Page 91&92

135 17 5
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 91&92

WACECE UMMIEY? WACECE HALIMATUS_SADIYA? WACECE MAHAIFIYAR ALEEYA ACIKIN SU?

FLASH BACK

Asalinsu fulanin chadi ne kasuwanci ya kawo Alh Ali Kano shi da matarsa Zara,ana cikin haka Allah ya azurtasu ɗa ɗaya tilo suka saka masa suna Ahmad tun daga shi kuma basu ƙara haihuwa ba.
Ahmad ya kasance yaro mai matukar shiga rai ga duk wanda ya raɓe shi,gashi Allah yayi masa baiwar kyau ,ya tashi cikin matsananciyar soyayya wacce iyayensa ke nuna masa kasancewar sa ɗaya Allah ya basu,yayi primary da secondry anan kano karshe ya nunawa mahaifinsa yana sha'awar karatu a kasashen ƙetare batare da ɓata lokaci ba mahaifinsa yayi shige da fice har ya tabbatar da cewar ɗansa ya samu gurbi a wata maƙaranta dake can kasar India, ya ɗauki tsawon shekaru yana ƙaratu a fannin kasuwanci,babban burinsa shine ya gaɗi mahaifinsa.
Acan gurin karatun ya haɗu da wata yarinya ƴar ƙasar mai suna jasmine.

Jasmine ta kasance yarinya mai matukar kyau wacce ake ji da ita a collegen,kowa ne saurayi burinsa ta kulashi amma ita sam basa gabanta.Allah ne ya haɗa jininta da ɗan nigeria duk da cewar ba baƙar fata bane,tun tana yarinya take sha'awar su fita yawon ƙasashe ita da parent ɗinta,Nigeria ta kasance cikin ƙasashen da take muraɗin zuwa.

Sun shaku da Ahmad sosai duk da cewar ba'a fanni ɗaya suke karatu ba ita tana karatu ne a fannin lafiya wato medicine kuma ta riga Ahmad farawa amma a sheƙara ɗaya zasu kammala,har gidansu Ahmad yake zuwa sun yi sabo da mahaifanta sosai,ko kaɗan basu nuna masa wani abu ba kasancewarsa ɗan Nigeria,duk wani abu da ƴar su take so shi suke so,a yadda Ahmad ke gani soyayyar da iyayensa ke nuna masa ko kwatan wacce mahaifan jasmine ke nuna mata bata yi ba,suna matuƙar sonta mara misiltuwa,a yadda suke ji itace rayuwarsu domin ita ƙadai ke garesu basa da kowa,itace ƴarsu kuma itace danginsu.
Mahaifin jasmine wato Abbu ya kasance balarabe ne kuma musulmi mazaunin india yayin da mahaifiyarta wacce take kira da Mah takasance ƴar addini Hindu.

Soyayyace ta haɗa Abdul-muddalib da Amrita har suka amincewa junansu zasu yi aure amma sam danginsu suka ƙi mara musu baya,dangin Abu sunce baza ya auro mushrika ya kawo musu gida ba haka ma dangin ma sukace bazata aure musulmi ba,duk yadda suka so su fahimtar da dangin nasu abun ya cutura daga ƙarshe suka tsere aka ɗaura musu aure kamar yadda addinin kowannensu ya tanaɗa ma'ana aka ɗaura musu aure a kotu kamar yadda indiyawa sukeyi idan suka tsere daga gida sannan kuma aka sake ɗaura musu aure kamar yadda addinin musulunci ya tana da suka nemi gida a mumbai suka zauna.Ko kaɗan ba wanda danginsa ya bincikesa suma kuma basu wai-wayesu ba, ana cikin haaka Allah ya azurtasu da ƴarsu suka saka mata suna jasmine.
Tun da jasmine ta girma taga irin kyawun da Allah yayi mata ga kuma hari da samari ke kawo mata ta dinga saka likab dama kuma sam iyayenta basa bari tayi shigar banza wacce zata bayyanar da surarta har a illata musu ita,suna ji da ita tamkar gwal ɗin da babu kamarsa.

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now