👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai
Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 53&54
Kallon_kallo suka shiga yi tsakanin su karar fashewar abu ya saka Agla janye jikinta da sauri dukawa tayi tana duban glass dìn dake cikin cube dìn da ya fashe shima dukawar ya yi suna facing juna so close kallon glass dìn da ya fashe yake wanda ke dauke da wani abu golden mai rubuce da harufa guda uku a yare biyu,turanci da larabci I LOVE YOU
Kallon kalmomin yake yayin da Aleeya ke tunanin ya zata kwashe wannan fasasshen abun me kuma zata cewa wadancan mutanen, ganin ta yi ya dago ya kalleta ya kuma kallon abubuwan dake kasa itama kallon rubutun ta yi taga abun da aka rubuta dágowa ta yi taga ita yake kallo a zuciyarta tace "me yake nufi?" juyawa tayi ta kalli mutanen da suka aikota suma idanuwansu akansu yake kamar yadda idanuwan kowa dake gurin yake a kansu Allah ya sa dai har yanzu fuskarta rufe take da likab
Mikewa ya yi ya dubi bayanta gurin da take kallo idanuwansa suka sauka akan na AYSHERT dàuke idanuwansa ya yi daga kallon ta ya mayar da su kan Aleeya amma kuma kamar almara bai ga kowa a gurin ba, waige_waige ya fari amma ba alamar ta
"wa ka ke nema ne bayan gani a gaban ka"
Muryar chewing gum dìn sa ta sauka a kunnuwansa waiwayowa ya yi tare da sauke fararen idanuwansa masu kwarjini a kanta basarwa tayi ta na janye nata idanuwan
"sakon welcome back ne na turo maka nasan cewa idan ni na baka da hannuna ba karba zakayi ba,naso ace ka karbá sannan na bayyana maka kai na amma kash waccan shashashar bebiyar ta lalatamun plan"
I love you d'in ya kára kalla sai yanzu ya lura da sunanta dake gefe a rubuce
Tafiya ya fara yi yayin da idanuwansa ke yawon nemanta amma ba wanda zai fuskanci hakan,biyo bayansa Dr.Ayshert tayi tana cewa
"amma bakomi ko yanzu zan iya welcoming naka da harshena domin hakan ma ya fi "
Shan gabansa ta yi ya dakata da tafiyar da yake tare da yin taku biyu baya
"WELCOME BACK MY LIFE I LOVE YOU"
ta fada tare da yi masa blowing dìn kiss tana murmushi,janyewa tayi daga gabansa sai da ta kawo dai_dai gurin kunnuwansa tace "ka shirya wa ganin soyayyar mahaukacciya This is the beginning" ta nufi gurin da kawarta Mina take.
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Historia Cortaبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
