*Zeey💞Abdool*
*(2021)**True life story*
*Love story*❤️❤️
*By Tooraee 🥰🥰🥰.
*Page 60*
.......Tundaga ranan Abdool yake zuwa wurin Zulaihat a skull duk ran Friday haka Deeja tatsara Kuma ya dauka,duk Friday sai yaje tun tana shashshareshi Amma inta tuna da maganar Deeja sai ta basar,Abu kaman wasa yazame Mata jiki Dan inhar Abdool baizoba Bata Jin Dad'i,Dan akwai ranan da tafiya takamashi ranan Friday so baizo wannan Fridayn ba har tashiga damuwa,gashi Batada Number shi bare Kuma takirashi,shuru tayi a d'aki Deeja tashigo ta sameta,"Assalamualaikum" Bata jita ba, Deeja ce tazo ta jijjigata tace "keh mekike tunani haka?" "Uhmmm Deeja ki fahimce Ni,Ina cikin damuwa" "meyafaru?" "Abdool nee baizo yauba,Kuma bansan dalili ba" "Toh menene Dan bezoba,keda kikecewa Yana damunki?" "No bahaka bane,duk Friday yake zuwa gashi wannan Fridayn bezo ba" "Toh fah,kikirashi Mana?" "Ai Banda Number shi" "Baki haddace number shi nadaba,sanda kuke Soyayyah" "inada ita Mana, Amma kina da tabbacin wancan Abdool dinne?" "Kuma hakane,Amma Bai Gaya Miki sunanshi bane?" "Yace sunanshi Abdool,Dan na tambayeshi" "Ok,toh shikenan kibari mujira zuwa gobe mugani" "toh ai gobe babu makaranta" numfasawa tayi sannan tasake cewa "Allah yasa Yana lfy" "lfyar ki kuwa Zulaihat? Karfa kice mun kin kamun da son wannan Bawan Allah?" "No bahaka bane,bazaki gane bane" saikuma tayi Shuru "Ina jinki?" "Uhmmm kinsan Allah Zulaihat komai nashi irin na Abdool dinane,Kinga yadda yake kulamun da Young G kuwa? Infa yazo wurina Young G yakoma hannunshi harsai inzamu dawo gida,gashi yarona Yama ganeshi tun kafin ya mikamai hannu zakiga Yana Mai dariya irin yakosa yadaukeshi dinnan,gashi da hankali irin na Abdool Dina da natsuwar su iri Daya" "Toh fah,kinason kice mun haryanzu kinason Abdool?" "Kai Deeja wanne irin tambaya kike mun haka,Naga kaman kinason ki kureni" "No bahaka bane,Dan Allah kiyi hakuri Baki fahimceni bane,Amma Ni na fahimce ki kinji" "Toh Nagode kema kiyi hakuri,Amma menene mafita pls?" "Mafita d'ayane shine muyi addu'a Allah yasa Yana cikin koshin lfy,and again indai yadawo kice Mai bakyason yasake zuwa wurinki a skull yazo gida" cikin mamaki da rudewa tace"gida Deeja?" "Eh gida" "a'ah Deeja wannan bashawara bane,ya zanyi da Aunty Hannafiya?" "Ita ce matsalar ki?" "No Amma itace babba,kinsanta Batada fahimta da wuri,yanzu yanzu saita hau" "Ok,idan yadawo kice yazo,idan kikaga yafara wasu tunani tunani to Real Abdool dinkine,idan Kuma yace Zaizo kaitsaye to bashi bane" "Koh?" "Eh" "inyazo fa?" "Ki kirani nizanshigo dashi gidannan" Ido tazaro tace "Deeja?" "Uhammm kedai kitayani da Addu'a" "toh Allah yabaki sa'a" "Ameeen,Amma gaba dayan mu" suna Gama magana Deeja tafita takira Abdool a waya ta bashi labarin abunda take Shirin yi "Anya zai yuwu kuwa?" "Uhmmm nima dai wannan nee last hope Dina,Amma inada yakinin Mummy bazata wulak'anta kaba" "Eh gaskiya nee Mummy macece Mai dattaku" "to Alhamdulillah daka fahimci hakan,inason zuwanka yazama akan kazo ma Mummy gaisuwane,karka ma nuna kana zuwa wurin Zulaihat a skull,Dan inkazo Ni zanshigo da Kai" "ok Nagode, Allah yasa muci nasara?" "Insha'allah,mahakurci mawadaci" harzata Mai sallama sai tatuna "yauwa koka dawo karkazo next Friday kaji pls" "karki damu basai kin rokeni ba, insha'allah hakan za'ayi, Deeja Ina godiya sosai da namijin kokarin ki" "Ah haba karka damu kade Kara hakuri pls" "Thank you best friend ever" murmushi tayi takashe wayanta Dan Abdool Yana Bata tausayi sosai,Dan bak'aramin dawainiya yake da son Kyakkawar shi ba a Zuciyarshi,Hannu tad'aga sama "Ya Allah ka taimakeni",gida tashiga tana jimami Dan tana danjin tsoro Kar Su Mummy Suki amsar Abdool,Amma Dole tayi hakan Dan shine mafita a yanzu.......
