Page 7~~8

448 47 0
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN* 👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab sardaunerh*

   بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚

         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔

     *page* 7~~8

   Duke take a bakin murhuu tana fitar wutar itacen duk hayak'i ya cika gidan sakamakon itacen da take amfanii dasuu dan yu ne, duk idanunta sun cika da kwalla, fita kawai take amma wutar taki kamawa sai dan banzan hayakin da takeyiii "sallamar k'anwar ta Salamatuu Tajii tana k'walawa inna Saude Kira, inna inna ga kukar na k'arbo miki, kuma tace nace tana gaishekiii"
       
      
     Inna Saude Ce dake fitowa daga ciki dakin ta, "tace yanxuu Salamatu Dan kin rainani shine baza ki shiga ciki ki mik'amin shine kike ta k'wallamin kira haka", maganar tace ta katse a lok'acin da hayak'ii ya mata maraba.

     "Innalilla'hi wa inna ilaihi raji'oon tafada tare da rafka salati",wanda yasa sai da Aleeya Ta mike tsaye da sauri, "yayin da inna Saude Tace, yanxu Aleeya kina zaune gidannan ya cika da hayak'ii amma ko ki heta wutar nan".
   
     "Wlh inna ita ce nake hetawa tun dazuu cewar Aleeya amma taki kamawa", "ok to bara nazo na heta miki k'ar ki ci gaba da hetawar"cewar inna Saude Tana kok'arin komawa cikin d'akin.

     Maganar Salamatuu Ce ta katse mata hanzari yayin da take cewa "ni gaskiya inna nace miki kidaina cemin Salamatuu".
      "Salmaat ne suna na fah, amma k'in ki barin kirana hakan, kin maida min suna sai kace na tsoffi tafada cikin shagwabaa".

      " Yi hakurii auta bazan k'ara ba  kinji", "murmushi salamatuu tayi", "inna Saude Tace ko kefa autaa, tare da shiga cikin dakin ta da ko arxikin ledar kasa bai samu ba balle ai maganar kujeruu....

     Salamatuu Ko nace Salmaat Ce ta nufi wurin Aleeya Tana cewa "Addana sannu da aikii",

" yawwa k'anwata harkin dawo daga aiken inna ne"?

  "Eh tace tare da cewa Addana wannan wutar ba kamawa zatayi ba,naga da alama itacen nan  danyu ne, bara na k'arbo kudii wurin inna na sayo miki yanga", (tafada cike da tausayin y'ar uwarta kan hayakin da take sha).

    "A'a barshii kawai kinji!
yanxu wutar zata kama",

   "Aa Adda bara na k'arbo dai tafad'a tare da nufar dakin inna Saude, ko sauraren Aleeya Bata tsaya yi ba tashiga dakin tana cewa inna bani kudii na k'arbowa Adda yanga, itacen chan basa ci suna bata wahala sosai".

  "Wai auta yaushe zakiyi hankali ne?
      "Ko sallama babu xaki fadowa mutane cikin dakii kamar karamar yarinya, baki ga yadda yayarki take yi baaa hala?
      "Msstwwwssss" "bana san shirme wlh ta fada tana jan tsakii".

       "To ni dai kiyi hakuri dan Allah" kan wannan dalilin tasan halin innar ta ta cewa zatayi batada su, dan shegen son kudin tsiya  gareta,shiyasa ma bata biyema fad'an da take mata ba ta bata hakuri, tare da cewa" ni dai dan Allah  inna ki bani na sayo mata mana, kinga  lokacii na tapiya hudu ta kusa gashiii kuma 5:30 zamu tafii makarantar dare".

     "Ah lallaima yanxu hutar ce baza ta kama ba sai an sayo yanga"? 
         "To kada Allah yasa takama indai sai na bada kudi, ai ubanku ba kawowa ya yi ya jibgemin ba" ta fad'a tana hucii.

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now