👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai
Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 89&90
Har Amna ta ɓacewa ganin su bata dai na waiwayensu ba kamar yadda Aleeya ta kasa ɗauke idanuwanta akanta har ta bar gurin.
Cikin motar suka shiga yah Anwar yaja suka bar gurin,tsit motar tayi ba mai magana acikinsu,kowa da abunda yake zuciyarsa.
Ana kiraye_kirayen sallar magrib suka isa gida wasu masallatanma har an tada salla,parking ɗin motar yah Anwar yayi, Aleeya ce ta fara fitowa sannan Hanna kowannensu jikinsa a sanyaye batare da sun kwashe bags ɗin shopping ɗinsu ba suka wuce cikin gidan,sun ci sa'a ba kowa a palon direct ɗakinsu suka wuce,jakar hannunta Aleeya ta aje ta faɗa banɗaki.
Yah Anwar ma bai bi takan kayan ba,gurin tap ya nufa tare da yin alwala ya wuce masallaci.
Bayan sallar isha'i ya shiga part ɗinsu tare da bags ɗin a hannunsa,a palo ya tsaya suka gaisa da Mum dake nan zaune,jakunkunan ya mikawa Hisham domin ya kaiwa su Agla a ɗakinsu.
Kin zuwa Hisham yayi saboda da zasu fita kin zuwa suka yi dashi,dariya yah Anwar yayi yana lallashinsa,sai da mum ta saka baki sannan ya ɗauki kayan ya tafi yana cewa "Allah idan naje komi dake ciki atare zamu rabasa"
Da sallama ya shiga ɗakin,zaune ya riskesu Hanna a saman gado Aleeya a saman darduma tayi tagumi,magana yake amma da'alama sunyi nisa a tunani,nooking ɗin kofar yayi wanda hakan ya saka suka dawo daga duniyar da suka afka
"What's wrong with you,since na shigo ina muku magana fa"
"Nothing"
"Allah ya baku lafiya"
"Ameen,what happen?"Hanna ta faɗa
"Yah Anwar ne yace na kawo muku shopping bags ɗinku,sannan kuma yace duk abunda yake ciki a raba dani"
"Keep it there"
Kamar yadda tace haka ya ajiye anan gurin da yake yayi tafiyarsa.
"Mum mi yake damun yaranki ne"
"Meya faru?"
"Da na shiga ɗakinne na ga kowannensu yayi nisa a tunani,then even a yanayin da Hanna tamun magana kamar akwai abunda yake damunsu,Anty Aleeya ma har tagumi tayi"
"ok bara zan bincikesu naji"
Kallon Aleeya Amna tayi tana cewa "Nasan there's alot of questions a zuciyarki haka nima, waɗanda dukkanmu bama da amsoshinsu,ada tamtama ne nake a kamannunku amma yau na tabbatar da cewa ba wai kama bace kawai duk yadda akayi there's relationship a tsakani "
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