Zulaihat Bata shiga damuwaba Saida wata Friday tayi bataga Abdool ba,har 6pm takai a skull Amma babushi Babu dalilinshi,Salati ta zabga sai kuma tace *Kai Zulaihat mekikeyi haka?* Tafiya tafarayi jiki babu kwari ga Young G yayi bacci,Goyashi tayi tana tafiya tana tunani *Allah yasa bawani Abu yasameshi ba?ko dai inkirashine?toh Inna Kira mezance?Kuma inbashi bane fa wannan Abdool din?* Haka tadinga tunani tana tafiya har ta Isa bakin skull ta hau mota,sai waige waige take Koh zataga Mai Kama dashi Amma Ina,haka ta hakura har ta Isa gida,tunda tadawo takasa sukuni gashi bazata iya gayawa Deeja ba Dan Kar Deeja Tamata wani fassara,ko da Deeja tazo wurinta tagane tana cikin damuwa Amma Bata Mata maganaba tunda Bata Gaya Mata ba,haka takwana babu karfi a jikinta ko kadan gashi Batada wani mafita, washegari tana tsaka da nuni akan wanne Hali yake ciki saiga Kira a wayanta,wayan ta dauko ta duba waye,tana ganin number tagene Dan ko bacci take akace ta fado numbers din zata iya batare da b'ata lokaci ba, d'agawa tayi tasa akunnanta, sallamarshi ce ta daki kunnanta kasa amsawa tayi Dan taji abunda ta kwana biyu Bata jiba,"Kinyi shuru ko nayi laifine?" Cikin inda inda tace "a'ah" "to madallah,haka akeso" wannan kalmar dayafada ne tagane Babu tantama Abdool nee,Dan shikadaine yake fadin wannan kalarma aduk mutanan datake mu'amala dasu, maganan dayasake yine yadawo da ita daga tunani "Ina my G?" "Yana wurin Aunty Hannafiya" "ayya nayi missing dinshi kwana biyu" batsan sanda tace "ai Yana fushi dakai....." Bata karasaba takashe wayan,wayan yabi da kallo Yana murmushi,Kiran Deeja yayi yabata labarin yadda sukayi,"yauwa to Daman na canza tsarinne saboda damuwan danaga tashiga" "Ok yanzu in tura Mata text ko?" "Eh Amma cemata zakayi a text din *idan badamuwa inason Zanzo Inga Young G gobe insha'allah*" "Ok angama insha'allah" sunagama wayan yatura sakon kamar yadda Deeja ta buk'ata,tana zaune taga sakon,tarasa yazatayi? Tanason yazo Amma tayaya?,Deeja Tama forwarding text din,ga mamakinta saitaga reply *Allah ya kaimu,karki cemai a'ah pls*, *Ok* Tamata reply,reply taimai kamar haka *Allah ya kaimu Rai da lfy*,wani tsalle yayi dayaga reply din Amma Yana tsoro dawane Ido zai shiga gidan, *Anya Zan iya kuwa?* sai Kuma yatuna Deeja "In nama Deeja haka bankyauta ba"
Washegari da sassafe Deeja tazo gidansu Zulaihat,"yauwa yakukayi dashi?" "Tunda namai reply shikenan" "ok Allah ya kawoshi,ai yau weekend Mummy nagida" "Eh tana gida Aunty Rahela ma nagida" "Ok karki Gaya musu fa?" "Daman fa,Ina Zan iya" "Ok Allah ya kaimu",bayan wasu 'yan a wanni saiga sako Abdool yashigo wayanta *na iso fa* kasa Mai reply tayi sai tanunama Deeja,Deeja ce ta amshi wayan tace *Ok,ga Deeja Nan zata shigo dakai* mikewa Deeja tayi Zuwa wurin Mummy Dan tagaya Mata, shiko Abdool Yana kofar gida a tsaye saiga Aunty Hannafiya ta dawo daga unguwa,d'aga Kan dazatayi Saita ganshi, k'ara bude idonta tayi Dan taga waye? "Tabbas Abdool nee,Toh meyakawo shi? Kuma Mai yazo yi?.....✍🏼✍🏼.
*Toh fah yau akeyinta,ga Deeja a wurin Mummy ga Abdool da Aunty Hannafiya a gate😅*
By Tooraee 🥰🥰🥰
*(GOLDEN PEN)*

YOU ARE READING
ZEEYABDOOL
Fiction HistoriqueLabarine na masoya,yadda suka shawala a rayuwar soyayyar su