ZeeyAbdool page 68

2 1 0
                                    

*Zeey💞Abdool*
        *(2021)*

*True life story*

*Love story* ❤️❤️

*By Tooraee 🥰🥰🥰*

*Page 68*


Deejah ce tazo ta dafata......
"Haba *Zeey💞Abdool* kinsan yanzu haka dakike kukannan Abdool yanaji ajikinshi?"
Hadiye kukan tayi,Dan tasan idan tana cikin damuwa Abdool nasani, Dr. Sameer nee yace musu "kuzo muje Koh?" Bin bayan Deejah tayi batare datayi maganaba,Koh da Suka shiga mota batace komaiba Dan hakalinta ma Yana Kan waya tanama Abdool typing message........

'Rayhan I miss you a little,A little too much,A little too often and a little more'

Yana cikin dannan wayanshi a mota sakonta yashigo, murmushi yayi sannan yafara typing kamar haka.....

' Miss u more than u do, longer than time can tell.....
As u r far from me now.....
Each moment my heart awaits ur love..!
So kyakkyawata,hold me tight in ur arms....
Let me feel d warmth of love....
Wen I feel like breaking down....
Kiss me and Give me a warm Hug....!
Hmmmm *Zeey💞Abdool* Someday Our life will be like a fairy tale....
Someday we wud b together....!
And then you'll stop hurting ur self.....
Coz I'll be dere to catch wen u fall...,and pls don't carry again🙏🙏🙏🙏'

Sakon na shigowa tashiga tana karantawa,tana jin kunyar wani wuri a ciki,Saida tazo karshe sai mamaki yakamata,badai Abdool yasan tayi Kuka ba,kawai saita tsinci Kanta cikin nishadi,tana sake karanta text message din tana Jin nishadi......

Kukan Young G nee ya dawo da ita daga tunanin datakeyi, waige waige yakeyi baiga Abdool ba,Aiko saya Kara sautin kukanshi Yana cewa.....

"Daddy, Daddy" rungumeshi tayi tana lallashinshi,Saida yayi shuru tukuna sai Dr. Sameer yace....

"Zuwa anjima inya sauka sai kuyi video call yaganshi kinji" Kai tadaga Mai alamar 'eh' Dan idan tace zatayi magana kuka zaizo Mata,Kuma gashi Abdool ya sake rokonta......

Haka suka kaisu gida daga ita har Young G basa cikin walwala,Koda suka koma gida barinshi tayi a wurin Nana da Auta,Dan Nana tazo wurin Auta suna Hira........

Shiga daki tayi ta kwanta akan gado tana ta tunani,sakone ya shigo wayanta,Ashe tabar Data a kunne,hotunan da Deejah ta musu ne Deejah ta turo Mata,aikoh budesu ta hauyi tana kallo yadda sukayi masifar kyau sosai,page dinsu ta hau tafara posting,Hade da short message......

'I miss you more than d sun misses d sky at night'

Habawa ai sai comments,iri iri kowa Sai fatan alheri akema Abdool,duk abunda Zulaihat tayi Abdool na gani,sai mamaki yake......

*Daman haka Suke da Fans,kowa sai Allah ya dawodashi lfy,da fatan Allah ya barsu tare*......

Alhamdulillah Abdool ya Isa Gombe lfy,Yana sauka Kiran Zulaihat na shigowa,Dan Daman tun a hanya yasha Kira minti minti, murmushi yay sannan yabari ya katse sannan ya kirata......

Kukan Young G nee ya daki kunnanshi,a hankali yace "Mai ya samu Moi son?" "Wai Daddy" "samai wayan a kunne" habawa kaman Young G jira yake,yanajin muryan Abdool Yana Mai magana sai dariya,abun Yama Abdool Dad'i,ai koh ya biye Mai dukda a gajiye yake,wakan dayake reramai nee yashiga yimai,sai dariya yake sosai,don cikin harshen larabci yake rera wakan,Dan Koh magana ya kemai da larabci yake ma Young G,haka suka shagala,harsaida ya tabbatar Young G ya gamsu sannan sukayi sallama,Shima har Umar yazo daukanshi da motan gidansu,shiga yayi suka Kama hanyar gida.......

Umman Abdool ta kosa Dan nata ya iso,sai murna take Dan cike take da labarai kala kala,datasan zaisa Dan nata farinciki,ai Koh sun Jin Karan shigowan motan Umar sai murna,Dan yasha tarba,kowa ya zagayeshi sai labari ake bashi kala kala, Murmushi yayi Yana kallon Yan uwan nashi, bak'aramin Dadi yajiba Daya gansu tare gabad'aya............

Bayan Abdool yayi wanka yaci Abinci yayi sallah,dakinshi ya shiga ya kwanta Dan ya huta,Yana jiran ayi isha'i yanayin sallah zai kwanta abunshi,Saida safe zai fito suyi Hira da Yan uwanshi,haka Koh akayi Yana idar da sallah sai bacci,Koda Zulaihat takira ba dauka ba,itama Bata damuba Dan tasan ya gaji yanada buk'atan hutu.......

*Washegari*

Bayan Abdool yagama breakfast yaje part din babanshi Dan yamai barka da safe,anan ya tadda ummansa suna magana,bayan ya gaishesu cike da kulawa suka amsa sannan Babanshi ya daura da......
"Kazo akan gaba,Dan muna tattaunawane Akan zancan auranka,kasanar Mata Nanda sati biyu za'azo neman auranka" Murmushi Abdool yayi sannan ya kalli ummanshi,itama murmushi tayi sannan tace "Masha Allah,ai Haka akeso,Allah ya kaimu" *Ameen*,Hira sukayi sosai dangane da shirye shiryen zuwa KADUNA neman auren Zulaihat,da nasihohi da babanshi yamai Akan Zama da Mata biyu ba mace Daya bane,yakamata yazama adali,Mai kula,natsuwa Dan gujewa shiga hakkin wata..........

Bayan Abdool yadawo part dinshi nee,yakira Zulaihat yanamata Abishir......

"Alhamdulillah,Allah na gode maka daka nunamun wannan ranan da Mai kyauna zai turo gidanmu Akan zancen auren mu"
"Uhmmmm,sai kace ance Miki an daura?" "Ai ankusa,tunda gashi za'a turu" "insha'allah za'a daura kinji,yauwa kyakkyawata in tambayeki Mana?" "Inaji?" "Mekika tanadan Mana Akan zamantakewar auran mu?" Shuru tayi takasa magana,dakyarshe ma kashe wayantayi,Dan wani kunyane ya lullubate,sai Kuma ta hau murna hade da tsale abunta,Dan ita kadai ce a gidan.........✍🏽✍🏽.

*Toh fah Zeey💞 Abdool fans,baba ya yarda,sai ahadama Mana walima🥣🥣🥣🥣😁💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼*

By Tooraee 🥰🥰🥰.

*(GOLDEN PEN)*

ZEEYABDOOLWhere stories live. Discover now