PAGE 45&46

235 28 9
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab Sardaunerh*

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS          🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

              *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Follow me on whattpad*
@Zeesardaunerh

_Assalamu Alaikum masoya littafin wasu matan barkan mu da dawowa hutun sallah dafatan anyi sallah lafiya, naji korafe -korafen ku da dama game da rashin samun update bayan sallah, ina mai baku hakuri wani uxirune ya rike ni amma inshaallah zan kokarta na dinga typing ko da sau biyu ne a sati.Inshaallah idan komi ya dai-dai ta zan cigaba da typing kamar da.Na gode da kulawar ku a gareni Son So Fisabillilah❤️❤️❤️_

*Page* 45~~46

      "bye na fita sai na dawo "
Ya yin da bata jira yace komi ba ta yi tafiyar ta tana kar ka d'a makulanta.

Bai ce mata uffan ba sannan bai yi yunkurin dakatbar da ita ba illa sake lumshe idanunsa da ya yi yana tunanin halayen Suhailat Da rayuwa Aurensu.

  Kamar  jiya haka ya yini cikin gidan yana aiki a system d'insa salla kawai ke fitar dashi,sai misalin karfe  biyar Suhailat Ta dawo gidan;lokacin da ta shigo yana dakin karatunsa.

   Ana kiran sallar magrib ya sauko daga sama domin zuwa masjid,zaune ya tarar da ita sanye da k'ana nan k'aya ta saka earphone tana shan waka tare da kallon abu a Instagram,har ya gitta ta ya dawo.
    Cikin muryarsa mai amo yace mata,

"hello"

bata lura da shi ba kawai sai jin saukar  lallausan y'an yatsunsa tayi a kunnenta ya zare earphone din.Dago idanunta tayi ta na kallansa tare da d'aga masa gira daya(ya dai)da idanunsa ya yi mata in kiya yana duba agogonsa.
      Agogon da ke sanye ga hannunta ta duba sannan ta dubesa tace ,

"ok"

tana narkar da idanuwanta cikin nasa lumshe idanuwansa yayi tare da mika mata abunda ya cire mata yana mata gargadin kar ya dawo ya cin mata nan, sannan ya yi ficewarsa.
       Turo lips d'inta tayi ,chan  kasan makoshinta tace,

"tou"

domin ta fahimci sakon da idanuwansa suka isar mata ba tare da ya furta ba.
    Tasan halinsa sarai shiyasa ta mike tayi sashen ta,har a ranta bata son takura  amma A.M ya kasa fuskantar hakan.
   Palon ta ya hadu iya kar haduwa.Ba'a ma maganar bedroom komi ya yi,duk wanda ya shigo sashen Suhailat Yasan cewa y'ar gata ce kuma naira ta koka a wannan wurin.Misilta muku yadda part dinta yake b'ata lokacin,iya abunda nasani shine tabass ya hadu sosai.
      Alwala tayi sannan ta shinfida carpet ta kabbarta sallah.

Sai bayan isha'i ya shigo gidan,bayan yayi shirin baccinsa coffee kawai ya hada a kitchen dake nan part dinsa ya zauna bisa gadonsa yana kurba yana waya da Ammiensa.

*_RANAR LITININ* *(MONDAY)*

Na tashi ciki farinciki a wannan ranar,hakan kuma baya rasa nasaba da abun Alkhairin da riske mu a jiya,ko a karin kumallon mu (breakfast)na yau da banbanci domin Inna Saude Mai bakin cin d'adi (inji Salmat)ta siyo muna abun karin kumallo mai rai da lafiya,harda kawai ta bada a tsoyo mata.

   Ga ba daya mun sha'afa da batun zuwa boko,gashi jiya ko islamiya ba muje ba.

********
Da sauki ta tashi yau domin rashin kwarin jiki ne kawai ke damunta amma ta d'aure ta shirya domin tana muradin ganin rabin ranta.

    Bayan ta kammala karin kumallonta ( breakfast)a nan sashenta ta wuce sashen momynta amma kash ko da ta shiga bata riske ta ba.Motar ta kawai ta shiga tare da wucewa Asibiti(Hospital) domin ta zaku tayi tozali da rabin rayuwarta HAYDAR.

********
Bata jima cikin baccin ba Kabir Ya kwan-kwasa mata kofa wanda yasa sai da tafarka gashi dama bacci ba wani nisa yayi ba sosai.
      Rasa abunda zata ce masa tayi domin imani yawa yayi mata kuma kalmomi suka mata karanci, tsaki kawai ne ya samu muhallin fitowa daga bakin ta ba tare da ta shirya ba.

