👩👩👧👧WASU MATAN 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
DIYAH
{ Short story }
Labari ne mai cike da ban tautsayi tare da soyayya mai zafi
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number 2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number 09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number 09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 83~~84
"Whattt? tsaya ma wai,ni fa ban fuskanta ba Dr.Abdull what are you trying to said(mi ka ke ko karin cewa ne)"
"Abunda kunnuwanki suka jiye miki"
"keep joke a side zuciyata na iya bugawa, please ka gayamin gaskiya"
"dama ina miki karyane"
"No impossible wlh,hakan bazai ma yiwu ba"
"kinsan Allah kin bani dariya wlh, domin yanzu haka da wuya A.M ya kasance a Abuja kinga yau juma'a yana yiwa ya kasance ya jima da wuce India kuma dawowarsa ba nan kusa ba"
Tsayawa kallonsa tayi tamkar Tv ta rasa abunda zata furta,gabadaya tarasa kalmomi a bakinta.
A duk tunaninta Aliyu yana tsakanin Abuja da Kano amma taya hakan ta kasance,duk wata kasa da zaije tana sani kuma some times har ta rigashi isa da sunan itama taje yin wani course a chan.
Tabbas tana bukatar sanin duk wani bayani da ya shafi tafiyarsa domin dole nema tabi bayansa,bazata iya jure rashin ganinsa a kusa da ita ko da kuwa na sati ne bare kuma shekara,bata san lokacin da ta furta cewa "this is impossible!"tare da bugun teburin dake gabanta har sai da file din dake gaban Dr Abdallah suka watse.
Dagowa ya yi yana kallon ta ba tare da ta kalleshi ba ta juya tare da ficewa daga cikin office din tana jawo handle din kofar da karfi ya rufe, yayin da kwakwalwarta ta hasko mata wani tunani wadda ya idar da chakuda lissafin ta; yanzu idan ya kasance tare waccan tsinanniyar matar shi ya tafi fa,wani kololon bakin ciki ne ya tokare makogaronta yayin taji yajin kishi a cikin idanuwanta.
juwa kawai tayi ta wuce cikin motar ta ta kifa kanta a stiyarin motar ta lula duniyar tunani;tun ranar talata take faman neman A.M har a yau jum'at.
Numfashi mai zafi ta sauke yayin da ta tuna tattaunawarta da Dr Abdallah bayan tafiyar Aleeyu da kwanaki gashi yanzu zancen satittuka ake, tabbas ta gaji zuciyar ta ta galabaita da rashinsa kusa da ita tana bukatar son tabi bayan sa kuma tana tuna Alkawarin da tayi a wannan lokacin da tari tambayoyin da zuciyarta ke bukatar amsarsu;
( lSHIN MINE NE MATSAYINA AGUNSA? MIYA ƊAUKE NI NE ?MIYASA YAKE AZABTAR DA ZUCIYATA DA RUHINA!
Ina bukatar waɗannan amsoshin daga bakin ka,zan jira ka har ka dawo kuma bazan daina sonka ba domin sonka numfashi na ne kuma jininane ko mutuwa sai dai ta ɗaukeni da soyayyar ka_. _zanyi jinyar zuciyata har ka dawo Aliyu domin wannan karon bazan bika ba amma zan jira ka!zan jira ka. )
Zaune take zaman Royal chairs din dake kawataccen parlon ta,tana sanye da duguwar riga mara nauyi wacce ta lafe a jikinta ta bayyanar da tsarin halittarta,tarasa wane hukuncin zata yanke.
Saida ta kwashe kusan awa daya kafin ta yanke hukunci, da yake bata da zuciya ta yanke shawara binsa ko da zata zauna nesa dashi batare da yasan taje ba ko ganinsa zai rage mata wannan zafin zuciyar da take fama dashi.
SUHAILAT
Jirgin su na sauka a Abuja gidan su ta wuce daman tayi waya da mamynta an turo mata driver ba batun taje ta gaida Ummyn A.M ko kala haidar baice mata dama ta saba irin wannan ba farau ba ya saba da ganin hakan ya motarsa ya shige shima batare da b'ata lokaci ba yayi gidan Ummieyn sa.
Kwanan sa biyu da zuwa jirgin sa ya lula samaniya sai kasar masu jajayen kunnuwa.
Duniya tayi wa SUHAILAT dadi duk da cewa mamynta na yi mata fadan yawo amma abu ga sagartattun yara sai a slow tun tashin ta dadynta ba ya kwabarta abunda take so shi take.
Yawon buki kam ba magana shigar kasaita, ado da kwalliya sai daukan hotuna da vedios ana posting tiktok ba abunda ya ragu.
Bayan 2weeks suka fara shirye_shiryen bukin daya daga cikin yan groups dinsu na Manyan Mata duk ta zama busy ko damuwa ba tayi na rashin waya da basa yi da A.M.
Tun daya ya tafi so daya suka yi waya bayan isar sa ya kirata lokacin tana tare da kawayenta but tana dauka ta gaya masa tana busy zata kirashi idan ta gama abunda take,har yanzu bai sake kiran ta ba itama bata damu da ta kirashi ba(Allah ya shirya).
AGLA
Ga surutun yan class da gulmarsu ga surutun yan group dinsu kanta duk ya yi mata ba dadi domin batason hayaniya dagyar taga antashi daga makarantar suka dawo gida,ko a saman hanya Amina firar abun da ya faru islamiyya take ko kala Aleeya(Agla)bata ce mata ba yayin da Salmat ke dari_dari sanadin abunda ta aikata.
Duk tunanin da zatayi ta kasa tuna waye MUHAMMAD KABEER tana lure da duk wani motsi na Salmat ko kala bata ce mata ba ta kyaleta ko abinci bata ci ba sanadin ciwon da kanta ke mata ta sha maganin ciwon kai ta kwanta ko firar da suka sabayi da bappa yau basuyi ba.
Inna Saude na lura da ita ko kala bata ce mata ba domin ko ita yau bata jin dadi Salmat ta sosa mata inda ke yi mata kai_kayi ko kadan batason tunawa da HALIMATU a Rayuwar ta.
Show me love patronize my book Diyah❤️
Zeesardaunerh ce
( ~Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)
# comment
# like
# share
comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Historia Cortaبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
