page 73&74

229 29 6
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
           by
Zainab Sardaunerh

🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          ⚜️©J.A.W📚🖌️

Page 73~~74

Bayan mu idar da Sallar magrib da Isha'I muka dawo saman tabarma muka zauna muna jiran dawowar Baffa ya yinda inna Saude ke cikin madafi tanashan hayaki takammala tuwo miya ce ta rage ta kada,na tashi na kama mata domin naga itacen danyu ne amma ta bankomini harara sai da najuya na dawo wurin da nake,Salmat ta dubeni cikin dariya tace,

"wa ya ake ki Adda,baki lura a kufule take damu ba shiyasa ta sharemu,kinci arzaki harara kawai ki ka samu banda zagi"

Shiru na yi bance komi ba Salmat cikin jan magana Salmat tace,

"Inna"

Shiru Inna tayi ta kyaleta amma duk da hakan ba tayi shiru ba so take sai ta tsokano hajiya Saude,

"Inna!Inna!!,Innata!!!"

A kufele Inna Saude da takammala kaďin miya ta juyo tare da cewa,

"dan Ubanki lafiya kike yimini kiran maharauta kamar wacce ta yi wa Ubanki sata"

"maida wukar Innarmu,kawai yunwa nakeji "

"zo ki cinyeni tunda baki san Inda abinci yake ba"

"Lah lah lah mi ya yi zafi haka hajiya inna?kawai naga rashin da cewar ace ga mai girki a cikin madafi ni da bani na girka ba na tashi zuwa diba,ba ki ga Adda Agla idan ta girka abinci zubawa kowa take takaimasa"

"ki jira Ubanki ya dawo ya zuba miki shine Sa'an yina ba ke ba"

Cikin dariyar da take kumshewa tace
"Allah ya huci zuciyar Uwargidan Baffa,duk wannan abun bai kai chan ba,nasan hayakin da kika sha ne ya b'ata miki rai har idaninki sunyi ja, bari Adda ta tashi ta zuba mana bakomi bane"

Wucewa inna tayi ta cigaba da harkokinta ya yin Aliya ta tashi ta zuba musu abincin,

"Inna ya naga abincin ba nama"

Inna Saude da ke kai lomar tuwo baki tace,

" yau Ubanki bai kawo an ka saka ba"

"Ayya ashe kullum nama ki ke ci inna gashi har kiba ma kinyi shiyasa kike cin magani baki so muka dawo b...."
    Maganar ta ce ta katse ganin Baffa ya shigo cikin gidan da Sallama a bakinsa,sannu da zuwa sukayi masa hakama inna amma ciki ciki ta yi,
ruwan randa masu sanyi Aliya ta dibar masa sannan ta zuba masa abincin.

Salmat takai lomar farko a bakin ta bayan haɗiya ta dubi inna Saude tace,

"Inna"

"Lafiya"
Cewar inna

"lafiya lau,dama wai cewa zanyi miyar nan daddawa da gishiri ya yi masa yawa kuma cin gishiri ba kyau musamman ma ga wanda ya tsufa"

takalmi inna ta ra rimo da niyar ta jefawa Salmat aiko kamar walkiya Salmat ta ari na kare sai dakinsu tana dariya,aiko inna ta dinga fada kamar taci babu dama hake ta ke da su ko ni kaina saida na dara haka inna tai ta fada har saida ta gaji tayi shiru.

   Fitowa daga dakin Salmat tayi taje gurin randa ta debo ruwan sanyi da kofi ta ajiye gaban inna,ba tare da musu ba inna ta dauka tasha domin tana bukata.

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now