page 47&48

212 29 4
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab Sardaunerh*

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS          🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

              *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Follow me on whattpad*
@Zeesardaunerh

*Page* 47~~48

"subhanallah lafiya dai salamatu mi ya sameki"

Dakyar tarin ya tsagaita amma ta d'an ji jiki.Na taso da sauri tare da mi kawa Salmat Ruwa tasha.

    Tunani kawai Salmat Keyi yadda za su kaya da Inna,tana cikin wannan tunanin ne Inna Saude Ta nisa da niyar yin magana Salmat ta rike kanta tana layi,duk sai Inna Saude Ta rud'e domin bata son abinda zai taba Agla Balle Salamatun Ta duk sai tabi ta rikice.Ni Aleeya Diyar Muhammadu jikanyar Yusuf na tsaya kallon ikon Allah,idan na kalli Salmat muka hada ido sai ta kyafta min ido tare da kashe min daya idan na kalli Inna Sai ta bani tautsayi sai tambayar Salmat Take ko bata da lafiya ne?ita kuwa sai kara langwabewa take ala dole ga marar lafiya.

     Daki Inna Ta kai Salmat tare da kwantar da ita bisa yaloluwar katifar mu tana tofa mata Addu'a domin ce mata Salmat tayi kanta ke ciwo kuma ta lafe kamar marar lafiyar gaske.

   Inna Na fita ta wuntsilo inda nike tana cewa,

"Addana Ya kika ga acting dina"

tana kwashewa da dariya,kafin nayi magana Inna Ta nufo dakin aiko kamar walkiya na nemi Salmat Na rasa.  

     A chan saman katifar mu na hangeta sai zuba nishi take a hankali,bayan Inna Ta shigo Salmat Ta daga kai ta kalleta sannan a hankali,

"Inna Da wani abu ne?"

"a'a bakomi,dama cewa nayi bari na kawo miki paracetamol kisha"

"tou Innata"

Kallon Salmat Nake amma bansan lokacin da takawo kusa dani ba tana cewa a hankali don kar Inna taji,

" yadai Adda Agla,acting dina ya yi kou?"

Komi bance mata ba na tsureta da idanu alamun tambaya,sai turo baki tayi sannan tace,

"wai fa kan batun kudin mu ne fa Adda Shine take son in bata shiyasa kika ga nayi wannan abun fa"

kallon mamaki na ke yi mata domin ni a sanina nace ta kaiwa Inna kudin gudun jidalinta amma ita da kanta tace mu bawa baffa ya ajiya, to mi hakan ke nufi?

    Na bude baki da niyar yin magana Salmat tayi azamar cewa,

"Adda Aleeya Don Allah Kada kice wani abu ki bari zan miki bayani kinji please!

Gyada mata kai nayi sai tayi murmushi tace,

"bara na koma gurina Inna ta kusan dawowa amma don Allah ki dauko min sauran danbun mu yasin ban koshi ba Inna Ta kirani kinji Addana"

dariya maganar ta ta bani amma sai na yi murmshi na mike domin kuwa ta narki dambu d'azu amma ta ke cewa wai bata koshi ba,ita kuma ta koma gurinta.

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now