page 79&80

269 25 12
                                    

👩‍👩‍👧‍👧WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
           by
Zainab Sardaunerh

🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          ⚜️©J.A.W📚🖌️

DIYAH
{ Short story }

Labari  ne mai cike da ban tautsayi tare da  soyayya mai zafi

Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number 2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number 09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number 09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295

©️♤♡ Zeesardaunerh


Page 79~~80 

Dukansu idanu suka zubawa Salmat har Aleeyar domin ita ma abun yazo mata a shock kamar sauran abokananta.

Kowanensu ya hau tambayar Salmat wanene?wayeshi?a ina suka hadu?

Ganin kallon da Aleeya ke mata yasakata jan jiki tana cewa,

"nidai nayi ajinmu har malam ma ya shiga,duk tambayar da Kuke bukatar amsarta zaku iya tambayar Adda,amasa daya ce zan baku wato sunansa"

Cikin zakuwa tare da mamaki suke tambayar sunan,saida ta bari ta kai bakin kofar fita ta daga murya yadda zasu jita tace,

"Sunansa MUHAMMAD KABEER"

Dukansu juyowa suka yi suka zubawa Aleeya idanu,

Amina tace,

"yanzu Agla haka lamarin duniya yake,shine ko a bamu labari"

"kedai kyaleta Amina ta kyauta,da yanzu Salmat bata sanar muna ba shikenan sai munji za a yanka engagement"cewar Aisha

"ni fah duk bama wannan ba abun mamaki ya bani wai Agla ta fara soyayya ikon Allah shiyasa naga kin chanza"Maryam ta karisa cikin dariya.
Dariya suka saka harda tafawa sannan Rahama tace cikin zakuwa,

""y'ar uwa bamu musha labari,wanene ya yi nasarar tafiya da zuciyar mai tsada"

Maryam taci gaba da cewa,

"yaushe kuka hadu har kika kware masa domin nasan duk namijin da ya ganki sai ya kware miki amma banyi zaton zaki fara soyayya soon  ba"
Wata dariyar aka saki domin yanayin yadda Maryam tayi maganar dole yasaka ka dariya

"don Allah ki bamu sha nifa har na gaji"inji Aisha

"kyaleta Aisha kinsan halinta yar air ce sai ta karemana jan aji"cewar Amina

Shiru Agla tayi ta zuba musu ido tana saurarensu domin ita fa takasa tuna waye MUHAMMAD KABEER din da Salmat ta fadi,ko ita kanta batasan wayeshi wannan da yabada sakon akawo ba.

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now