👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkaiYa ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 51&52"wai Umma meyasa kike wannan abun ne,me Azeema tayi miki ne a ko da yaushe baki da aiki sai zaginta da aibata ta,maganar gaskiya banajin dàdin hakan ko kadàn,Azeema fa matata ce uwar yayana kuma suruka a gareki hakan sam bai dace ba"
"yayi kyau Abubakar, dakyau gara ka nunan iyakata amma bakomi,basai kayi mun rashin kunya ba nasani,nasan cewa wannan makirar matarkace amma ka sani ba suruka ta ba ce akul dinka karka kàra danganta ta dani domin har abada bazan karbeta a matsayin suruka ba, bana sonta bana kaunarta kuma bazan tabà sonta ba"
Wasu hawaye masu zafi suke fita daga cikin idanuwan Umman khaleel kàsa jurar kalaman Umma Hadiza ta yi ta tashi ta fita daga cikin d'akin
Tana cikin goge hawayen fuskar ta Mama Hawwa ta fito daga cikin kitchen tsaye ta yi tana kallon ta na wani lokaci dama tasan hakan zata faru,tun auren Azeema ba lokacin da zata zo gaida Hadiza bata fito tana hawaye ba.
"ba zaki gaji ba ko?"
Cikin sauri ta d'ago idanuwanta ta dake da damshin hawaye ta sauke su cikin na yayar mahaifiyarta
"magana kike Mama"
ta fadá domin batason mama ta fuskanci halin da take ciki"kwarai kuwa magana nake kuma nasan kinji abunda nace kawai kina basarwa ne"
"ba haka bane Mama"
"idan ba hakan bane yaya ne? fadamin ina saurarenki?"
Shiru Azeema ta yi domin idan tace magana za tayi ba shakka kuka ba zai bari a ji abunda zatace ba
Hannunta mama taja suka shiga cikin d'akin ta suka zauna ta dubi Azeema ta ce
"sai yaushe ne zaki daina zubar da ruwan hawayenki saboda Hadiza eii"
ko yanzun shiru tayi
"ki bude baki ki mun magana ba na son shiru,hat sai yaushe zaki sa ba da cin mutunci da cin kashin da take miki ne? ya kamata ace yanzun kin sa ba da duk wata halayya ta Hadiza ! ki daina wahalar da kanki da idanuwanki kina zubar da hawaye a dominta"
"har abada mama !! har abada bazan daina zubar da hawaye ba sai lokacin da ta karbeni a matsayin surukarta sannan,wanda watakil nasan sai bayan mutuwata..Mama ko yanzun ta saka sai Yah Abubakar ya kara aure"
takarisa maganar cikin kuka mai ciwo
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Historia Cortaبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...