👩👩👧👧 *WASU MATAN* 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
*Story and Writting*
by
*Zainab sardaunerh*
بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚
_________________
______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_
🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y
*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
_Nagode da Addu'o'in ku a gareni_ my fans _ _na ji sauki_ _sosai Allah ya bada__ _lada_
*Page* 15~~16
Tana cewa "k'aunata jeki ki wanke hannunki muci abincin ci"
"tou Addana"ta fada tare da mikewa tsaye,bayan ta wako hannun na tane ta zauna kusa da Aglaa,bisimilla tayi suka faracin tuwon.
Da suka kammala cin Abincin ne suka zauna kusa da bappa suna fira yana basu labarai kala-kala masu sa nishadi da ban dariya,salmat Sai dariya take ita ma Aglaa Murmushi takeyi.
A duk lokacin da suke firar dare tsakaninsa da yaransa wani lokaci da inna Saude sai yaji a ransa inama tana raye,inama ace a yanxu hakan suna tare.da zai iya dawo da hannun a gogo baya da ya gyara kuskurensa da zai sanyata farinciki fiye da misali,
Ajiyar zuciya ya sauke ya dubi su Aglaa Yana cewa "mamana kutashi ku tapi dakinku ku kwanta da wuri kar da safe ku makara zuwa makaranta"
"tou bappa sai da safe komi munka yima ka yafe mana"suka ce suna mikewa tsaye
"na yafe muku,Allah muku Albarka"
"ameen bappa"
Bayan bappa ya kulle gida ya nufi dakin inna Saude,su Aglaa kuwa suka nufi nasu dakin.
*WASHE GARII*
Tun da bappa ya ta dasu sallar subahin bata koma bacci ba tana zaune tana azkar bayan ta idar da sallah, jin bappa ya dawo daga masallaci ne ta fito tana cewa "bappa ina kwana"
"lfy lau mamana kintashi lapiya"
"lpy lau na tashi bappa, kaifa?
"nima qalau nake,salamatu ko ta tashi tayi sallah?"
"eh bappa tana idarwa ta koma bacci "
"yawwa, na dauka haryazun batayi sallar ba ne "yace yana shiga cikin dakinsa .
Ayyukan da tasan wajib ne tayi su ta fara,dan bata san ta makara a makarantar bokon.
Gidan ta fara sharewa ta masa tas sannan tayi wanke-wanken k'wanuka, ta daura ruwan damun kunu.Da suka ta fasa ta dama kunun sannan ta d'aura zazafen tuwo.
Dakin inna Saude ta nufa ta gaya mata ta gama abincin karin kumallon tazo ta raba.
cikin dakin ta shiga da sallamarta, inna Saude ta hango tayi reshe-reshe bisa katifarta tana shakar baccinta.
A ka'idar inna Saude ba'a tada ita bacci,kuma ko waye yayi gigin tada ita yasin sai yaga cin mutunci kala-kala,Bappa d'ai ne dai-dai da ita dan tana shakkunsa wani lokacin amma wani lokaci inta tashi rashin arzikinta harda shi take mawa.
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Historia Cortaبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
