Page 59&60

140 10 0
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN  👩‍👩‍👧‍👧
          @2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
           by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          ⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

       WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

    GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
   Page 59&60

Lokacin da suka isa ana sallar isha'i, bansan iya adadin awannin da muka ɗauka muna tafiya ba abunda kawai na sani shine sau biyu ina farkawa daga baccin da ya ɗaukeni amma bamu isa ba.

Wani plat ɗin gida Abba Muktar ya danna horn mai gadi ya buɗe muka shiga,gaba ɗaya a gajiye nake ina jin ko tafiyar da muka yi da Abba bata yi nisar wannan ba.

Fitilar waya mum ta kunna muka shiga cikin palon gidan, dif ko'ina yake ba haske,wani madanni Abba Muktar ya danna haske ya gwauraye ko'ina,jan akwatin nayi tare da bin bayan Hanna muka shiga wani lungu.Bamu yi doguwar tafiya ba muka riski kanmu a matsakaicin palo bamu tsaya ba sai da muka isa ɗakin kwana dake cikin palon.
  Zubewa Hanna ta yi bisa gadon tana raki,toilet dake cikin ɗakin ta nuna mun na shiga,bayan na kammala alwala na fito, darduma na tambayeta ta nuna mun na shinfida tare da kabbarta sallah.

Tun da nake bantaɓa hada salla uku wuri daya ba, amma gashi yau sallah hudu na hada banyi su ba,har na kammala azzahar da la'asar tana nan kwance bata tashi ba,magrib da isha'i na yi,na ɗau dogon lokaci a zaune ina Addu'a .

Bayan Hanna ta rama sallolin da ke kanta ta fita,bayan wani lokaci ta dawo tare ɗa ledar take away da Abba Muktar yayi muna saman hanya.

Bayan kammala cin abincin muka watsa ruwa sai bacci.

*****************
Na yi bacci sosai har na so na makara  ban tashi sallar asuba da wuri ba sai da mum ta tada mu,bayan mun kammala salar Hanna ta koma bacci,kasa komawa bacci nayi na tasheta ta nuna mun abunda zan yi sharar gidan da shi,sai tace mun ai mai aikin gidan tun da subahin take fara aikinta watakil yanzun ma takammala, tana gama faɗin hakan ta koma ta yi kwanciyarta.

Zaune na yi sai nake jin kaina ba daɗi kwata_kwata ni ban saba da zaman banza ba,ko kaɗan bana da lokacin hutu a gida sai idan Dadda ta kawo mana ziyara ko naje gidan mama Kareema ko kuma Innarmu ta fita unguwa,hakan na zauna ina tunanin rayuwata,nafi awa ɗaya a hakan sai da mahaifiyar Hanna tazo domin ta tashemu muyi kari,da ta ganni a farke sai tace na tadda Hanna mu sameta a palo.

  Kamar yadda tace hakan na yi bayan na tadda hanna ta yi brush na saka hijab ɗina muka fito palo,wani gurin naga hanna ta nufa na bita a baya,kujera taja ta zauna tare da jamun daya nima na zauna.
Bamu jima a zaune ba Abba da Mum suma suka zo gurin,kasa na yi da kaina tare da yi musu ina kwana, cikin sakin fuska kamar ko yaushe suka amsa min,Hanna ma ta yi musu ina kwana,irin abin da ake kawo muna a wancan gida da muka fito shi naga ta zubawa kowa da masar kwai sai shayi da bread,tsakurar masar nake yi a hankali duk na kasa sakewa

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now