Page 85&86

132 14 11
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 85&86

"Ke wace irin mata ce Saude,na rasa a wane fanni zan ɗoraki,yanzu da ke za'a haɗa baki a yiwa mai tsada ƙaryar mutuwa? Ko da yake ma ba haɗa baki akayi dake ba kece kika shirya komi,wacce irin tsanace kika yiwa Aleeya,wace irin kiyayyace kike mata da har kike mata fatan mutuwa a waɗannan ƙananan sheƙaru nata,me ta tsare miki,me ta tare miki da har bakya bukatar ganin ta a doron duniya? Nace me ta tsare miki?

Shiru Inna Saude tayi tana kallon mama Kareema har yanzun kuma tana dafe da kuncinta,Mama Kareema taci gaba da cewa "Dama na faɗa miki tun ba yanzu ba a duk lokacin da na kama munafukin da yake ɗaukar sirrinmu da duk wani motsin Agla yana kaiwa waccan gidan sai na binciko shi kuma haɗuwar mu dashi bazata yi kyau ba to gashi yau Allah ya tone asirinki,ki sani kin ɗebo ruwan dafa kanki sai na nuna miki cewa Aleeya tanada gata,rayuwarta na daraja a gurin mu,tafi karfin ayi wasa da rayuwarta wallahi,tafi karfin ki mayar da rayuwarta kamar ƴar tsanarki wacce zaki juya a duk lokacin da kika so,yanzu ke ko kunya ba kyaji idan kika kalle kanki,yarinya marainiya ta ɗauke tamkar uwa tana miki biyayya fiye da ƙima tana ganin girmanki da mutuncinki duk abunda kikace shi take bata tsallakewa umurnin ki,itace zaki saka a binneta da ranta? Itace zakisa ayi jana'izarta alhalin tana raye bata mutu ba? Anya kuwa akwai imani a zuciyarki Saude,ko kaɗan bakya tunanin hakan ya zama matsala ga rayuwarta? To wallahi ki sani ina mai tabbatar miki bazaki ci bulus akan wannan abun ba zamu haɗu dake a kotun musulunci sai kin faɗa mana lokacin da kika kashe Aleeyar da har kika saka aka yi an ansar gaisuwarta,kuma ki sani da yardar Allah sai kin riga mai tsada mutuwa,sai mai tsada taga muturwarki da ran ta da lafiyarta, sai kinga ƴaƴa da jikokin Aleeya a gabanki ko bakyaso,baƙar mace mai baƙar zuciya"

"Ni Saude nafi karfin na ɓata lokacina akan Aleeya,na cutar da ita ko na yi fatan mutuwarta wannan sam basa gabana,nafi karfin nayi da uwarta sannan na dawo nayi da ita,bata kai wannan matsayin ba,uwarta na tsana,uwarta na ƙi,uwarta ce bana fatan gani a doron duniya,kuma Allah ya cikamun burina ya ɗauki rayuwarta ba ita ba,tsanar da nakewa uwarta ta shafeta amma ko kaɗan rayuwarta da mutuwarta sam ba abunda ya shafeni bane,duk abunda kika ga Saude ta mayar da hankali akansa akwai dalili idan ba haka ba mai tsada tama isa na tsaya har ina ɗauki ba daɗi ga aurenta,ki bar ganin kin girmeni a shekaru hakan bazai hana na miki rashin mutunci ba wallahi,kin fi kowa sanin wacece Saude ada ma ballantana yanzun,kin tafka babban kuskure na ɗaura hannunki akan fuskata wanda sam bazan bari hakan ya tafi a banza ba,sannan ki sani ba kotun musulunci zakije ba idan akwai kotun da tafi ta kije,matukar aka aikowa Saude da sammaci zaki ganta,ba uban da nake tsoro a faɗin duniyar bayan Ubangiji na kema kin sani;mara gaskiya,ma ƙaryaci ko munafuki shike jin kunyar tsayuwa gaban alkali ba Saude ba,ki kuma sani kisa a ranki ko kaɗan Aleeya bata gabana a yanzu da har zan saka ayi jana'izarta saboda wani abu ya sameta,ta fi ruwa gudu ko ta tabbata bata dawo ba wannan ba abunda ya dameni bane" taƙarisa tana saukewa Mama Kareema yatsunta biyar a fuska a rashin sa'a marin ya sauka a fusƙar Salmat wacce ta lura da abunda mahaifiyarta ke shirin yi ta shiga tsakani

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now