*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story* ❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰🥰*
Page 43
Shuru Zeey💞Abdool tayi Dan tasan halin Aunty Hannafiyan batada kirki wani sa'in,kukanta Tasha tagodewa Allah sannan har tamike zata shiga d'aki saiga Kiran Abdool.....
Saida yamata missed call kafinnan dayasake Kira saita d'aga,ga mamakinta saitaji Yana magana Kam bawani Abu dayafaru tsakaninsu shuru tayi saboda mamaki,Amma Duk dauriyanshi Bai iya cemata I love you ba,Wanda a yayin Soyayyar su ada wannan shine babbar Sunnah dasuke ai watarwa a cikin sunnonin Soyayyar su,karashe zancan yayi da Bata Labarin rasuwar Shatima, Zeey💞Abdool tayi kuka dukda Bata taba ganinshi ba Amma sunayin waya sosai taji mutuwarshi,halin Abdool nanan na kwantarwa mutun da hankali aduk yanayin dayake Ciki,lallashinta yahauyi Yana Bata hakuri,shuru tayi tana sauranran sauti datafiso Taji,Sallama yamata tareda jajjada mata dafatan tanayin haddanta dakuma sauran azkar din dayake koyamata,shuru tayi batace komaiba hakan yasa yafasa kashe wayan yafara magana cikin rashin jindadin abunda ta aikata...
"Kyakkyawata Ashe zakiyarda wani canjin yanayi ko rayuwa na Duniya yahanaki gyara lahiraki?" Shuru tayi batace komaiba "magana nake Miki?" Kuka tafashe dashi,shuru yayi na Dan wani lokaci sannan yace "kiyi hakuri Inna takura Miki,Amma Dan Allah karkiyi watsi da burinki dakuma abunda zai taimakeki Duniya da lahira pls,Kar laifin danamiki yashafi rayuwarki,Dan Allah in Kika bar haka yafaru toh bazan taba yafewa kaina ba"Yana Gama maganan yakashe wayan Yana tunanin kyakkawar shi...
*Allah sarki kyakkyawata,tabar kuka yazame Mata jiki,Kuma Duk nine sula,da farinciki nee tasaba dashi,Amma yanzu Labari ya canza, insha'allah Zan canza mikishi kikoma Zeey💞Abdool dinki a da, insha'allah*
*Uhmmmm😅😉, Xuuby Anya Abdool zai iya kuwa?*
Zulaihat kuwa d'aki tashiga tafara abunda tasaba,kuka takeyi kaman Babu gobe Dan a tunaninta Babu yadda za'ayi Abdool yadawo hannunta,Auta ce tashigo tasameta tana Aikin kuka "haba Zeey💞Abdool bazaki daina wanna abunba?" Juyowa Zulaihat tayi da idonta dayayi ja Kuma yakara kanana tafara magana cikin fushi "Auta nine nace a kirani da Wannan sunan dakika Kira yanzu Koh?" "Eh". "Dan Allah na rokeki kidaina kirana yanzu banaso,pls and pls" "ok anbari" "thank you" "Amma sai kinyi Alkawari Zaki daina kuka any how" "eh na dauka" "Inna ganki Zan Kira" shuru tayi Bata Bata amsa ba,Dan dakaman wuya....
B'angaran Uncle G kuwa,haryazo KADUNA Akan magananshi da Dr. Zulaihat Amma Alh. Bai yardaba,dakyar Hajiyar su da gwaggo suka shiga maganan ya yarda, Dadi yaji sosai Dan yanzu bayason abunda zai batawa Dr. Dinshi Rai,Dan yanzu ya sadaukar da zai auri Dr. Nee Akan idan ya aureta zai sota kaman yadda yaka son Zeey💪Abdool.
*Anya zai yuwu Mr Man?,mom Anwar Bashi amsa*
washegarin rananne Yaje gidansu Zeey💞Abdool,ya tausayamata yadda yaga tarame,Amma bashi da yadda zaiyi,Dan yasan bata sonshi,dazata yarda ta amshi Soyayyar shi wlhy zai iya hakura da Dr. Zulaihat ya aureta,Amma Kash yasan bazata yarda ba, Mummy yasamu yasanar Mata da zancan auranshi shida Dr., Mummy tayi murna sosai hadda su Auta,Amma Zulaihat tayi mamaki dataji ranta kawai yabaci Dan Uncle G yace zaiyi Aure,Amma ta daure ta tayashi murna....
Aunty Rahela ce take Mai Duk wani shirye shirye anan,Dan Daman sunshaku Kuma Duk abun yakeso tana zak'ewa tamai Dan karkumanta nace muku a gidansu ya taso Kuma komai Daddyn su nee yake mishi...
Biki yataso ranga ranga Dan ba'asa Rana Mai tsawo ba,Dan Uncle G ya gyara gidanshi na P/Harcourt Kuma komai ya zuba Dan al'adar yaransu Dr. Zulaihat miji keyin kayan d'aki Kuma ya yarda sunyi, shi baya shawara da kowa sai Aunty Rahela Kuma Duk abunda tace shiyakeyi Dan yasan bazata cuceshi ba,yanzu ma itace zata gyara komai Dan KADUNA za'akawo Dr. Tayi sati Daya kafin ya dauki matarshi sai P/Harcourt.....
Anko aka fitar Mai Rai da lafiya,lace nee Mai tsada Aunty Rahela tafito dashi,Kuma dukkansu sunyi Dan sunmai kara,yadawo KADUNA saboda yanzu bikin saura 1 week,sai hidima suke shida Aunty Rahela da ya imran,Dan Duk dawainiyar da akeyi nakudi ya imran nee yakeyi,Oga Zayyad ma Yana can shiyake kula da hidimar can,Dan shi yace sai an daura Aure zasu taho da Amarya,Dan sun bar events din bikin sai ankawo musu Amarya KADUNA,Dan har *Swords crossing* za'ayi a Kaduna, burin Aunty Rahela Dan tanason taga anyishi a biki,Kuma taci burin bikin Uncle G Dan tashirya komai yadda takeso....
Uncle G nee yake kwance akan kujera Suna waya da Dr. Zulaihat tana gayamai zasuje garinsu gaisheda Uncle dinta (wan mamanta),shuru yayi baice komaiba Dan bayason taje Amma bayadda ya iya kawai yace Allah ya tsare hanya,cikin murna da jindadi ta amsa "ameen" "Naga kina Jin dadine my Dr." "Wlhy nakosa saboda inason inje kyauyen mom Dina,Dan nakwana biyu banje ba" "Masha Allah,Allah yakaimun ku lfy" Hira suka Sha sosai Akan gobe da sassafe zasuje Dan ana saura 2 days Uncle G da Yan gidansu zasu tafi P/Harcourt hadda Mata Uku kuma Aunty Rahela na cikin su....
Washegari da sassafe su Dr. Zulaihat suka shirya itada Aunty ta suka Kama hanya zuwa kyauyansu,cikin murna da Jin Dad'i,tunda gari yawaye hankalin Uncle G Bai kwantaba,yarasa Meke Mai dad'i,har breakfast yakasayi Dan baisan Meke damunshi ba,yaudai wuni yayi kaman wani Mara lafiya,tsaye yake ajikin motanshi Yana tunani, saiga wayanshi ya dauki k'ara d'aga wan da zaiyi,sai yaji muryan maman Dr. Zulaihat tana kuka tana magana....
"Oga G,Dr......✍️✍️."
By Tooraee 🥰🥰🥰.
*(GOLDEN PEN)*
YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Historical FictionLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su