👩👩👧👧 *WASU MATAN* 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
*Story and Writting*
by
*Zainab sardaunerh*
بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚
_________________
______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_
🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y
*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 43~~44
Tabe baki inna Saude da ke fitowa daga d'aki tayi sannan ta ce,
"lafiya ake ne ma na kamar wadda ta b'ata"
"ai kam kin b'ata innarmu domin tun shigowarmu ba mu gan ki ba sai da mu ka kai ga cigiyarki"cewar Ramlat Tana dariya,Salmat ta chab'e zancen cikin dariya tana cewa,
"hmmm ke dai kawas bari,inna kud'i ta yi shiyasa ki ka ga ta b'ata,tana gudun ta fito daga d'aki aljani ya santale mata kud'i"
Dariya su mama suka sa ka harda ya *ANWAR* Duk da cewa ba su fahimci zancen Salmat Ba,amma ganin yadda inna ta ha yayyako musu da fad'a kamar taci babu ya saka su dariya.
Ni dai lokacin da na sa mu hankalinsu ya d'auku ga fad'an inna na sulale zuwa d'aki na saka hijab d'ina blue iyakrsa guiwa sannan na dawo gunsu na zauna.
*ANWAR*
Dukda cewa idanuna na kan diramar su Ramlat Da inna amma hankalina na gunta,ina kallonta sai da ta diba taga ba mai kallonta sannan ta shiga d'aki,bayan wasu mintukka ta fito sanye da hijab d"inta ta zauna,dama ni tun da ta shiga d'aki nasn cewa da wuya ba shine zata saka ba domin yadda take takura kanta kamar wadda z'a cinye d'anya.
Bayan inna ta gama fad'an nata suka gaisa da mama kareema sannan ya Anwar Da Ramlat suka gaida ita,ta amsa gaisuwar ya Anwar Amma ta Ramlat cewa tayi ba ta so ta rike abunta,aiko mi Salmat zatayi in ba dariya ba .
Ana cikin haka Bappana ya shigo gidan da sallamarsa muka amsa tare da gaidashi,ya samu wuri ya zauna suka gaisa da mama kareema da su ya Anwar.
Bayan sun gaisa ne yake fad'a mata dalilin kiranta inda ya shiga ba ta labarin abun alkhairin da ya same su.
Alokacin da taji bappa na fad'in "dalilin da ya sa nace kizo......."har zuwa in da yake sanar da ita kudin da aka ba ma su inna Saude,wani takaicine ya yi nasarar lullube inna cikin ranta take cewa,
"yo da ma kenan shi ya kirata,hmmm to mi yake nufi da sanar da ita kudin da muka samu?yasin ni ko kwandala ta baza ta gani ba bare na b'ata ehhhe"
tana cikin wannan tunanin ne taji Bappa na fad'in Muktar ya ba shi kud'i kimanin dubu saba'in,cikin zaro idanu tace,
"wai don Allah dagaske dunbu saba'in ya baka malam?"
dago kansa kawai yayi yana kallonta sannan yace,
"eh"
a takaice domin shi lamarin saude kan kud'i mamaki yake bashi,tun d'a zu yana lura da ita yadda ta b'ata ranta saboda kawai ya fad'awa k'aunarsa abun da suka samu,,amma dibe ta yanzu kamar ba ita ba daga jin maganar kud"in da ya samu.
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Storie breviبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
