page 99&100

179 12 2
                                        

👩‍👩‍👧‍👧WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
           by
Zainab Sardaunerh

🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          ⚜️©J.A.W📚🖌️

Assalamu Alaikum sunana Ummu Maleek

Muna siyarda kayayyaki masu  kyau da inganci

munada maganin Ni’ima macce duk rashin ni’imarta Insha allahu rabbi zataji ni’ima tamkar korama ±💃💃💃💃

Muna da maganin infection ko wanne iri duk nacin infection Insha allahu rabbi kikayi amfani dashi zai rabu dake

munadasu Tsumin kala kala Munada gumbar nonon rakumin munadata dabino

Akwai mallakar miji masu zamu🔥🔥wanda inki kayi amfani dashi mijinki ko dutsene shi saiya tanka

Munada Emergency thghting duk yadda kika kai da budewa zaki hade tsaf Insha allah’ akwai hips Elargenment akwai breast Elargenment

Munada kayayyakin mata kala da iri masu zafi🔥🔥tamkar boom😻😻sha yanzu magani yanzu

Duk abinda kake da bukata zaka iya nemana ta👉07037112549

©️♤♡ Zeesardaunerh

Page 99~~100

  
Ana wata ga wata hausawa suka ce tashin hankali ba'a saka masa rana, hakanne ne kuwa ya kasance a gurin Maryama domin kasa gasgata Inna Laure ta yi tana cewa ai wannan shirme ne ita bazata taba yarda ba,duk da cewa zuciyar ta a saba'in take bugawa a lokacin.

    Kai ina wannan abun karyane ta ya ma hakan zata kasance gareta,duk wata kofa sai da tasan ta toshe ta bata bar wata kafa ba,to a ina Kabeer ya hadu da wata har ake batun aure kuma taya yaya hakan takasance?

Korar Inna Laure tayi yayinda ta zurfafa a tunani, ko kadan bata taba lura da cewa Kabeer na boye mata wani abu ba, a ina ma yasamu kwarin guiwar yin wannan tunanin batare da sanin ta ba? shi da ko gardama da jayayya bai iyayi da ita,itace ke juyasa duk yadda take so acikin gidan wannan abun bazai ta ba faruwa ba.

A haka ta kwana cikin zullumi da tunani batare da ta nunawa Kabeer komi ba zuciyar ta sai zafi take, wutar bala'in kishi na kara ta'azzara cikin zuciyar ta,da ace za'a aunata a wannan lokacin da tabbas za'a tarar da cewa jinin ta ya yi mugun hawa sosai .

Abunda Maryama bata sani ba shine duk tasirin asirinta a gida yake ko kuma idan tana tare dashi amma da ya fita waje ba wani sihiri da yake tasiri a kansa face tana tare dashi ko a wajen.

Da niyar da safe taje gidan su wannan tsohuwar matar domin tana bukatar sanin gaskiya idan ba haka ba zuciyar ta bugawa zatayi.

Allah Allah kawai take Kabeer ya fita gidan itama ta fita domin ba taga zama ba.

Bayan fitar Kabeer da kimanin mintuna goma sai ga Inna Laure a gidan duk wata shaida da zata tabbatar wa da Maryama gaskiyar ta sai da ta nemo ta saka a cikin wayar Hindatu domin wannan karon tare da ita suka zo .

Kamar zararra haka Maryama ta koma idanuwanta sunyi jawur sab'agen kishi ya yin da zuciyar ta ta cigaba da bugawa da sauri_sauri ganin cewa fa tana iya zube musu anan ya saka Inna Laure jan y'ar ta suka yi gaba yanzu ko ba komi tasan ta  hadawa Kabeer boom wanda zai tashi da shi karshe ma ya yi sanadiyar wargajewar auren kuma hakan take so.

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now