👩👩👧👧 *WASU MATAN* 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
*Story and Writting*
by
*Zainab sardaunerh*
بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚
_________________
______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_
🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y
*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 33~~34
Dole ta karo wata y'ar aiki tunda ya hana ta korar wannan matar.
Tana shiga d'an madaidaicin bedroom da Suhailat ta bata,zaunawa tayi bisa katifa tana cewa " ohni hasiya duniya ina zaki damu?ina zaman zamana gdan mutunci ta d'aukoni amma gashi kwana na daya na fara fuskantar wulakanci harda mari abunda ko uwa ta har ta koma ga Allah na manta rabon da ta yi mun wannan marin " tafada tana rike hab'a " anya bazan gudu ba dan da'alama matar nan ba mutunci gare taba ko wancan gidan da ta d'aukoni in tazo sai tai ta nuna isa tana wulakanta irina y'an aiki bata d'au ki talaka a bakin komi ba"cikin zuciyarta take wannan zancen batare da tasan ya fito fili ba .Allah ka sawwaka mana katausayawa talaka(nace ameeen)
Bangaren Haidar kuwa yana shiga cikin room d'insa aka kira wayarsa *UMEEY LUV* shine sunan da ya bayyana akan screen d'in wayar,accepting calling d'in yayi tare da k'ara wayar a kunne " Assalamu Alaikum ya Umeey"
shiru yayi sannan yace "afuwan umeey ayyukane sukamin yawa wallahi shiyasa ban shigo Abuja ba kamar yadda na fad'a miki"shirun ya sake yi yana saurarenta sannan yace " yace inshaallah cikin weak d'innanzan shigo domin akwai wani course da nake son na tafi nayi a india "jim kadan yace "ok badamuwa sai na shigo,bye "yaman nawa wayar kiss .
Bayan ya ajiya wayar ne bisa d'an madaidaicin glass dake gabansa,ya zauna saman royal kujera 1siter tare da kunna tv yana kallon news.
Abangaren Abban Khaleel kuwa biyar da rabi daidai ya kulle shagonsa,bayan ya fito daga kasuwar direct islamiyya ya nufa,yau ranar hardace don haka harda ya dibawa yan class d'insa bayan sun kammala akayi addu'ar tashi sannan ya wuce gidansa.
Kamar kullum yadda gidansa yake haka ya tarar dashi,bata gajiya da ayyukan gidan shiyasa ko da yaushe kaunarta ke kara ratsa zuciyarsa da gangar jikinsa ,komi baci da ransa yayi idan yashigo cikin gidansa sai yaji ya wanke musammanidan yayi tozali da kyakkawar matarsa wannan ita ce ake kira *_MAR'ATUSSALIHA_*.
Sallama yayi ta'amsa tana cikin kwalliyarta mai daukar hankali,riga da siket ne take sanye dasu na atamfa yayin da d'unkin yayi mata cip a jikinta gwanin shawa tokarewa yayi a bakin kofar yana kallonta itama shi d'in take kallo rungumar davyaran sukamasa yasa yadawo cikin haiyacinsa suna cewa oyoyo Abba sannu da zuwa rungumarsu yayi yana amsa musu tare da tambayarsu suma suna lafiya,kusa dashi tazo ta zauna itama tana masa sannu da zuwa amsawa yayi d'auke da murmushi a fuskarsa yayin ta cewa yaran oya ku tashi kubari Abba yaje yawatsa ruwa "tou umma"sukace yayin da suka daga daga cinyar Abban khaleel ta kardun da ya shigo dasu a hannunsa ta dauka da'alama daga islamiyya ya biyo dasu dakin sa ta kai masa yayin da tafito cikin tsakar gidan ta hada masa ruwan wanka ya shiga yayi yayin da a zuciyarsa yake cewa" miya kai haka dadi a duniya!samun mace ta gari shine ginshikin farin ciki a rayuwa shiyasa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wassalam yake cewa,فنكح المراءة لاءربع لمالها, ولجمالها,ولحسبها,ولدينها,فعلك بذات الدين تركت يداك.
Manzon (S.A.W)ya bada zabi ku aure mace don abubuwa guda hudu.
1-Domin dukiyarta
2-Domin kyawunta
3-Domin nasabarta
4-Domin Addininta
Amma sai yace wacce tafi alkhairi itace ku aureta dan addininta domin shi yake dawwama kuma shine dawwamamme.
To hakika shikam yayi dace mai Addini, kyau,nasaba duk yasamu.
Bayan yafito daga wanka tana tamaka masa yana saka tufafi ya dube ta yace "madallah da samun mace ta gari mai Addini,ako da yaushe ina kara godewa Allah da ya mallaka min ke a matsayin matata"murmushi ne ya subuce mata ta rungumeshi tana cewa "madalla da samun miji kuma malamina "bayan ya kamma shirin suka fito falo suna cin abincin dare,sannan suka dan taba hira saida yaran suka yi bacci ta kaisu makwancin su tare da sauya musu kaya zuwa na bacci ta musu Addu'a tasha fa musu sannan suma suka nufi ma kwancinsu.(Asuba ta gari )
Aka ce dare mahutar bawa amma abangaren Dr.Aysha ba haka bane zaune take takasa bacci da ta rufe idanunta Dr.Haidar take gani ji take kamar ace yana kusa da ita da ta nuna masa kalar soyayyar da take masa zuciyarta na kunci ne idan ta tuna ko wani ma'aurata a wannan lokacin suna tare da junansu,rumtse idanunta tayi tanaji kamar an watsa mata tafasasshin ruwan zafi idan tayi wanan tunanin.juyi kawai take yi bisa makeken gadonta daga kai tayi ta kalli agogon dake manne bisa bangon dakin na zinari karfe 1:30Pm na dare jingina jikinta tayi da gadon yayin da ta lalibo wayarta iphone 11pro ta danna tsakiya haske ya kawo photonsa ta zurawa ido wanda yake a walpeper wayarta yana sanye da suit black yayi masifar kyau kayan sun kara haskaka hasken fatarsa suman kansa sai sheki take yana d'aura agogo a hanunsa da'alama unexpected pics akayi masa galeery dinta sunansa ne a password dinta Aliyuheartbeat💓 bayan ta cire password d'in ta cigaba da kallon pics dinsa kala kala dake cikin wayarta kama daga na kananan kaya,suit,shadda,boyel,da kayansu na likitoci bata ankara ba sai da taji agogo ya buga karfe uku saura na dare ajiyar zuciya ta sauke yayin da zuciyarta ta kasa hakuri saida ta lalibo number sa ta d'an na masa k.......................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
( ~Y'ar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)
# _comment_
# _like_
# _share_
*Comment and vote d'inku shike* *karamin karfin guiwar* *typing* 💋
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Historia Cortaبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
