page 69&70

234 28 7
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab Sardaunerh*

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          *⚜️©J.A.W📚🖌️*

Page 69~~70

Su Ummu sun yi farin cikin jin cewa ba'a samu karaya ba,Alhj Sa'id da Kansa yaje ya duba Agla hakama Ummu taje ita da Fatima a kabar Batul da girki kamar ta yi kuka fatima sai gwalo take mata.

     Inna dije na jin abunda ke faruwa amma ko cikanku ba ta ce musu ba sai ma yawon da take a kwanakin nan bata cika zama ma acikin gidan ba.

Bayan Ummu sun dawo daga gidan su Ramlat Fatima ke bawa Batul labarin abunda akayi bata nan har da sakon Antynmu (Agla) da Salmat na gaisuwa da suka  bada a kawo mata,nan suka hau firar Agla wadda Ummu ce ta jawo ta tambayarsu kawai ta yi wacece antyn tasu?abunka da mai nema cikin duhu bare an haska sai kawai suka hau firar ta domin fa tayi bala'in burgesu,Ummu na sauraren su bata tanka ba amma ko ita yarinya ta kwanta mata a rai ta ya ba da nutsuwarta sosai har cikin zuciyarta.

Bayan Sati biyu

Rayuwa kenan;gamu muna shirye_shiryen komawa gida muda muka zo da niyar weekend gamu Munyi kwana Goma sha bakwai sanadin wannan accident da na samu.

 

   Hada kayan mu muke slowly kowa jikinsa ya yi sanyi domin duk da cewa wannan Jimawa ba ta lafiya bace amma shakuwa ta kara Shiga tsakani kamar kar mutafi.

  Amma tafiya dole domin nayi kewar Baffana sosai ga kuma WAEC da ke kusantowa.

Salmat ce ta dubi Batul dake kusa da ita tayi shiru baki ya mutu ta kyalkyale da dariya tana cewa,

"amma fa yarinyar nan Kazar kauye ce ke, dubi fa yadda kika bata fuskarki kamar wacce aka cewa idan muntafi shike nan baza mu sake haduwa ba,ga yayanku nan basai kusa ya kai ku gidanmu mu ba ana tare ai"

Wata uwar harara na bankawa Salmat domin ta bani haushi Allah,
su baza su iya Shiga napep suje Inda muke ba sai tace su saka yayansu ya kaisu salon ya dinga takurawa mutane,yana cikin abunda yasa na keson komawa gida saboda ya takuramin da sunan zuwa dubiya duk ya bi ya dameni.Idan maganar sabo ake tabass munyi mugun sabo da su Batul mussamman Fatima domin na lura tafi Batul nutsuwa;domin Batul irin Salmat da Ramlat ce Kaudi ke gare su ga rawar kai.

    Tunda suka zo dubiya Allah ya hada jininmu shiyasa ko da yaushe in basa school ko Islamiyya suna gidan mama Kareema hakan ya karasa shakuwarmu karfi.

  Sometimes haka kawai yayansu wanda suke cewa yah KB ya ke kawo su da daddare mu zauna muyi ta nishadi sai dare ya yi misalin 11 ko 10:30 ya dauke su su koma gida.

Bugu da kari Ramlat itama barin zuwa makaranta tayi ya yin da ta antayawa malaman karyar cewa sun yi tafiya,shirme da shiririta kuwa karuwa ma suka yi domin Batul ba baya ba itama.

Hakan suke shiryawa suje gidan su Batul suma idan suka ishi mama Kareema da haukarsu sai ta korasu tasamu ta yi bacci musamman da rana wannan shine yasa Shakuwar tayi karfin da akejin ba daďi wurin rabuwa.

Ta bangarena kuwa ina cikin farincikin nazo yah Anwar ba ya nan sai ga wani kuma kaddara ta hadamu ya na takuramin idan badon shi ba da kuma Baffana da nake son gani da sai na kara sati daya dai-dai naji sauki sosai,

"Mssstwwwsss"
tsukin da ban shirya masa ba ya fito.

Duba na Ramlat tayi domin itace kawai taji tsukin su Salmat hankalinsu baya kaina tana cewa,

"y dai Adda?"

"bakomi Ramlat"

"Ok"
tace tana maida dubata ga Fatima da tayi murmushi tana cewa Salmat,

"hakan ma za'a yi kuwa Salamatun inna koma bai kaimu ba sai mushiga napep.."

"ah to amma duk kinbi kin bata ranki,yi murmushi mana"
tafada cikin sigar tsokana tana jan kumatun Batul har saida ta tuntsire da dariya.

Karfe biyu na so mu wuce amma Salmat tace sai Hudu kafin mu isa biyar ta yi domin tasan muddin muka isa karfe uku sai inna Saude ta samu girkin dare.

Bayan munyi Sallar la'asar muka yi Sallama da juna ya yin da mama Kareema ta hada mana sha tara na  arziki,namu da na inna Saude hakama Ummun su Batul itama tabada kayan kwalliya da turare su Batul suka kawo mana tare da Kudi aciki inji Abban Batul bansan ko nawa bane da farko naki karba saida su Fatima suka nuna rashin jindadinsu sosai sannan na amsa nayi godiya.

Tafiya muke yi a hankali ya yin da su Salmat ke fira har muka kawo bakin titi da zamu tare napep mun jima tsaye abu Kamar wasa amma ba emtyn napep din da ta wuce duk wadda suka tara mutane ne a ciki har suka gaji da tsayi domin biyar har ta kusa.

Ana cikin haka sai ga motar Kabeer, tun daga nesa Fatima ta hangeshi ta yi murmushi tare da cewa,

"shikenan ma Allah ya yanke muna wahala ga yah KB nan sai ya yi dropping dinku "

"Wlh kuwa,Allah ma ya hutar da kudin napep dinmu"
Cewar Salmat,Ramlat ta dube ta tana cewa,

"baki da dama fa kawas "

"ah to waye yaki sauki,kuma waye ba ya son kudi?"

Batul ta ba Samlat hannu suka taba hannu har suna hada baki wurin cewa,

"babu"

Ko kanzil bance ba domin ga badaya na rasa ta cewa.

***************

Tun daga nesa ya hangesu ya sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya domin bai saka sammanin  taraddasu ba tun dazu yake sauri ya taho amma go slow ya saida shi a kan hanya.

Tsaye muke a jera gefen titin inda nice farko then Fatima,Salmat,Batul sannan Ramlat amma duk saida ya gota su  ya iso inda na ke ya yi parking tare da zuge glass dinsa yana cewa... 🖊️🖊️🖊️

Zeesardaunerh ce

          ( ~Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)

# _comment_ 
# _like_
# _share_

Comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now