********
Jin ya kwan-kwasa mata ba amsa ya sashi kutsa kansa cikin dakin.Dai dai da shigowarshi tsakin ta ya dira a kunnuwanshi,baisan lokacin da ya juya ba,hakan kawai yaji zafin abinda tayi masa,gashi har yana neman rasa jam'i saboda ita aransa yake kara mamakin hallinta batasan darajar wanda ya halicce taba balle ma shi mijinta.Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya kutsa kanshi cikin massalacin.

********
Mikewa tayi ta shiga ban d'aki(bathroom)ta watsa ruwa domin jikinta ya saki sannan tayi brush tare da Alwala,tsaye tayi tana duban kanta acikin madubi,duk ta rame dare daya tak kamar ba maryama ba,zuciyarta zafi take mata kuma har yanzu bata jinta dai-dai,fitowa tayi ta kabbarta sallah yayin da yin sallar kawai take amma batasan mi take karantawa ba balle tasan raka'a nawa tayi,zuciyarta sai tunzurata take kan kar ta ragawa kabir,a da ta dauki zabi daya cikin zabin da mahaifiyarta ta bata amma a yanzun bata jin zata aikata daya acikin su dole kabir yasan wacece MARYAMA In ma yasani mantawa ne yayi  to ya tuna,
sai da ta gaji dan kanta ta sallame sallar zuciyarta fal tunani.

********
Gaba daya ya gama tafiya da da imaninta har hasaso kanta take tare dashi suna tafiya a jere cikin farinciki,kallonsa take ta kasa dauke idanunta a kansa duk da kwarjininsa da ya cika mata idanuwa.Matsayi DR.ALIYU MUHAMMAD AHMAD Daban yake a zuciyarta baza ta iya hakura dashi ba,ga ba d'aya ta fita daga duniyar mutane ta afka duniyar SOYAYYA ba ta ankara ba sai ji tayi ya gifta ta gefenta ya wuce ba tare da ya ko kalleta ba sai zazzakar muryarsa take ji  dake amsa amo a cikin kunnuwanta yana amsa gaisuwar sauran Doctor's da ke gaba da ita kadan.

********
Office d'insa ya shiga yana k'ara hade rai,shifa duniya ya tsani mutum mai shegen kallon tsiya amma Aysha Ta ki fahimtar hakan,shin wannan abun da take shi zai sa ya SO ta komi,

"mssstwwss"

yaja tsaki,dariya yaji an kwashe masa da ita,dago kyawawan idanuwansa yayi ya sauke su kan Dr.Abdallah Dake cikin office d'in.
        Gaba daya shi sam bai lura dashi ba har ya iso tsakiyar office din,saurin d'auke idanunsa Dr.Abdallah Yayi domin kwarjinin da Dr.HAYDAR Ke masa amma hakan baisa ya tsagaita da dariyar da yake ba,share shi haydar yayi yaje kan kujerar sa ya zauna ba tare da yace masa komi ba sai da Dr.Abdallah Ya gaji don kansa yayi shiru sannan ya dubi A.M Yace..

*******
Bayan mun yiwa Baffa Allah ya tsare domin ya fita kasuwa yana son yau ya zuba abubuwan da ya dace ya saida a shagonsa.

  Misalin sha biyu na rana da wasu mituna muna zaune ni da salmat muna cin dambun shinkafa da zogale wanda shine yau na dafa matsayin abincin rana, muka jiyo muryar Inna Saude dake chan nesa damu tana shan sauti a redionta tana kwalawa Salmat Kira, mikewa Salmat tayi tana cewa,

"Adda Agla Bara naje naji kiran da inna ka yimin"

da "tou"Aliya Ta amsa mata.
     Diban dambun ta sake yi da hannunta sannan ta wuce tana amsawa Inna Saude, lokacin da ta isa inda take tana cewa,

"gani fa  Inna Dafatan lafiya ?"

"lfy lumi.... dama batun kudin ku ne da nace kibawa mai tsada(Agla)ta ajiye,karbo mini s.........
Bata ida zancen ta ba Salmat Ta waro idanunta waje tare da hadiye dambun dake cikin bakinta batare da ta shirya ba haka ya yi sanadiyar sarke ta, ta rika tari ba kakkautawa.

     Zeesardauner ce

           ( ~Y'ar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now