne Aunty Umma tace....
"Mummy dafa sunanshi aciki,Kuma kikace Babu?"
"Haba Umma maiyasa bakida tunanine,bakiga halin datake ciki bane?yakamata A tausaya mata"
"Hakane Kuma fa"
"Toh kingani"......
Su Abdool sun Zama Abun Tausayi a DAJI,Dan duk sun zubar da wayoyin su saboda tashin hankali,Koh Goran ruwansu ma bakowa bane yake rike danashi,da shatima sai Abdool sukeda Goran ruwa,suna cikin tafiya ne suka hadu da wani bala'i dayafi na Boko Haram........
Dan dukkansu Saida sukayi danasanin shiga aikin Soja Amma Banda Abdool......
Wasu Dabbobine Masu fuffuke suka biyosu,Gasu tsalle Sukeyi....
Kuma wani Tashin hankalin basajin harbi Dan idan kaharbesu fuffuken su ke k'ara budewa,gashi tsallen su yafi gudu su Abdool,kuma suna yin tsalle zasu Kama mutun su yaga shi biyu,Su Caccakeshi shikenan ya mutu,Kuma ba cin mutun din suke ba.......
Hankalin kowa yatashi,Dan sun Kama wani Oga jecob sun yaga,yanzu su 9 suka rage........
Abdool yaga gudu fa bazaiyi ba,gashi Tubabbe yayi sharkaff da fitsari ajikinshi,Shatima Kuma kuka yakeyi Yana Kiran sunan Abdool😭😭 kaman wani yaro,Yanzu Abdool yakoma kaman Ubansu,kowa saishi yake kira.....
"Abdool shikenan mun mutu gasunan zuwa wlhy🙆🏾♂️🙆🏾♂️🙆🏾♂️"
"Munshiga Uku,wayyo babana😭😭"
Shima Abdool hankinshi yatashi sosai,Dan bashida wani Option yanzu,Dan ga tashin hankali Nan Shima Kara a idonshi....
Amma sai yayi tamaza....
"Shatima muyi sujjada muyi kalmar shahada kawai mun mutu,Dan bani dawani dabara Yanzu....."
"Yanzu haka zamu mutu munaji muna gani 😭?"
Tsawa Abdool ya daga musu,Dan bayason su mutu batare da kamar shahada ba,tunda ba harbesu akayi ba.........
"Kayi sujjada my friend suna zuwa,kayi kallamar shahada,shikenan karshan mu tazo....."
Haka Koh sukayi sukafara Addu'oin,musulmai suna kiransunan Allah kamar yadda Abdool yagaya musu, Christian suna kiransunan Jesus........
Abdool Kam kabbara yayi, yafara kalmar shahada a bayyane,duk abunda yayi shi Tubabbe yakeyi yana shashshekar kuka,Dan Abdool ne kawai baya kuka a Halin yanzu.....
Dan suna jiyo kukan Dabbobin suna tsalle zuwa wurinsu.........✍️✍️.
*Love you ol my Fan*💖💖💖
By Tooraee🥰🥰🥰
*(GOLDEN PEN)*
YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Historical FictionLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su