👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
Page 67~~68
"Nima Ummu bansani ba wlh sai munje zamu gani amma dazu naje basa nan sunyi wamako"
"amma Muhammad baka kyauta ba,shine ko ka fada naje na bawa iyayen nata hakuri shine ka kama bakinka kayi shiru"cewar Alhji Sa'id "
Dukar da kai kawai Kabeer ya yi yana sauraren mahaifinsa ya yin da Ummu ta cigaba,hakuri ya ba su sannan su kayi musu Allah ya tsare Alhji Sa'id nacewa inshaallah gobe shima in yasamu time zai je ya dubata.
Cikin kankanin lokaci su Kabeer suka isa gidan mama Kareema bayan sun biya sun siyowa Agla kayan makulashe na marasa lafiya.
Sun samu tarba ta mutunci kwarai ya yinda Salmat da su batul suka Jone suna zuba labari duk da cewa zasu girmi Salmat a shekaru amma kadan sai dai Salmat akwai girman jiki ga shegen iya yi.
Sun yaba da Agla kwarai ga kyau ga nutsuwa duk abunda zaya saka ta dariya Batul yin sa take ya yinda Fatima ke daukar wa Kabeer pics din Agla cikin hasken da ya haskaka gidan na generator da Abban Ramlat ya kunna.
Labari sosai ya barke tsakanin su Ramlat da su Fatima kamar anjima da haduwa duk da cewa ita Ramlat ta san su Fatima domin tana ganinsu a shiyar gashi school d'insu daya amma sun tsare mata da aji guda.
Dakyar mama Kareema ta Kora su Batul da suka shanya Kabeer waje yana jiransu,sallama su kayi da kowa batul na cewa,
"sai mun dawo gobe antynmu"
Har zasu fita waje sai ga Abban Ramlat bayan sun gaisa da Kabeer ya shigo dashi ya ga jikin Agla ya yi mata ya jiki suka gaisa da mama Kareema ya ajewa Agla ledodin tare da kudi amma Sam mama Kareema tace aa ba'a haka kayan ma an gode,badon ya so ba sai don baya son jayayya ya maida kudin ya wuce yana Allah kara sauki(Anya kabeeru kodai_kodai🤣)
Ko a yanzu sai da Salmat da Kabeer suka taba drama Kafin su wuce su batul na daga musu hannu suma hakan.
Aleeya
Fada sosai nasha wurin mama Kareema na watsar da maganin da nayi kafin ta saka min wani a baki da hannunta na kora da ruwa kamar nayi amai amma ba hali domin ta daure fuska ba sassauci irin no mercy dinnan,mi kuwa su Salmat zasuyi in ba dariya ba;wai yau anga uwa da d'iya a rana.
Zuwan su Batul su ke kowa ya d'an taimaka na saki jikina domin yammatan akwai ban dariya da zasu tafi ba daďi domin Al'umma rahama ne suma suna da rawar kai irin na Salmat.idan suka cemin antynmu kunya ma nakeji domin ba wata tserayyyar shekaru a tsakanin mu sosai illa girman jikin da bana da sai ka dauki shekarunmu guda dasu Samlat.
Rufe idanuwa na nayi da yayyansu ya shigo domin Kafeni ya yi da idanuwansa shegen kallo ke gareshi kamar yah Anwar.
Bayan tafiyarsu su Ramlat suka buďe ledodin Salmat na cewa,
"ai wannan abun mu aka kawo wa domin mune masu jinyar ko ba haka bane k'awas"
"hakane tawan,idan bamu ba waza'a kawo wa kibar ma fadin wannan zancen"
"to Kajin turai surutun mi ne ko ke mata akai kunki barin ta tayi bacci "
"Ayya mama yau kuma wannan sunan muka samu?mungode dama kasafin kayan dubiya ne muke yi da aka kawo mana"cewar Salmat
"Kune ko da yaushe baku gajiya da surutu,kasafi sai kace kayan sai dawa?wai ma saya cikin ku wacece aka kawowa kayan dubiyan?
Ramlat ta dubi mama Kareema tace,
"ni dai bani ba"
Hararar ta Salmat tayi tana cewa,
"wlh Salmat kiji tsoron mai mana ruwan sama domin yana kallonki,yan zu bada amsar ne shine sai kin ware kanki daban to tsaya kiji ni ba irin ki bace sannan kuma ki sake hali, ta dubi mama tana cewa,
"to dai mama maganar gaskiya Adda Agla aka kawowa amma kinsan halinta ba ci take ba shine muke kasafawa ni da Ramat kar ya lalace"ta karisa tana saka cinyar filamingo a bakin ta.
Girgiza kai kawai mama Kareema tayi domin iskancin su Salmat mai degree ne.Pate ta dauka ta dibarwa Agla gasasshen nama tare da flamingon ya yin da ta dibarwa su Salmat lemo da ayaba domin tasan idan ta barmu cinyewa zasuyi tunda kurayen gaskene ta dau Hollandia guda ta barmu su guda suna chan wurin rikincin da ya barke tsakaninsu kan Salmat tace Ramlat ta sake hali shine fa yazama abun gardama.
Mama na bawa Agla naman ta naci shima cikin ta matsa mata domin Agla bata son ciye-ciye da yawa domin ko naman bata ci tsunke biyar ba sai kankana da tasha da ayaba.
Ganin rigimar tasu bata ajewa bace mama ta daka mutsu tsawa tana cewa Allah zata kora su waje ko suje dakin Ramlat su kwana tunda hakan ake jinya sannan sukayi shiru aka koma ciye_ciye.
Kabeer
fadan da yaso ya yi musu na shanya shi da sukayi ya kau domin yaga annurin zuciyarshi.
Su Fatima sun cika shi da surutun sun dace,sai yabon ta su ke domin duk wanda ya zauna da Agla sai ta shiga ranshi.
Haka suka ci gaba da tafiya cikin motar suna masa firar Aliya da kuma sabbin abokanai da suka samu;da yake ba yawo suke yi ba shiyasa basa da kawaye da yawa.
Yana jin farin ciki from no where yana shigarsa shi Kansa ya tabbatar da cewa ba karamin so ya kewa Agla ba sai dai fatan Allah yasa ta so shi ko da kwatan son da yake mata ne.🖊️🖊️🖊️
Zeesardaunerh ce
( ~Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)
# _comment_
# _like_
# _share_
comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
